Mutuwa Ta Sake Girgiza Najeriya, Mai Magana da Yawun APC Ya Rasu a Ƙasar Waje
- Mai magana da yawun jam'iyyar APC reshen jihar Ogun, Abdulraheem Tunde Oladunjoye ya rasu bayan fama da jinya a ƙasar waje
- Iyalan marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da suka fitar ranar Juma'a, sun ce za su sanar da lokacin da za a yi janaza
- Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana kaɗuwarsa bisa wannan rashi, yana mai cewa marigayin mutum ne mai kwazo da basira
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar APC reshen jihar Ogun, Alhaji Abdulraheem Tunde Oladunjoye, ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin, wanda ya kasance mai ba Gwamna Dapo Abiodun shawara kan harkokin yada labarai, ya rasu a ƙasar waje bayan fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba.

Source: Twitter
Kakakin jam'iyyar APC na jihar Ogun ya rasu
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa iyalan marigayi Tunde Oladunjoye sun tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Juma'a, inda suka ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Cikin bakin ciki da mika wuya ga Allah muna sanar da rasuwar mahaifinmu, mijinmu, ɗan’uwanmu kuma babban jagora, Alhaji Abdulraheem Olatunde Ayinde Oladunjoye, wanda ya rasu a ranar Juma’a, 4 ga Afrilu, 2025.
"Alhaji Oladunjoye mutum ne mai kima, gaskiya, da halin kirki. Rayuwarsa ta kasance cike da hidima da sadaukarwa ga jama’a.
"Bayan kasancewarsa uba nagari ga iyalinsa, ya zama uba ga da dama daga cikin al’umma. Ana girmama shi kuma an kaunace shi sosai da sosai."
- In ji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa za a sanar da shirye-shiryen jana'izarsa (Janazah) nan ba da jimawa ba.
Gwamna Dapo Abiodun ya yi ta'aziyya
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya bayyana rasuwar Oladunjoye a matsayin babban rashi da ke da matuƙar wahalar jurewa.
A cewarsa, ya girgiza da ya samu labarin rasuwar kakakin APC kuma hadiminsa, wanda ya ce ya kasance mutum mai kwazo da ƙarfin guiwa.

Source: Twitter
"Wannan labari na mutuwarsa ya girgiza ni matuƙa.Tunde mutum ne mai basira, ƙwazo da sadaukarwa wanda ya tsaya tsayin daka wajen kare manufofin gwamnati da jam’iyya.
"Ya kasance ɗaya daga cikin mutane mafi ƙwazo, mafi ƙarfin gwiwa, kuma mafi iya magana da jam’iyyar APC a Jihar Ogun ta taba samu a tarihi.
"Gaskiyarsa da rikon amana sun yi tasiri sosai wajen bunƙasa jam’iyyar APC a jihar. Oladunjoye mutum ne mai gaskiya, da tsantsar aminci. Zamu yi kewarsa ƙwarai."
- In ju Gwamna Dapo Abuodun.
Jigon PDP a jihar Oyo ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP (na Kudu), Yekini Ayoade Adeojo, ya riga mu gidan gaskiya.
An ruwaito cewa jigon jam'iyyar PDP ya rasu ne ranar Juma'a, 4 ga watan Afrilu, 2025 a gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
A 1999, Adeojo ya nemi takarar gwamna a ƙarƙashin PDP, amma ya sha kaye a hannun marigayi Alhaji Lamidi Adesina na jam’iyyar AD.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

