Iyalai da Abokan Mafarautan da Aka Kashe a Edo Sun Yi Magana kan Daukar Fansa
- Ana ci gaɓa da kira ga gwamnati da ta tabbatar an yi adalci kan kisan gillar da aka yi wa wasu mafarauta 16 a jihar Edo
- Abokan aikin mafarautan da aka kashe sun yi gargaɗin ɗaukar fansa idan har ba a cafke waɗanda suka yi ɗanyen aikin ba
- Sun nuna cewa sun san hanyoyin da za su bi su je har Uromi domin zaƙulo waɗanda ke da hannu a kisan gillar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Iyalai da abokan aikin mafarauta 16 da aka kashe a Uromi, Jihar Edo, sun yi gargadin cewa za su ɗauki fansa
Mutanen sun yi gargaɗin ɗaukar fansa ne idan gwamnati ta kasa kamawa tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aikar.

Asali: Original
A cikin hirarraki daban-daban da aka yi da jaridar The Punch, abokai da iyalan wadanda aka kashe sun ce adalci ne kaɗai zai kwantar musu da hankali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yawancin mafarautan da aka kashe ƴan asalin ƙauyen Toranke ne, a ƙaramar hukumar Bunkure ta Jihar Kano.
An bukaci gwamnati ta yi wa mafarautan adalci
Wani shugaban al’umma kuma mai farauta daga Toranke, Alhaji Musa Dogo, ya ce dole gwamnati ta hukunta masu laifin.
"Ba za mu lamunci a bar wannan lamarin haka kawai ba. Waɗanda aka kashe ƴan uwanmu ne. Mun yi horo tare, mun yi yaƙi da ƴan ta’adda tare, mun kare garuruwanmu tare."
"Idan gwamnati ba ta kama wadanda suka aikata wannan kisan gilla ba tare da gurfanar da su a bainar jama’a ba, to mu da kanmu za mu ɗauki mataki."
"Mun san yadda ake bibiyar masu laifi, kuma ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba idan aka ki yin adalci."
- Alhaji Musa Dogo
Za a ɗauki fansa kan kisan mafarauta a Edo
Abokinsa Bala Danburan, wanda ke zaune tare da shi, ya ɗaga kai yana goyon bayan hakan.
"Mun san yadda za mu shiga Uromi mu ɗauki fansa da kanmu idan aka ƙi yin adalci. Wannan ba barazana ba ce, alkawari ne."
"Mun binne mutane da yawa daga cikinmu, ba za mu iya ci gaba da hakan ba. Mu farauta ne, ba mazaje marasa ƙarfi ba. Idan gwamnati ta ki ɗaukar mataki, za mu yi abin da ya dace."
- Bala Danburan
Mafarautan sun kuma buƙaci a mayar da shari’ar zuwa kotun jihar Kano, inda suka faɗi yadda gwamnatin Kano ta miƙa wani da ake zargi, Yunusa Yellow, ga gwamnatin jihar Bayelsa dangane da zargin garkuwa da mutum.
Haka kuma, wani mazaunin garin, Malam Sani Umar, ya bayyana cewa ƙaninsa Yahaya Umar na daga cikin waɗanda aka kashe.
A cewarsa, Yahaya ya bar mata da yara huɗu.
"Yahaya mutum ne mai jarumtaka, kullum yana cikin son kare rayuwar wasu. Ya yi imani da adalci, amma an kashe shi cikin rashin adalci."
"An bar mu da ciwo kawai, kuma waɗanda suka aikata haka har yanzu suna yawo a cikin ƴanci. Yaya za mu yarda da hakan? Yaya za mu iya barci idan gwamnati ba ta dauki mataki ba?"
- Malam Sani Umar
Barau ya raba tallafi ga iyalan mafarautan da aka kashe
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa iyalan mafarautan da aka kashe a Edo.
Sanata Barau Jibrin ya ba da tallafin N1m ga dukkanin iyalan mamatan da aka yi wa kisan gilla, kamar yadda ya yi alƙawari lokacin da ya je musu ta'aziyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng