"Yana da Abin Al'ajabi da Kura Kurai," Sheikh Ahmad Gumi Ya Yi Magana kan Dutsen Tanshi

"Yana da Abin Al'ajabi da Kura Kurai," Sheikh Ahmad Gumi Ya Yi Magana kan Dutsen Tanshi

  • Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi ta'aziyyar rasuwar Malam Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma'a
  • Dr. Ahmad Gumi ya roki Allah Ya gafarta masa kura-kuransa saboda a cewarsa mutum ne wanda ke da abin al'ajabi
  • Babban malamin ya bayyana yadda marigayi Dutsen Tanshi ya tsayu kan tauhidi kuma ya yi faɗa da ƴan ɗariku a jihar Bauchi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Fitaccen malamin addinin musuluncin nan, Sheikh (Dr.) Ahmad Abubakar Gumi ya yi ta'aziyar rasuwar Malam Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi.

Shehin malamin ya bayyana cewa Marigayi Sheikh Dutsen Tanshi yana da abin al'ajabi a rayuwarsa duba da yadda ya tsayu kan tauhidi.

Sheikh Ahmad Gumi da Marigayi Dutsen Tanshi.
Sheikh Ahmad Gumi ya yi ta'aziyyar rasuwar Dutsen Tanshi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Ahmad Gumi ya yi wannan furuci ne a wurin karatun da yake gudanarwa a masallacin sultan Bello da ke Kaduna wanda aka wallafa bidiyon a shafin X.

Kara karanta wannan

Bayan jana'izar Dr Idris, wani limami ya ja sallar Juma'a a masallacin Dutsen Tanshi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Ahmad Gumi ya yi addu'ar Allah Ya jikan Malam Idris Dusten Tanshi, ya gafarta masa kura-kuransa.

Rasuwar Dr. Idris Dutsen Tanshi

Legit Hausa ta kawo maku rahoton rasuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi, wanda ya koma ga mahaliccinsa a daren Juma'a bayan doguwar jinya.

Haka nan kuma an yi jana'izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanada da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Juma'a, 4 ga watan Afrilun 2025.

Malamai musamnan na sunnah a Najeriya, shugabanni da sauran manyan mutane sun yi ta'aziyyar rasuwar wannan babban malami tare da addu'ar Allah gafarta masa.

Sheikh Gumi ya yi ta'aziyyar Dutsen Tanshi

Da yake miƙa sakon jaje da alhinin wannan rashi, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa marigayin yana da abin al'ajabi kuma ya yi kura-kurai a rayuwarsa.

Sai dai Dr. Gumi ya jadadda cewa Malam Idris mutum ne da ya tsayu a kan tauhidi, inda ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 19 sun yi maganar rasuwar babban malami, Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Wane abin al'ajabi Dutsen Tanshi ke da shi?

"Yau Allah ya yi wa Malam Idris Abdul'Aziz Dutsen Tanshi rasuwa a Bauchi. Wannan bawan Allah abin shi akwai al'ajabi, Allah ya tsayar da shi a kan tauhidi."
"Allah don wannan Tauhidi Allah ka mai rahama ka gafarta masa, amma kuma yana da kura-kurai, yana da kura-kurai na iya da'awa da kuma zagi da sukar mutanen ba su ji ba, ba su gani ba.
"Abin al'ajabin shi ne malam (Marigayi Abubakar Gumi) da ya assasa sunnah a nan da tauhidi, sai ƴan ɗarika suka je Bauchi suka ɗauko malami domin ya yi faɗa da malam, shin ya iya rusa karatun malam?
"Sai ga shi mu ba mu aika kowa ya rusa da'awarsu ba ko? Sai Allah ya fitar daga tsakiyar Bauchi wanda ya zo ya tsaya kai tsaye ya nuna abin da suke yi kuskure ne. Sabida haka mun gode Allah, Allah Ya gafarta masa."

Kara karanta wannan

"Mutane sun manta": Tinubu ya faɗi aikin da Sheikh Dutsen Tanshi ya yi wa Najeriya

- Sheikh Ahmad Gumi.

Gwamnoni sun yi jimamin rasuwar Dutsen Tanshi

A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan marigsyi Sheikh Idris Dutsen Tanshi.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin kuma gwamnan Gombe ya ce labarin rasuwar malamin ya girgiza shi domin rashi ne da ya shafi ɗaukacin al'ummar musulmi.

Gwamna Inuwa Yahaya ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, Ya sanya shi cikin Aljannar Firdaus.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng