Tirkashi: Uba ya kashe saurayin 'yarsa ya auri abar shi

Tirkashi: Uba ya kashe saurayin 'yarsa ya auri abar shi

- Wani mutum mai suna Larry McClure da ke yammacin Birginia a Amurka ya kashe saurayin ‘yarshi inda daga baya ya aureta

- Mutumin ya bayyanawa kotu cewa, tare da ‘ya’yan nashi suka hada kai suka hallaka saurayin daya daga ciki har lahira

- A halin yanzu, McClure na zaman aure tare da Amanda a gidan da suka kashe saurayinta tare da birneshi

Wani mutum a yankin Yammacin Birginia da ke kasar Amurka ya shaidawa hukumomi yadda ya yi nasarar kashe saurayin daya daga cikin ‘yarsa kuma aka birneshi a wani kabari da suka gina. Daga baya kuma mahaifin ya aure ‘yar ta shi.

Larry Paul McClure dattijo ne mai shekaru 55 a duniya. Ya aikewa hukumomin tsaro wasika inda yake bayyana yadda suka hada kai tare da ‘ya’yanshi mata biyu wajen kashe saurayin daya daga ciki.

Amanda Michelle McClure na da shekaru 31 a duniya inda ‘yar uwarta Anna Marie Choudhry ke da shekaru 32. Saurayin da aka hallaka, masoyin Amanda ne.

Wani jami’in ‘yan sanda a yankin Birginia din ya bada shaida a zaman kotun da ya gudanawa a kan mutanen uku da ake zargi da kisan McGuire. An gano sun maka mishi kwalbar giya ne a kai, daga bisani suka daureshi tare da yi masa allura guba, kamar yadda bincike ya gano.

KU KARANTA: Abin da mamaki: An ciro almakashin tiyata da ya shekara 18 a cikin wani mutumi

Daga nan sai suka shakeshi har ya mutu, inda daga baya suka haka kabari suka binneshi a cikin gidan da suke zaune.

A wasikar da mahaifin ya mika, ya sanar da cewa, sun yi kisan ne bayan da ‘yarshi Amanda ta kawo shawarar. Amma bai san dalilin da yasa Amanda take son mutuwar John McGuire ba.

‘Yan sandan sun gano cewa, Amanda da mahaifinta sun tafi Birginia inda suka yi aure a majami’ar United Methodist.

Larry McClure, wanda ya yi kaurin suna wajen cin zarafi, na zaman aure da ‘yarshi a gidan da suka kashe McGuire. A halin yanzu dai, ana tuhumar McClure da ‘ya’yanshi da laifin kisan kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel