Bayan Jana'izar Dr Idris, Wani Limami Ya Ja Sallar Juma'a a Masallacin Dutsen Tanshi
- Bayan rasuwar Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wani limami da ba a saba ganinsa ba ya hau mimbarinsa ya gabatar da hudubar Juma'a
- Limamin ya jaddada cewa kowa zai mutu, kujerar mulki ko wa'azi ba ta dawwama, kuma duk wanda ke kai zai sauka wani ya hau wata rana
- Ya tuna da irin gaskiyar da Dr Idris ke fada, yana cewa Dr Idris ya zama na karshe daga cikin malaman da ke faɗin gaskiya ba tare da tsoro ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - 'Yan awanni da kammala jana'izar marigayi Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, babban malamin addini a Bauchi, wani limami ya hau mumbarinsa.
Mallam Idris Dutsen Tanshi ya rasu ne a daren ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025 a gidansa da ke Bauchi, bayan fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan
'Abin da Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya faɗa kafin rasuwarsa': Ɗalibinsa ya magantu

Asali: Facebook
A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Dutsen Tanshi Majlis Bauchi na Facebook, an ga wani malami, bakuwar fuska, yana gabatar da hudubar Juma'a a masallacin marigayin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Limami ya yiwa mabiyan Dutsen Tanshi nasiha
A hudubar da sabon limamin ya gabatar, ya tunatar da mabiya marigayi Idris Dutsen Tanshi cewa:
"Muna yi wa junanmu ta'aziyya, na rashin wannan babban malami. Jama'a, mutuwa ta na a kan kowa, amma rashin babban malami irin wannan malamin, babbar asara ce.
"Annabi Muhammad (SAW) ya yi rashin lafiya, kamar yadda mallam ya yi rashin lafiya. Manzon Allah ya samu sauki, sannan Allah ya dauki rayuwarsa, shi ma mallam ya samu sauki sannan ya rasu."
Yayin da ya ke magana kan tabbatuwar mutuwa a kan kowa, limamin ya ce:
"Wata rana, wurin da kake dole za ka matsa, kujerar da kake a kai dole za ka sauka wani ya hau, munbarin da kake a kai dole za ka sauka wani ya hau, idan kai mai mulki ne, ka da mulkin ya rude ka, wata rana za ka matsa wani ya hau."

Kara karanta wannan
"Yana da abin al'ajabi da kura kurai," Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan Dutsen Tanshi
'Dr Idris ba ya tsoron fadin gaskiya' - Limami
Limamin ya tuno yadda manyan malamai masu fadin gaskiya a Najeriya ke komawa ga mahalaccinsu, inda ya buga misali da rasuwar Mallam Albani Zariya da Sheikh Jafar Mahmud Adam.
Limamin ya ce:
"Mun yi asarar irinsu Shiek Jafar da Albani Zaria. Mutane suna cewa, yanzu a Najeriya, a iya abin da ya bayyana, Mallam Idris ne ya rage mana, a wajen fadin gaskiya komai dacinta.
"Mallam ne kawai ya ke iya tunkarar gaskiya a fade ta, ko ta yi dadi ko kar ta yi dadi, bai yi don ya fada maka ko faranta maka rai ba, ya fade ta a matsayinta ta gaskiya.
"Shi ne kadai cikin wadanda suka rage idan sun ga bidi'a, sun ga ba daidai ba ko wa ya yi ta, ko shi ya yi ta zai fito ya fada, kuma ko ya kuke da shi, ganin ido ba ya hana shi ya ci kai."

Kara karanta wannan
"Mutane sun manta": Tinubu ya faɗi aikin da Sheikh Dutsen Tanshi ya yi wa Najeriya
Mutane sun yi alhinin rasuwar Dutsen Tanshi
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin sakonnin ta'aziyya da mutane suka aika na rasuwar Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi:
Aly Tureta"
"Idanu sun kasa daina zubar da hawaye, amma tuno da mafificin halitta da yafi kowa ya yayi wafati, ke sanyaya zuciya. Rayuwar can ta fi ta nan ga malam insha Allah."
Umar Garba Namalam"
"Juma'ar farko ba tare da Dakta ba, Allah ya jikanka Dr Dutsen Tanshi, hakika duniya ta yi rashi."
Murtala Mohammed"
"Allah ya jikansa da rahama, gaskiya musulunci ya yi babban rashi."
Kabiru Usman Ya Aqub:
"Allahu Akbar kabiran. Ina yi wa 'yan uwa musulman duniya ta'aziyya, Allah ya kai haske kabarin malam."
Shuaib Ahmad:
"Muna nan a kan akidar mu, ba mu kasance muna makauniyar bibiya ga Dakta ba, muna nan a kan abin da ya daura mu."
Amiru Aliyuu Ladda"
"Rayuwa kenan, Allah ya jikan Dakta."

Kara karanta wannan
'Haka suka yi wa Albany': Dutsen Tanshi ya fadi abin da yake tsammani bayan ya mutu
A zantawar Legit Hausa da Mubarak Mahmud, mazaunin Unguwar Jahun, Bauchi, ya nuna kaduwa da rasuwar Mallam Idris. Mubarak ya ce:
"Shi fa Dakta Idris sai dai ka ƙi gaskiya, amma malami ne da ke karantarwa bisa gaskiya da rashin tsoro.
"Wallahi da ace wani malami ne ya fuskanci irin abin da Dakta Idris ya fuskanta, da tuni ya daina da'awa. Amma har rasuwarsa, yana nan a kan fadin gaskiya.
"Zahiri mun yi babban rashi a Bauchi. Kuma muna addu'ar Allah ya jikan Mallam, ya sa dalibansa su dora daga inda ya tsaya."
Ita ma Mamah Khadija, daga Unguwar Rail Way, Bauchi, ta ce mutuwar malamin ta girgiza ta sosai.
"Na kwana biyu ban ji mutuwa irin ta wannan ɗan tahalikin ba. Duk azumi za ka ji ana sanya karatunsa a rediyo, muna saurare.
"Ko wannan azumin ma ya yi karatu. Kwatsam muka ji cewar ya rasu. Na shiga damuwa sosai. Malamai sai rasuwa suke yi, karshen duniya kenan."
- Mamah Bauchi.
Kalli bidiyon a nan kasa:
Muhimmin Abubuwa game da Dakta Idris
Tun da fari, mun ruwaito cewa, marigayi Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya rayu ne a kan wasu muhimman abubuwa 7 da suka hada da tsayuwa a kan tauhidi.
An ce malamin ya kasance mai riko da Sunnar Annabi Muhammad (SAW), kuma ya kasance a sahun gaba wajen kawo abubuwan da za su inganta rayuwar al'umma.
Asali: Legit.ng