'Muna Kallonka': Jam'iyyar SDP Ta Ja Kunnen El Rufai da Sababbin Mambobinta

'Muna Kallonka': Jam'iyyar SDP Ta Ja Kunnen El Rufai da Sababbin Mambobinta

  • Majalisar shugabannin SDP ta gargadi Nasir El-Rufai da sababbin mambobi da su bi tsarin jam’iyyar, su guji tsoma baki a shugabancinta
  • Shugaban SDP na Legas, Femi Olaniyi, ya ce ba za su canja tsarin mulki, tambari, ko take ba don sababbin mambobi ko faranta ran wani ba
  • Femi Olaniyi ya bukaci sababbin mambobi da su yi rajista ta hanyar shugabannin gunduma, ba tare da karya tsarin cikin gida na SDP ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Majalisar sugabannin jam'iyyar SDP ta gargadi tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da sabbin mambobinta da ma masu niyyar shiga jam'iyyar.

SDP ta ce ya zama dole El-Rufai da sauran baki su bi tsarin jam'iyyar, su kuma guje wa kokarin canza shugabancin jam'iyyar ko tsarin da take tafiya a kansa.

Kara karanta wannan

APC ta yi bayani kan shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Jam'iyyar SDP ta gargadi El-Rufai da sababbin 'yan jam'iyyar
SDP ta ce ba za ta yi canje-canje saboda El-Rufai ko sababbin 'yan jam'iyyar ba. Hoto: @elrufai
Asali: Twitter

Shugaban SDP na Legas, Femi Olaniyi, ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Alhamis, inda mambobi 25 suka halarta, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan siyasa ke sauya jam'iyya Najeriya

Shugabannin jihohin sun kuma nuna goyon baya ga shugaban SDP na kasa, Shehu Gabam, da Sakatare na kasa, Dr. Olu Agunloye, da dukkan mambobin kwamitin aiki na Jam'iyyar.

Legit Hausa ta ruwaito cewa an samu yawan sauye-sauyen 'yan siyasa daga jam'iyyun APC, PDP, LP da PRP a cikin watanni biyu da suka gabata.

Ban da El-Rufai, wani shahararren mawaki kuma tsohon mamba na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Obinna Simon, wanda aka fi sani da MC Tagwaye, ya koma SDP.

Hakazalika, wasu tsofaffin 'yan takarar gwamna na PRP kamar Emiyare Etete (Rivers), Chris Agu (Enugu), Anthony Umeh (Anambra) da Abdulkareem Mustapha (Kwara) suma sun koma SDP.

Kara karanta wannan

'Ka gaggauta daukar mataki': An fadawa Tinubu abubuwa 2 da ke barazana ga Najeriya

"Ba za mu canza tsarin jam'iyya ba" - SDP

Duk da cewa SDP na samun karuwar mambobi, Femi Olaniyi, ya ce ba su bukatar canza shugabanci ko sauya tambari da kundin tsarin aiki na jam'iyyar.

Jaridar The Nation ta rahoto shugaban SDP na Legas din ya ce:

"Muna maraba da zuwan sababbin mambobi cikin jam'iyyar mu, ciki har da fitattun 'yan siyasa daga sassan kasar. Mun fahimci cewa akwai gyare-gyaren da sun zama wajibi a yi.
"Sai dai, ba za mu yarda wani ya kawo kudurin canjin suna, tambari, alama, take, ko babban sauyi akan kundin tsarin mulki ko manufofin jam'iyyar ba.
"Ba za mu yarda a canja tsarin mulki na SDP a matakin jihohi da na kasa don dacewa da sababbin mambobi ko wani mutum ba. Dole ne a bar jami'an da aka zaba su kammala wa'adinsu."

"SDP ba ta tsoron zuwan El-Rufai" - Olaniyi

Shugabannin SDP sun yi magana kan ko suna tsoron El-Rufai ya kwace ikon jam'iyyar
Shugabannin SDP sun ja kunnen El-Rufai da sababbin masu shiga jam'iyyar. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

A cewar Olaniyi, dole ne sababbin mambobi su shiga SDP ta hanyar yin rajista a gundumominsu, tare da gargadin masu fitowa suna bayyana kansu a matsayin mambobin jam'iyyar gaba gadi.

Kara karanta wannan

'Ba zan yi sata ba': Ɗan majalisa ya cire tsoro a gaban ƴan mazabarsa bayan shan suka

An tambayi Olaniyi ko suna jin tsoron cewa El-Rufai da wasu manyan 'yan siyasa za su shigo cikin SDP su kuma kwace mulkin jam'iyyar, sai cewa ya yi:

"Ba mu jin tsoron mutum ya shigo jam'iyyar mu. Muna maraba da tasirin sababbin mambobi cikin jam'iyyar. Amma ba mu son masu shigo wa cikinta don tayar da tarzoma."
"Wai don ka shigo jam'iyyar tare da mutane 30,000 zuwa sama da 40,000, to wannan ba shi zai sa ka yi tsammanin samun shugaba ko sakataren jam'iyya ba."

El-Rufai ya fice daga APC zuwa SDP

Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya fice daga jam'iyyar APC da ya sa hannu aka assasa ta saboda sauya wa manufofinta.

A cikin wata wasika da ya aike wa shugaban APC na gundumarsa, El-Rufai ya ce yanzu APC ta sauka daga turbar da aka gina ta, don haka ya koma jam'iyyar SDP.

Sauya shekar tsohon gwamnan na zuwa ne bayan an gan shi ya na ganawa da manyan jiga-jigan 'yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar da Rauf Aregbesola.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.