'A Tsaye Aka Karɓi Ta'aziyya Ta': Sheikh ya Fadi Dattakun Ɗaliban Malam Dutsen Tanshi
- Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya jinjinawa daliban marigayi Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi bisa mutunta wasiyyar da malaminsu ya bar musu kafin rasuwarsa
- Shehin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, ranar Asabar 5 ga watan Afrilu 2025, bayan rasuwar malamin
- Sheikh Ibrahim ya ce abin yabawa ne ganin yadda daliban suka tsaya kan wasiyyar malaminsu har a tsaye aka karɓi gaisuwar ta'aziyyarsa
- Malamin ya bayyana cewa bai samu halartar jana'izar ba saboda cunkoson al'umma, amma ya yi masa addu'a Allah ya gafarta masa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi magana bayan rasuwar Malam Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi a Bauchi.
Shehin malamin ya yabawa ɗaliban matigayin inda ya ce tabbas sun mutunta wasiyyar Sheikh Idris Dutsen Tanshi.

Kara karanta wannan
'Abin da Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya faɗa kafin rasuwarsa': Ɗalibinsa ya magantu

Asali: Facebook
Malami ya yabawa ɗaliban Sheikh Dutsen Tanshi
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a yau Asabar 5 ga watan Afrilun 2025 a shaifnsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Ibrahim Kaduna ya ce abin yabawa ne yadda ɗaliban suka tabbatar da bin wasiyyar da marigayin ya bayar.
Ya ce shi kansa a tsaye aka karɓi ta'aziyyarsa wanda hakan ke tabbatar da bin ka'idar da marigayin ya ba su kafin rasuwarsa.
A cikin rubutunsa, ya ce:
"Dr. Idris ya hana a yi masa zaman makoki, daluban Dr. Idris sunyi ruko da wannan wasiyyah.
"Nima a tsaye aka karbi ta'aziyyah ta."
Har ila yau, malamin a wani rubutu a Facebook ya ce bai samu damar halartar jana'izar marigayin ba saboda cunkoson al'umma.
Daga bisani, ya yi masa addu'a ta musamman domin rokon Ubangiji ya gafarta masa ya sanya shi gidan aljannar Firdausi.
Sanarwar ta ce:

Kara karanta wannan
"Yana da abin al'ajabi da kura kurai," Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan Dutsen Tanshi
"Saboda yawan al'ummah da cunkoso shiga filin da ake sallar gawar Dr. Idris ya gagare ni."
"Allah ya gafartawa Dr. Idris ya ba shi gidan aljannah."

Asali: Facebook
Martanin wasu kan rubutun Malam Aliyu Kaduna
Mutane da dama sun yi tsokaci kan rubutun shehin malamin inda suke tabbatar da cewa marigayin ya yi mutuwar shahada.
Abu Safiyyah:
"Wato karatu da aiki da karatu sai Dr Idris, kuma a zahiri duk malaman Nigeria babu kamarsa.
"Ina rokon Allah ya jikan Dr idris da rahama."
Anas Mika'eel Jido:
"Labari mai dadin ji shi ne Malam yana maimaita kalmar shahada ya cika, ga shi a daren Juma'a, muna kyautata zaton Dr. na cikin farin ciki in sha Allah."
Suraj Mohd:
"Ya kamata duk maluman ahlus Sunnah su ba da wannan wasiyar su da mabiya a kore wannan bidi'ar"
Dutsen Tanshi: Sheikh Gumi ya yi ta'aziyya
Kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi ta'aziyyar rasuwar Malam Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma'a 4 ga watan Afrilun 2025.
Dr. Ahmad Gumi ya roki Allah Ya gafarta masa kura-kuransa saboda a cewarsa mutum ne wanda ke da abin al'ajabi.
Babban malamin ya bayyana yadda marigayi Dutsen Tanshi ya tsayu kan tauhidi kuma ya yi faɗa da ƴan ɗariku a jihar Bauchi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng