'Abin da Sheikh Idris Dutsen Tanshi Ya Faɗa Kafin Rasuwarsa': Ɗalibinsa Ya Magantu
- Wani matashi da ke tare da Sheikh Idris Abdulaziz a lokacin rasuwarsa ya bayyana yadda lamarin ya faru a gidansa da ke Bauchi
- Matashin ya ce a gabansa Sheikh Idris ya cika, suna cikin daki tare da ɗansa Muhammad lokacin da marigayin ya ambaci kalmar shahada
- Ya kara da cewa tun da jikinsa ya fara tsanani misalin karfe 10:00 na dare aka kira shi don ya zo wajen malamin da ya samu shaida na kwarai
- Matashin ya bayyana cewa dukansu a cikin dakin ba su ji wani abu daga bakin Sheikh Idris ba sai kalmar shahada har ya yi ajalinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Wani bawan Allah ya yi magana game da yadda Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya cika a gidansa.
Dalibin wanda bai bayyana sunansa ba ya ce a gabansa marigayin ya rasu lokacin da jikinsa ya yi tsanani.

Kara karanta wannan
'A tsaye aka karɓi ta'aziyya ta': Sheikh ya fadi dattakun ɗaliban Malam Dutsen Tanshi

Asali: Facebook
Dalibi ya gode Allah kan mutuwar Dutsen Tanshi
Matashin ya bayyana haka ne a yau Asabar 5 ga watan Afrilun 2025 a cikin wata sanarwa da Hamidan Badamasi Rijiyar Lemo ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin ya ce a gabansa marigayi Malam Idris Abdulaziz ya rasu lokacin suna tare da ɗansa, Muhammad a cikin daki.
Ya ce ko wane irin mutuwa ya yi su kam sai dai su ce Alhamdulillah saboda yadda ya cika da kalmar shahada.
A cikin bidiyon, ya ce:
"Ni a gaba na Dakta ya cika, ina daya daga cikin wadanda suke zaune, kan Dakta lokacin da ya yi numfashinsa na ƙarshe.
"Allah ne shaida ba zan fada ba ne domin ka yabe shi, a'a mu yanzu koma yaya ne mun godewa Allah yadda ya rasu.
"Tun da ni a gaba na ya rasu, kunnuwa na da na ɗansa Muhammad da sauran ƴaƴansa da mu ke wurin babu abin da muka ji sai kalmar shahada da Dakta ya furta."

Kara karanta wannan
"Yana da abin al'ajabi da kura kurai," Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan Dutsen Tanshi

Asali: Facebook
Yadda Dutsen Tanshi ya rasu a hannun ɗansa
Matashin ya ce kusan misalin karfe 10:00 aka kira shi lokacin da jikin marigayi Dutsen Tanshi ya yi tsanani da ke da ban tsoro.
Ya kara da cewa:
"Ni lokacin da suka kira ni ya kai 10:00 na dare, lokacin da na gan shi hankali na ya tashi har na fara samun wani yanayi.
"Da naga yanayin jikinsa na ce lallai mu kai Dakta asibiti, shi kuma Muhammad da Dakta ke hannunsa ya ce to a saka masa kaya a tafi.
"Hankalinmu ya tashi, a lokacin da Dakta ya furta kalmar shahada ne hankalinmu ya dawo jikinmu muka fara karanta kalmar shahada.
Shehin malami ya jinjinawa ɗaliban Dutsen Tanshi
Kun ji cewa Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya jinjinawa daliban marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi bisa mutunta wasiyyar da malaminsu ya bar musu kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan
Bayan jana'izar Dr Idris, wani limami ya ja sallar Juma'a a masallacin Dutsen Tanshi
Shehin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, ranar Asabar 5 ga watan Afrilu 2025, bayan rasuwar malamin.
Sheikh Ibrahim ya ce abin yabawa ne ganin yadda daliban suka tsaya kan wasiyyar malaminsu wanda shi kansa a tsaye aka karɓi gaisuwar ta'aziyyarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng