'Yan Bindiga Sun Yi Awon gaba da Matafiya a kan Hanya, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki
- Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare matafiya tare da yin garkuwa da su a jihar Benue a cikin watan sallah
- Tsagerun ƴan bindigan sun hallaka mutum biyu a motar tare da tafiya da sauran fasinjojin zuwa cikin daji
- Jami'an rundunar ƴan sandan jihar sun kai agajin gaggawa, suka samu nasarar kuɓutar da mutanen da aka sace
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari kan wata motar haya mallakin kamfanin Benue Links a yankin Ikobi da ke ƙaramar hukumar Otukpo, jihar Benue.
Ƴan bindigan sun harbe direban motar da wani fasinja da ke kujerar gaba, sannan suka yi garkuwa da sauran fasinjojin da ke cikinta.

Asali: Original
Ƴan bindiga sun sace fasinjoji a Benue
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis, kusa da tsohon kamfanin Benue Burnt Bricks.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Motar wacce mallakar kamfanin gwamnatin jiha ne, tana kan hanyarta daga Makurdi zuwa Otukpo lokacin da aka tare ta.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na kamfanin, Johnson Ehi Daniel, ya fitar a ranar Juma’a, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da yabawa da saurin ɗaukar matakin gaggawa daga hukumomin tsaro.
Ƴan sanda sun ceto mutanen da aka sace
Rundunar ƴan sanda ta jihar Benue a ranar Juma’a ta ce ta ceto fasinjoji 14 da ƴan bindiga suka sace a daren Alhamis a ƙaramar hukumar Otukpo.
Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar, SP Catherine Sewuese Anene, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Makurdi, cewar rahoton jaridar Vanguard.
Catherine Anene ta ce motar ta fuskanci harin ne a ranar 3 ga Afrilu, a kusa da Otukpo, direban da wani fasinja suka rasa rayukansu.
Ta ce bayan haka, ƴan bindigan sun ɗauke sauran fasinjoji 14 zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Kara karanta wannan
Ana cikin bikin Sallah, 'yan bindiga sun tafka ta'asa kan jami'an tsaro a Katsina
Ta ce jami’an ƴan sanda tare da hadin gwiwar ƴan sa-kai na jihar sun garzaya wajen da lamarin ya faru, suka tarar da direban da wani fasinja a cikin mota da raunukan harbin bindiga, yayin da sauran aka tafi da su.

Asali: Twitter
“An garzaya da waɗanda suka ji rauni zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwarsu.”
“Jami’an tsaro sun fara bin sawun ƴan bindigan cikin dajin da ke kusa da wurin nan da nan. A ranar 4 ga Afrilu, da misalin karfe 3:00 na rana, suka hango ƴan bindigar a cikin daji, sannan suka kuma yi artabu da su."
"Ƙarfin makaman ƴan sanda ya tilasta musu guduwa, inda suka bar waɗanda suka sace."
“Abin baƙin ciki, sun yi wa wasu daga cikin wadanda suka sace raunuka da adda kafin a ceto su."
"An ceto mutane 14, an kai su asibiti, aka tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikinsu, sauran kuma na karbar magani a halin yanzu.
- SP Catherine Anene
Ƴan bindiga sun ƙona makaranta a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun bindiga ɗauke da makamai sun.kao harin ta'addanci a jihar Zamfara.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a garin Rijiya da ke ƙaramar hukumar Gusau, suka hallaka mutane takwas tare da ƙona wata makarantar firamare.
Miyagun ƴan bindigan dai sun kai harin ne a ƙauyen a ranar 3 ga watan Afirilun 2025 da misalin ƙarfe 4:00 na yamma
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng