'Inyamurai Sun Rufe Shaguna': Halin da Ake ciki a Sokoto kan Kisan Hausawa a Edo

'Inyamurai Sun Rufe Shaguna': Halin da Ake ciki a Sokoto kan Kisan Hausawa a Edo

  • Fargaba ta mamaye Sokoto, musamman a unguwannin Inyamurai bayan jita-jitar harin ramuwar gayya saboda kisan Hausawa 16 a Edo
  • Yawancin Inyamurai sun rufe shagunansu domin gudun tashin hankali, musamman a unguwannin Emir Yahya, Sahara da Aliyu Jodi
  • Sai dai rundunar 'yan sanda ta tabbatar da shirin samar da tsaro, inda aka baza jami'ai a birnin duk da babu rahoton kai hari zuwa yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - An shiga fargaba a jihar Sakoto sakamakon jita-jitar zanga-zangar da ake shirin yi da kuma zargin kai harin ramuwar gayya kan kisan Hausawa 16 da aka yi Edo.

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa wasu bata gari sun tare motar fasinjoji a garin Uromi, jihar Edo, inda suka kashe mafarauta 16 da ke hanyar zuwa Kano.

Kara karanta wannan

Hausawa da Fulani sun gwabza fada a Zamfara, an zubar da jini

Inyamuran da ke zaune a Sokoto sun rufe shaguna saboda tsoron harin ramuwar gayya
Sokoto: Inyamurai sun rufe shaguna saboda fargabar harin ramuwar gayya kan kisan Hausawa a Edo.
Asali: Getty Images

Inyamurai sun rufe shagunansu a Sokoto

Wakilin jaridar Punch da ke Sokoto ya lura a ranar Juma’a cewa an rufe yawancin shagunan da baƙi ke gudanar wa, musamman Inyamurai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce an rurrufe yawancin shagunan da ke cikin unguwannin da Inyamurai suka fi yawa birnin jihar, irin su Bello Way, Emir Yahya, Sahara da Aliyu Jodi.

Wani mai shago da ya bayyana sunansa da Chinedu, ya ce tsoron kai masu harin ramuwar gayya ne ya sa ya rufe shagonsa, inda ya ce yana gudun ya yi asarar dukiyarsa.

“Mun ji jita-jitar cewa wasu matasa za su yi zanga-zanga bayan sallar Juma’a, kuma hakan na iya kai wa ga kai harin ramuwar gayya, shi ya sa muka dauki matakin rufe shaguna.
“Ba za mu jira abin ya faru ba kafin mu yi shiri, shi ya sa muka rufe shagunanmu."

- Inji Chinedu.

Dalilin Inyamurai na rufe shaguna a Sokoto

Kara karanta wannan

Uromi: Barau ya yi alkawari bayan ziyarar iyalan Hausawan da aka kashe a Edo

Haka zalika, wani Inyamuri da ke sayar da tayar motoci a Unguwar Sahara ya ce tsoron masu fasa shaguna ne ya sa suka rufe nasu shagonsu.

Mutumin da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce suna son daukar matakin gaggawa don kada su rasa dukiyarsu a irin wadannan tashe-tashen hankulan.

Ya sanar da cewa:

“Lokacin zanga-zangar da aka yi kan marigayiya Deborah, an yi amfani da damar wajen kai hari da fasa shagunanmu, shi ya sa muka yanke shawarar daukar mataki tun wuri."

'Yan sandan Sokoto sun yi martani

'Yan sandan Sokoto sun yi martani kan halin da ake ciki a Sokoto bayan harin Edo
'Yan sanda sun tabbatar da ba da tsaro a Sokoto da ake fargabar harin ramuwar gayya. Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

A bangarenta, rundunar ‘yan sanda ta Najeriya reshen jihar Sokoto ta tabbatar da cewa tana cikin shiri domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Ahmed Rufai, yayin da yake magana da wakilin jaridar, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa sassan birnin domin tabbatar da doka da oda.

Sai dai wakilin jaridar ya tattaro cewa babu wani rahoton kai hari da aka samu har zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto.

Kara karanta wannan

Uromi: An jibge jami'an tsaro a garin da aka hallaka Hausawa 16 a Edo

Edo: Halin da ake ciki a garin Uromi

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu mazauna Uromi sun fara barin gidajensu saboda fargaba da ta biyo bayan kisan gillar da aka yi wa Hausawa a jihar Edo.

Rahotanni sun ce al’ummar yankin na nuna damuwa kan yadda ake cafke mutane ba tare da cikakken bincike ba, alhali wadanda suka aikata laifin sun tsere tun tuni.

Mazauna Uromi sun shiga firgicin ne bayan hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike tare da damke wadanda ake zargin na da hannu a kisan Hausawa 16.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.