Kamar a Jahiliyya: An Tono Gawa bayan Mahaifi Ya Kashe, Ya Birne 'Yarsa a Najeriya
- Rundunar ‘yan sandan Legas ta kama wani mai suna Kamoru Ojo bisa zargin kashe ’yarsa mai shekaru 27, sannan ya birne ta a gida
- Lamarin ya faru ne a unguwar Afromedia da ke karamar hukumar Ojo, amma an kai rahoton ne ga 'yan sanda kwana takwas da birne ta
- Rahoto ya nuna cewa ’yan sanda sun tono gawar marigayiyar daga inda aka birne ta, kuma an tura gawar zuwa asibiti domin a yi bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum da ake zargi da kisan kai a kan ‘yarsa.
Ana zargin cewa bayan ya kashe ta, ya birne ta a rami mai zurfi a cikin gidan da suke zaune a unguwar Afromedia, cikin karamar hukumar Ojo ta jihar.

Asali: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa lamarin ya faru ne ranar 26 ga Maris, amma sai ranar 3 ga Afrilu, 2025 aka kai rahoton ga ‘yan sanda na Okokomaiko misalin karfe 8:00 na safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ‘yan sanda ta shaida cewa ana zargin mahaifin, Kamoru Ojo, ne ya doke diyarsa, Shakirat Ojo har ta mutu, kafin daga bisani ya bine ta a cikin gidan da suke zaune.
’Yan sanda sun tono gawar Shakirat
Bayan samun rahoton, rundunar ‘yan sanda ta tura tawagar binciken laifin kisa da masu tantance aikata laifi zuwa gidan.
Tawagar ta gano wurin da aka birne marigayiyar, sai aka tono gawarta a gaban jami’an tsaro da shaidu.
An dauki hotunan wurin domin tabbatar da sahihancin bincike kafin a dauki gawar zuwa dakin ajiye gawa na gwamnati domin gudanar da gwajin binciken kisa.
Jami’an tsaron sun ce suna ci gaba da bincike domin gano dalilin kisan da kuma yiwuwar akwai wasu da suka taimaka wajen aikata laifin ko kuma suka san da lamarin amma suka boye.
Cigaba da bincike don gano masu laifi
Wani jami’in ‘yan sanda da ke da hannu a binciken ya bayyana cewa sun fara bincike domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru wajen yi wa budurwar kisan gilla.

Asali: Facebook
Ana sa ran cewa yan sanda za su fitar da rahoto bayan kammala tattara bayanai da bincike kan lamarin.
Haka zalika bayan kammala bincike ana sauraron matakin da 'yan sanda za su dauka kan duk wanda aka samu da laifi a kan mummunan aikin.
Hausawa da makiyaya sun yi fada a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa an gwabza wani kazamin fada a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya tsakanin wasu Hausawa da Fulani makiyaya.
Rahotannin da aka samu sun tabbatar da cewa an kashe wani matashi kuma bayan jami'an tsaro sun tsananta bincike an samu gawarsa a kwance a cikin jini a wani waje.
Rahoton Legit ya bayyana cewa an fara gwabza fadan ne yayain da aka taru a wata makaranta a lokacin bikin karamar sallah, wanda ya jawo babbar asara a garin da abin ya faru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng