Badaƙalar Abdulrasheed Maina da Wasu Manyan Badaƙalolin Kuɗi 4 da Suka Gigita Najeriya

Badaƙalar Abdulrasheed Maina da Wasu Manyan Badaƙalolin Kuɗi 4 da Suka Gigita Najeriya

Badaƙalar cin hanci da almundahana a harkokin siyasa a Najeriya sun daɗe suna jawo hankalin jama’a da ce-ce-ku-ce, har ma da fusata a wasu lokuta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wadannan abubuwa da suka shafi rashin gaskiya, cin amana, da amfani da iko ba bisa ka’ida ba, na iya haifar da mummunar illa ga ƙasa kuma su sauya akalar siyasa.

Jami'an EFCC.
Manyan badakalolin da suka ɗaga hankalin ƴan Najeriya Hoto: EFCC
Asali: Twitter

Hukumar EFCC ta wallafa badaƙalar kudin fansho ta Abdulrasheed Maina a shafinta na yanar gizo, wacce tana ɗaya daga cikin manyan badaƙalolin da suka girgiza Najeriya.

A cikin wannan rahoto, Legit Hausa ta duba manyan badakalar siyasa guda biyar da ake ganin su ne mafi girma da suka girgiza siyasar ƙasar nan. Ga su kamar haka:

1. Badakalar cin hanci ta Halliburton

A abin da yanzu aka fi sani da “Badakalar cin hanci ta Halliburton”, wasu kamfanoni huɗu na ƙasashen waje sun jefa kansu cikin harkokin rashawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: SDP ta waiwayi manyan ƴan adawa, Atiku, Obi da Kwankwaso, ta mika masu buƙata 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanoni sun haɗa da KBR (reshe na Halliburton), Technip daga ƙasar Faransa, Snamprogetti (reshe na kamfanin ENI daga Italiya), da Gasoline Corp daga Japan, sun biya fiye da Dala miliyan 180 a matsayin cin hanci ga jami'an Najeriya.

Cikin waɗanda suka danne waɗannan kudi har da wasu tsofaffin shugabannin ƙasa da manyan jami'an Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) a tsakanin 1993 da 2004.

Kamfanonin sun biya waɗannan kudi ne domin samun kwangilar gina matatar iskar gas mai a Bonny Island da ke yankin Neja Delta.

An tilasta wa wadannan kamfanoni huɗu biyan tarar Dala biliyan 1.65 ga Amurka sakamakon karya dokar cin hanci bisa ƙa'idar dokar FCPA.

Wasu 'yan ƙasashen waje da ke da hannu a cikin lamarin an gurfanar da su a ƙasashensu kuma an hukunta su.

2. Badaƙalar Diezani Alison-Madueke

Diezani Alison-Madueke ta kasance Ministar Albarkatun Man Fetur daga shekarar 2010 zuwa 2015, a lokacin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Iyalai da abokan mafarautan da aka kashe a Edo sun yi maganar daukar fansa

Tun kafin ranar da Jonathan ya mika mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari a 2015, ta tattara kayanta ta bar ƙasar.

Diezani.
EFCC ta tuhumi tsohuwar ministar man fetur Hoto: @TrendingEX
Asali: Twitter

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta zargi tsohuwar Ministar da satar dala biliyan 2.5 daga asusun gwamnatin Najeriya yayin da take kan mulki.

Ita kuwa ta musanta zargin, amma duk da haka EFCC ta fara ɗaukar matakan dawo da ita Najeriya domin fuskantar shari’a.

Gwamnatin tarayya ta samu umarnin kotu na ƙwace kadarorin Diezani da ke cikin Banana Island Foreshore Estate, Ikoyi, Lagos, ciki har da gidaje 18 da gine-ginen sama guda shida.

3. Badakalar sayen motocin sulken Stella Oduah

A 2013, Sanata Stella Oduah ta faɗa cikin rikicin siyasa kan zargin siyan motoci masu kariya daga harbi.

Lokacin ta na ministar sufurin jirgen sama, rahotanni sun bayyana cewa Stella ta tilasta Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta saya mata motocin.

Stella Oduah.
Yadda EFCC ta binciki Stella Oduah Hoto: Stella Oduah
Asali: UGC

Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce a fadin ƙasa, inda wasu ‘yan fafutuka kamar Femi Falana (SAN), suka bukaci EFCC ta gudanar da cikakken bincike domin gurfanar da tsohuwar Ministar.

Kara karanta wannan

Ta tabbata Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP? An samu bayanai

Sai dai Stella Oduah, wadda ta zama sanata a 2015, ta ci gaba da musanta aikata wani laifi.

A martaninta ga tambayar da tsohon Shugaba Jonathan ya yi a watan Oktoba 2013, ta bayyana cewa sayen motocin yana cikin kasafin kuɗin NCAA, kuma an biya kudin cikin shekara uku.

4. Badakalar Farouk Lawan da Femi Otedola

A watan Fabrairu na shekarar 2013, an gurfanar da Farouk Lawan da laifin cin hanci bayan da aka zarge shi da karɓar $500,000 daga biloniya ɗan kasuwan mai, Femi Otedola.

Kudin dai wani ɓangare na Dala miliyan 3 da ake zargin Farouk Lawan ya nema daga wurinsa a matsayin na goro.

Otedola ya yi ikirarin cewa Frouk ne ya nemi kudin domin cire kamfaninsa, Zenon, daga jerin kamfanonin da kwamitin majalisar wakilai ya taso kan wata badakala.

Daga baya an tura Farouk Lawan gidan yari. A watan Janairun 2024, Kotun Koli ta ƙi amincewa da ƙorafin da ya shigar kan hukuncin karamar kotu wadda ta yanke masa hukunci dauri.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin kamfanin NNPCL tun daga kafuwarsa da jihohinsu

A watan Oktoban shekarar nan, aka sako shi daga gidan yari, kamar yadda jaridar Premium.Times ta kawo.

5. Shari’ar Fansho ta Abdulrasheed Maina

Abdulrasheed Maina ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho a lokacin gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan.

Sai dai ya tsere daga Najeriya a shekarar 2015 bayan an fara zarginsa da karkatar da Naira biliyan 2 (kimanin Dala miliyan 5.6 ko Yuro miliyan 4.8).

Abdulrasheed Maina.
Badakalar kudin fansho ta Abdulrasheed Maina ta ja hankali a Najeriya Hoto: Abdulrasheed Maina
Asali: UGC

Ko da yake an fitar da sammacin kama shi ta hannun Rundunar 'Yan Sanda ta Ƙasa da Ƙasa (Interpol), hakan bai hana shi dawowa Najeriya ba, aka ce ya samu kariya daga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Gwamnatin Jonathan ce ta kore shi daga aiki tare da fara bincike a kansa bisa zargin cin hanci, amma daga baya gwamnatin Buhari ta dawo da shi aiki tare da ba shi karin matsayi har sau biyu.

Daga ƙarshe, an same shi da laifin halasta kuɗin haram kuma kotu ta yanke masa hukuncin dauri a gidan gyaran hali, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ruwa ya yi gyara: Gidaje sama da 70 sun yi fata-fata a Filato

EFCC ta taso gwamnatin Bauchi a gaba

A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta danke Akanta-Janar na gwamnatin jihar Bauchi bisa zargin karkatar da kudi kimanin Naira biliyan 70.

EFCC ta kama Sirajo Jaja a Abuja a ranar Laraba, 19 ga Maris, 2025, tare da Aliyu Abubakar na kamfanin Jasfad Resources Enterprise da wani mai sana'ar POS.

An ruwaito cewa an cire Naira biliyan 59 daga asusun banki daban-daban, wanda ake zargin shi Akanta Janar din ya bude a madadin gwamnatin Bauchi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng