Bayan Kashe Mutane Sama da 50, Gwamna Ya Gano Waɗanda Ke Ɗaukar Nauyin Ta'adi
- Mai girma Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana cewa rikicin da ke faruwa a jihar Filato ba faɗan manoma da makiyaya ba ne
- Mutfwang ya ce wasu ɓata gari ne a gefe, suke kitsa duk wannan kashe-kashen da ke faruwa domin hana jihar Filato zaman lafiya
- Ya tabbatar wa al'umma cewa da ikon Allah, gwamnati da hukumomin tsaro za su shawo kan lamarin kuma zaman lafiya zai dawo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau - Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana cewa hare-haren da ake ci gaba da fuskanta a wasu sassan jihar ba rikicin manoma da makiyaya ba ne.
Gwamna Mutfwang ya yi ikirarin cewa waɗannan hare-hare da ke jawo asarar gomman rayuka, wasu marasa son zaman lafiya ne ke ɗaukar nauyinsu saboda wata manufa.

Asali: Facebook
Caleb Mutfwang ya bayyana hakan ne yayin bikin baje kolin kayan ado da fasaha na Tincity Fashion Week da aka gudanar a daren Juma’a a Abuja, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe mutane 52 a Filato
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a ranar 2 ga Afrilu, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan al’ummomin Manguno, Daffo da Josho da ke karamar hukumar Bokkos.
Maharan sun kashe mutane da a yanzu aka ce sun kai 52 tare da kona gidaje da dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira.
Mutfwang ya dage cewa hare-haren ba su da alaka da rikicin makiyaya da manoma, yana mai cewa laifi ne da aka tsara domin tayar da hankalin jama’a da hana zaman lafiya.
Ya ce gwamnati tare da hukumomin tsaro sun dauki matakan da suka dace don hana faruwar irin hakan nan gaba.
Wane mataki gwamnati take ɗauka a Filato?
Gwamnan ya ce:
"Ina gode wa dukkan ku da kuka zo domin goyon baya da girmamawa ga jihar Filato a wannan gagarumin taron. Muna godiya matuka.
"Mun yi tunanin soke wannan taro saboda halin da jihar ke ciki, amma muka yanke shawarar kada mu bar halin da ake ciki ya hana mu murnar abubuwan kirki da muke da su.
“Manufar maƙiyanmu ita ce jefa jihar cikin bakin ciki da dimuwa, amma za mu fuskance su kuma ba za mu bari su cimma burinsu ba.
"Ga wadanda ke ganin cewa abin da ke faruwa rikicin manoma da makiyaya ne, ina so in fitar da ku daga wannan tunani, wannan abu ne da wasu mugaye suka tsara domin hana zaman lafiya a Filato."

Asali: Facebook
Gwamna Mutfwang ya tabbatar wa mutanen Jihar Filato cewa da ikon Allah za su yi nasara a kan wadannan bata-gari, kuma karshen su ya zo.
Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu a wasu hare-hare da ake zargin fulani makiyaya da kai wa a jihar Filato.
An ruwaito cewa akalla mutane 10 suka mutu a hare-haren wanda aka kai kauyukan ƙaramar hukumar Bokkos ranar Laraba.
Wadannan hare-hare sun faru ne kwana shida bayan makamancin hakan ya faru a garin Ruwi, inda aka harbe mutum goma har lahira,
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng