Natasha za Ta Fitar da Hujjoji kan Zargin Neman Lalata da Ta Yi wa Akpabio

Natasha za Ta Fitar da Hujjoji kan Zargin Neman Lalata da Ta Yi wa Akpabio

  • Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce za ta gabatar da hujjojin zargin neman lalata da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi mata
  • Haka zalika Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yabawa hukumar zabe ta INEC bisa kin amincewa da korafin mata kiranye daga majalisa
  • Sanata Natasha ta yi magana ne bayan INEC ta bayyana cewa korafin kiranye da ake son yi mata bai cika sharuddan kundin tsarin mulki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta ce ba da jimawa ba za ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zargin da ta ke yi wa Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio.

Ta kuma ce hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi daidai da kin amincewa da korafin mata kiranye, ka da yake ta ce bai kamata a ma fara karɓar koken ba tun da farko.

Kara karanta wannan

INEC ta sanar da shugaban Majalisa matakin da ta ɗauka kan buƙatar tsige Sanata Natasha

Natasha
Natasha ta ce za ta fitar da hujjoji kan zargin da ta yi wa Akpabio. Hoto: Nigerian Senate
Asali: Twitter

Ta bayyana haka ne a wani shiri na tashar Channels TV a ranar Alhamis, inda ta ce za ta fitar da shaidar a lokacin da ya dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Natasha za ta fitar da hujjoji?

Sanata Natasha ta ce tana da hujjoji da ke nuna cewa Shugaban Majalisar Dattawa ya taba neman lalata da ita, kuma za ta gabatar da su a lokaci na gaba.

“Zan gabatar da shaidar da nake da ita a lokacin da ya dace da kuma a wurin da ya dace,”

- Sanata Natasha

Lamarin ya samo asali ne bayan rikicin da ta samu da Akpabio kan batun zaman kujera a majalisa, abin da ya kai ga dakatar da ita daga majalisa na tsawon watanni shida.

Sanata Natasha ta yaba wa hukumar INEC

Sanata Natasha ta ce ko da yake hukuncin da INEC ta yanke ya ɗan makara, amma ta yaba da yadda hukumar ta fahimci cewa korafin yi mata kiranye bai cika sharuda ba.

Kara karanta wannan

Abin da Sanata Natasha ta ce da INEC ta yanke hukunci kan bukatar kwace kujerarta

Sanatar ta ce:

“Ina da masaniya a kan dokokin Najeriya, kuma na san cewa wannan yunkurin mani kiranye ba zai yi nasara ba,”

Ta kuma bayyana cewa yawancin adiresoshin da aka bayar a cikin takardar koken ƙarya ne, saboda yawancin gidaje a yankinta ba su da lamba.

“Ko da yake INEC ta ce an tara sa hannun mutane 208,000, amma da an shiga matakin tantancewa, ba za a samu mutum 500 da za su tabbatar da cewa sun saka hannu ba,”

- Sanata Natasha

A ranar Alhamis, INEC ta sanar da cewa koken da aka gabatar na neman yin kiranye wa Sanata Natasha bai cika sharuddan sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ba.

Yakubu
INEC ta yi watsi da batun yi wa Sanata Natasha kiranye. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Facebook

Gwamnan Kogi ta musa shirin kashe Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio ya musa zargin cewa yana da hannu a shirin kashe Sanata Natasha Akpoti.

Kara karanta wannan

Kurunƙus: Hukumar INEC ta gama nazarin bukatar tsige Sanata Natasha, ta yi hukunci

Haka Zalika gwamnan Jihar Kogi, Akhaji Usman Ododo ya ce babu gaskiya a cikin zargin da Natasha ta yi na cewa suna shirin kashe ta.

Sanata Natasha ta yi zargin cewa ana shirin kashe ta a wani taron Sallah da ta gudanar a mazabarta duk da hana ta da hukuma ta yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng