Abin da Malaman Musulunci ke Fada game da Rasuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Abin da Malaman Musulunci ke Fada game da Rasuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

A safiyar ranar Juma’a, daruruwan Musulmi suka hallara a jihar Bauchi domin jana’izar Sheikh Abdulazeez Dutsen Tanshi.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Fitaccen malamin ya rasu a daren Juma’a, 4 ga watan Afrilu na shekarar 2025, bayan ya shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.

Tanshi
Malamai sun yi ta'aziyyar Dutsen Tanshi Hoto: Bala Lau/Jibwis Nigeria/Umar Shehu Zaria
Asali: Facebook

Legit ta tattaro abubuwan da wasu daga cikin manyan malaman addinin Musulunci suka fada yayin ta’aziyyar mashahurin malamin.

1. Sheikh Pantami ya yi ta’aziyyar Dutsen Tanshi

Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya nuna alhini kan rasuwar babban malamin Musulunci, Dr. Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Pantami ya bayyana cewa wannan babban rashi ne ga al’umma, musamman a wajen malamai da ɗalibai.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rasuwar Dutsen Tanshi, an sanar da mutuwar fitaccen Sarki a Kebbi

Farfesa Pantami ya yi ta'aziyya tare da addu’ar Allah ya jikansa kuma ya gafarta masa kura-kuransa, tare da yi masa fatan Al-jannah.

2. ‘Izala ta yi rashin Dutsen Tanshi’ — Bala Lau

Shugaban ƙungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan marigayi Sheikh Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma'a a jihar Bauchi.

A cikin saƙon ta'aziyyarsa, Sheikh Bala Lau ya bayyana rasuwar malamin a matsayin babban rashi ga Ahlus-Sunnah da al’ummar Musulmi gaba ɗaya.

Tanshi
Marigayi, Sheikh AbdulAzeez Dutsen Tanshi Hoto: Jibwis Nigeria
Asali: Facebook

Ya ce:

"Allah ka gafarta masa kurakuransa, ka sanya Aljanna ce makomarsa, ka kyautata bayansa, ka ba wa iyalansa dangana.”

Sheikh Bala Lau ya roƙi Allah da Ya ji kan Sheikh Idris da rahama, Ya sanya haske a kabarinsa, kuma Ya ba iyalansa ƙarfin gwiwa.

Ya kuma bayyana cewa marigayin ya yi ayyuka masu yawa na hidima ga addini da koyar da Sunnah, don haka ya roƙi al’umma da su ci gaba da yi masa addu’a da neman rahama.

Kara karanta wannan

Yadda Dutsen Tanshi ya dawo Najeriya daga Indiya duk da tsananin rashin lafiya

3. Umar Zaria ya yi alhinin rasa Dutsen Tanshi

A nasa ɓangaren, Sheikh Umar Zaria ya bayyana kaduwarsa da samun labarin rasuwar Sheikh Abdulazeez Dutsen Tanshi, wanda ya koma ga Allah SWT a daren Juma’a.

A jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Facebook, malamin ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa.

Ya ce:

"Innaa lillahi wa innaa ilaihi raaji’un. Yanzu nake samun labarin rasuwar Sheikh Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi. Allah Ta'ala ya gafarta masa kuma ya kyautata namu bayan nashi."

4. Addu’ar da Dr. Asgar ya yi wa Dutsen Tanshi

Dr. Kabir Abubakar Asgar, a sakon da ya wallafa a Facebook, ya bayyana alhini kan rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi.

Yayin da yake yi wa marigayin addu’a, malamin jami'ar na ABU Zaria ya ce:

"Allah Ubangiji ya jiƙan Dr. Idris Abdulazeez Bauchi. Allah ya sa mutuwa hutu ce a gare shi. Allah ya gafarta mana, mu da shi baki ɗaya."

Kara karanta wannan

Hotuna: Yadda musulmi suka yi cikar ƙwari a wurin janazar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Atiku ya yi ta’aziyyar Dutsen Tanshi

A baya, mun ruwaito cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana alhini kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi.

A cikin sakon ta'aziyyarsa da ya fitar a safiyar Juma’a, Atiku ya bayyana marigayin a matsayin malami mai kishin yada ilimi da zaman lafiya a tsakanin al’umma, tare da kira ga Allah.

Ya ce malamin ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina al’umma ta hanyar koyarwa da bayar da fatawowi, kuma mutum ne mai nagarta da ilimi, kuma rashinsa zai taba musulmi baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng