An Nemi Tinubu Ya Kafa Sansanin Soji a Garin da aka Kashe Hausawa a Edo
- Sarkin Uromi, Zaiki Anslem Eidenojie II, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya kafa sansanin soji a Uromi don inganta tsaro
- Zaiki Anslem Eidenojie II ya ce an gina sansanin Mopol a yankin, amma har yanzu ba a yi amfani da shi yadda ya kamata ba
- Ya kuma yi Allah-wadai da kashe matafiya da aka yi a Uromi, yana mai cewa rashin tsaro ya kara tabarbarewa a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Sarkin Uromi, Zaiki Anslem Eidenojie II, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta amince da karɓar sansanin Mopol da aka gina a yankin don bai wa ‘yan sanda damar inganta tsaro.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a Benin, inda ya ce sansanin ya kasance a Uromi tsawon lokaci ba tare da amfani da shi yadda ya kamata ba.

Kara karanta wannan
Wike ya fadi halin da yake ciki bayan cewa ya yanki jiki ya fadi, an tafi da shi Faransa

Asali: Twitter
The Guardian ta wallafa cewa ya yi Allah-wadai da kisan wasu matafiya ‘yan Arewa a yankin, yana mai cewa hakan wata alama ce da ke nuna yadda matsalar tsaro ta kazanta a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Neman a gina sansanin soji a Uromi
Sarkin Uromi ya ce sansanin ‘yan sandan Mopol da aka gina a yankin da nufin karfafa tsaro ba a amfani da shi sosai.
“Mun gina wannan sansanin ne da gudunmawar ‘yan uwanmu da ke gida da kasashen waje, amma har yanzu ba a amfani da shi yadda ya kamata.
"Gwamnatin tarayya ta karɓe shi don tabbatar da tsaro a Uromi,”
In ji sarkin Uromi
Sarkin ya kara da cewa ya zama dole a kafa sansanin soji a yankin domin samar da kwanciyar hankali
Uromi: Maganar kisan Hausawa a Edo
Basaraken ya nuna matukar takaicinsa kan yadda wasu ‘yan Arewa da ke tafiya gida don bukukuwan sallah suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu suka kai musu.
Sarkin ya ce:
“Lamarin ya faru tsawon sa’o’i ba tare da wani dauki daga ‘yan sanda ba. Wannan babban al’amari ne da ke nuna gazawar tsaro a yankinmu,”
Baya ga haka, ya kuma jajanta wa iyalan mamatan, al’ummar Kano da duk wadanda lamarin ya shafa da cewa:
“Mutanenmu ma na fama da matsalar garkuwa da kashe-kashe da ba bisa ka’ida ba. Dole ne gwamnati ta tashi tsaye don kawo karshen wadannan matsaloli,”
Bukatar karin jami’an tsaro a Edo
Sarkin Uromi ya bukaci gwamnatin Edo da ta hada kai da shugabannin yankin don tabbatar da amincewa da sansanin MOPOL da kuma kara tura jami’an tsaro yankin.
“Ya kamata a kara yawan jami’an tsaro tare da amfani da wadannan gine-gine da aka tanada domin su,”
- Zaiki Anslem Eidenojie II
Ya kuma yi gargadin cewa idan ba a dauki mataki ba, matsalar tsaro za ta ci gaba da ta’azzara a yankin, lamarin da zai jefa al’ummar Uromi cikin damuwa.

Asali: Facebook
APC ta zargi PDP kan kashe Hausawa a Edo
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta zargi PDP da haddasa kisan Hausawa a jihar Edo suna dawowa gida hutun sallah.
Shugaban APC na jihar ya yi zargin cewa PDP tana son amfani da rikicin ne wajen hana abubuwa tafiya a jihar bayan faduwa zabe.
Baya ga haka, shugaban jam'iyyar ya ce PDP na neman gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta sanya dokar ta baci a jihar saboda lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng