Kebbi: Gwamna Ya Dakatar da Malamin Musulunci a Mukami kan Maganar Luwadi
- Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya dakatar da babban sakataren Nasiru Abubakar Kigo saboda wata magana da ya yi game da Luwadi
- Kigo ya ce Kebbi da Sokoto su ne ke da mafi yawan 'yan luwadi da madigo da aka yi musu rajista, wanda ya janyo cece-kuce
- Amma tuni Gwamnatin jihar Kebbi ta ce maganar Kigo ba ta da tushe ko makama, ta kuma bayyana hakan a matsayin karya
- Kigo, wanda malamin addini ne, ya fadi hakan ne a wani taron Ramadan da aka gudanar a Birnin Kebbi kwanan nan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Birnin-Kebbi - Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya dakatar da babban sakataren na ofishin majalisar zartarwa.
Gwamnan ya dauki matakin ne kan Nasiru Abubakar Kigo, saboda wata magana da ya yi game da luwadi da madigo a jihohin Kebbi da Sokoto.

Source: Facebook
An tabbatar da dakatarwar ne a ranar Juma’a a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu ta bakin mai magana da yawun gwamnan, Ahmed Idris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kebbi ta fara daukar ma'aikata
Hakan na zuwa ne bayan Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da daukar sababbin malamai 2,000 domin inganta harkar ilimi da ilimantarwa.
Kwamishinar ilimi ta jihar, Dr. Halima Muhammad-Bande, ta ce an riga an tantance malamai 391 da suka cancanta a matakin farko.
An samu jimillar masu neman aiki 18,000, amma 4,000 ne kawai aka tantance, inda sauran jerin sunayen za su fito nan gaba.
Gwamna ya dakatar da babban sakatare a Kebbi
Nasiru Kigo ya ce Kebbi da Sokoto su ne ke da mafi yawan 'yan luwadi da madigo da aka yi musu rajista, wanda wannan magana ta jawo maganganu.
A cewarsa, an mika masa wasikar dakatarwa daga shugaban ma’aikata na jihar, Malami Shekare, bisa dokar aikin gwamnati.
Sanarwar ta ce:
“Dangane da dokokin aikin gwamnati, an dakatar da kai har sai an kammala bincike kan wannan ikirari naka.”
“Maganarka ta sabawa dabi’u, kuma tana bata sunan jihar da aka san ta da tarbiyya da kima.”

Source: Twitter
Gwamnatin Kebbi ta ƙaryata ikirarin Kigo
Gwamnatin Jihar Kebbi a baya-bayan nan ta fitar da wata sanarwa inda ta karyata ikirarin Kigo, tana cewa karya ce.
An bayyana cewa Kigo, wanda kuma malamin addinin Musulunci ne, ya fadi hakan ne a lokacin wata ganawa ta musamman.
An gudanar da taron ne a lokacin azumin Ramadan a rukunin gidaje na Adamu Aliero da ke cikin Birnin Kebbi.
Sarkin Bunza ya riga mu gidan gaskiya
Mun ba ku labarin cewa an yi rashin fitaccen Sarki a jihar Kebbi wanda ya rasu a ranar Laraba 2 ga watan Afrilun shekarar 2025.
Ɗan majalisar wakilai da ke wakiltar yankin, Hon. Ibrahim Mohammed ya nuna alhininsa kan rasuwar Sarkin Bunza, Dr. Mustapha Muhammad Bunza.
Hon. Ibrahim ya ce marigayin ya rayu da sadaukarwa ga al’umma, musamman a fannin ilimi, inda ya rike mukamai da dama na ilimi da shugabanci.
An ce marigayin ya yi mulki na tsawon shekaru 30 yana kare al’adu da ci gaban yankin Bunza, tare da ba da shawarwari ga mutane.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


