"Mutane Sun Manta": Tinubu Ya Faɗi Aikin da Sheikh Dutsen Tanshi Ya Yi wa Najeriya

"Mutane Sun Manta": Tinubu Ya Faɗi Aikin da Sheikh Dutsen Tanshi Ya Yi wa Najeriya

  • Mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin musulunci, Dr. Abdul'Aziz Idris Dutsen Tanshi
  • Bola Tinubu ya bayyana cewa aikin da malamin ya yi wajen yaƙi da tsattsauran ra'ayi da ta'addanci a Arewa maso Gabas ya nuna irin jajircewarsa
  • Shugaban Najeriya ya roki Allah ya gafarta wa Sheikh Dutsen Tanshi kuma ya ba iyalansa da almajiransa haƙurin jure wannan rashi da aka yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen malamin addinin Islama daga Bauchi, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.

Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya rasu ne a daren ranar Juma'a yana da shekaru 68 a duniya.

Shugaba Tinubu da Idris Dutsen Tanshi.
Shugaba Tinubu ya yi alhinin rasuwar Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Shugaba Tinubu ya yi ta'aziyyar rasuwar malamain a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar kuma jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 19 sun yi maganar rasuwar babban malami, Sheikh Idris Dutsen Tanshi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka yi janazar Dr. Idris Dutsen Tanshi

Da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Juma'a aka yi janazar Dutsen Tanshi a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Dubban mutane da suka haɗa da malamai da da ɗaliban ilimi ne suka halarci janazar marigayin domin roka masa gafarar Allah SWT.

Tinubu ya tuna gudummuwar Dutsen Tanshi

Da yake miƙa sakon ta'aziyya, Bola Tinubu ya yabi marigayi Dutsen Tanshi bisa gudummuwar da ya bayar wajen yaki da tsattsauran ra'ayi a Arewa maso Gabas.

Tinubu ya ƙara da cewa Malam Idris ya kasance jagora mai kyakkyawan hali wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen ilmantar da matasa da musulmi da dama kan koyarwar addinin Islama.

Shugaban ƙasa ya ce:

“Gudummawar da Dr. Abdulaziz ya bayar wajen yaƙar yaɗuwar ta’addanci, musamman a shekarun farko na rikicin Boko Haram, hujja ce ta jarumtarsa da sadaukarwarsa ga zaman lafiya.”

Shugaba Tinubu ya miƙa sakon ta'aziyya

Kara karanta wannan

Abin da malaman Musulunci ke fada game da rasuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Haka nan, Tinubu ya yaba da jajircewar malamin wajen koyar da kyawawan ɗabi’u da gaskiya.

Ya ce al’ummar musulmi za su yi babban rashi, domin an rasa jagora mai tsantsar basira da hangen nesa, kamar yadda Leadership ta kawo.

Shugaba Tinubu.
Shugaba Tinubu ya tuna da taimakon da Dutsen Tanshi ya yi wa Najeriya a yaki da ƴan Boko Haram Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa ya yi addu’a Allah ya ji kan sa, sannan ya roƙi iyalansa, almajiransa, da masoyansa su yi haƙuri da wannan rashi.

Ya ce idan suka duba irin tasirin da rayuwarsa ta yi a duniya za su samu nutsuwa tare da fatan Allah Ya masa rahama.

Dr. Idris Abdulaziz ya kasance ɗaya daga cikin manyan malaman addinin Islama a Arewacin Najeriya.

Yadda Dutsen Tanshi ya dawo Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Idris Dutsen Tanshi ya sha fama da jinyar da ta kai ga fita zuwa ƙasar Indiya neman magani kafin Allah SWT ya masa rasuwa.

An ce lokacin da Sheikh Idris ya je asibiti a ƙasar Indiya, likitoci sun bukace shi da ya ci gaba da zama a can don ci gaba da shan magunguna da shirin tiyata.

Amma malamin bai amince da haka ba, yana mai cewa zai fi so ya koma gida Najeriya, domin idan mutuwa ta zo, ta riske shi a cikin iyalai da ‘yan uwa Musulmai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262