'Ya Na da Zuhudu': Shaidar da Mutane Suka Yi wa Marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi
- Rasuwar Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ta tayar da hankalin Musulmi a Bauchi da Najeriya baki ɗaya tun daga daren Juma'ar nan
- Fitattun mutane irinsu Sheikh Umar Zaria da Shehu Musa Gabam sun bayyana alhini tare da rokon Allah Ya kyautata makwancinsa
- A hannu daya, an samu ra'ayoyi mabambanta yayin da jama'a ke fadin albarkacin bakinsu a kan rayuwar marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Rasuwar babban malamin addini, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi na ci gaba da girgiza zukatan malamai, dalibai da Musulmi baki daya.
Tun daga daren ranar Alhamis da aka sanar da rasuwar Dutsen Tanshi, kafofin sada zumunta suka cika da sakonni na ta'aziyyar rasuwar malamin.

Asali: Facebook
Allah ya karbi rayuwar Dr. Idris Dutsen Tanshi
Legit Hausa ta ruwaito cewa Sheikh Idris Abdulaziz ya riga mu gidan gaskiya ne da daren Alhamis, 3 ga Afrilu, 2025. Za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 10:00 na safiyar Juma’a.

Kara karanta wannan
"Yana da abin al'ajabi da kura kurai," Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan Dutsen Tanshi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Umar Shehu Zaria, ne ya tabbatar da labarin rasuwar, ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.
Rahotanni sun nuna cewa kafin rasuwarsa, Dr. Dutsen Tanshi ya shafe lokaci yana fama da jinya, wanda hakan ya sa ya dakatar da karatuttukansa na yau da kullum.
Shaidar da mutane suka yi wa Dutsen Tanshi
Bayan rasuwar babban malamin, Legit Hausa ta tattaro shaidar da mutane suka yi wa marigayi Dr. Idris Dutsen Tanshi da kuma sakonnin ta'aziyyarsu ga iyalan malamin:
Abdullahi A Abdullahi, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
"Gaskiya har ga Allah zan yi kewar Malam Idris a wannan sahar, Malam Idris mutum ne iya mutum.
Malam Idris yana da yanayi mabambanta, wani lokaci ya yi sanyi, wani lokaci ya yi zafi, ba za ka kalubalance sa da munafurci ko kin gaskiya ba, musamman a kan tauhidi.

Kara karanta wannan
Bayan jana'izar Dr Idris, wani limami ya ja sallar Juma'a a masallacin Dutsen Tanshi
"Misali, bisa abin da ya bayyana mana - da wuya ka same shi da son rai - sai dai ka same shi da fahimta cikin kuskure ko wani abu haka.
"Amma dai kam an rasa malamin da ba makwadaici ba, bai da handama, Dr. Idris kudin sa yake nema wurjanjan ba kuma a gwamnati ko wajen wani dan siyasa ya samu jari ba, kudi ne da aka sha wahalan nema da gaske - Abin da malamai da yawa na yanzu ya gagare su.
"Mutuncin Dr. Idris ba abin a yi kokonto a kansa ba ne, kuma ko a idon makiyansa da abokan hamayyarsa, yana da kwarjini.
"Allah ya sani, Malam Idris ya na cikin malamai da suke ban farin ciki a wannan sahar, har a kan wasu abubuwan da nake da sabanin fahimta da shi - yadda yake gabatar da jawabinsa yana ban sha'awa da nishadi ba kadan ba. Allah ya yi masa Rahama."
Aliyu Naziru Officer ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
"Babu wanda zai ji mutuwar Malam kamar wannan alaramman na shi, hakika ya tasirantu da Malam sosai. Allah ya kyautata makwancin shi."
Shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Shehu Musa Gabam, ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa:
"Allah ka jikan Sheik Dr. Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi, ka kyautata makwancin sa, Ubangiji Allah kasa Aljanat-ul-Firdaus ce makomar mu baki daya.
"Hakika mutanen jahar Bauchi , Arewa da kasa baki daya an rasa daya daga manyan malamai na addinin musulunci.
"Ubangiji Allah ya jikansa da Rahama, Ameen.-SMG."
Comr Abba Sani Pantami ya wallafa a shafinsa cewa:
"Murnar mutuwa murnar banza ce, duk wanda ya mutu bai yi sauri ba, mu da muke nan bamu dadewa wallahi sai munzo. Allah ya jikan Dutsen Tanshi da Rahama, idan tamu ta zo Allah yasa mu cika da imani."

Kara karanta wannan
"Mutane sun manta": Tinubu ya faɗi aikin da Sheikh Dutsen Tanshi ya yi wa Najeriya
Aliyu Dahiru Aliyu ya yi martani a shafinsa na Facebook, yana cewa:
"Mun sosu kwarai da irin maganganun da Dutsen Tanshi ya dinga gaya wa Manzon Allah (SAW) da iyayensa a matsayinmu na mutane. Rahama kuwa ta Ubangiji ce, da yake bawa bayinsa. Allah ya jikansa. Amma mun fi son iyayen Manzon Allah (SAW) da rahama fiye da shi."
A zantawar Legit Hausa da Mubarak Mahmud, mazaunin Unguwar Jahun, Bauchi, ya nuna kaduwa da rasuwar Mallam Idris.
Mubarak ya ce:
"Shi fa Dakta Idris sai dai ka ƙi gaskiya, amma malami ne da ke karantarwa bisa gaskiya da rashin tsoro.
"Wallahi da ace wani malami ne ya fuskanci irin abin da Dakta Idris ya fuskanta, da tuni ya daina da'awa. Amma har rasuwarsa, yana nan a kan fadin gaskiya.
"Zahiri mun yi babban rashi a Bauchi. Kuma muna addu'ar Allah ya jikan Mallam, ya sa dalibansa su dora daga inda ya tsaya."
Ita ma Mamah Khadija, daga Unguwar Rail Way, Bauchi, ta ce mutuwar malamin ta girgiza ta sosai.
"Na kwana biyu ban ji mutuwa irin ta wannan ɗan tahalikin ba. Duk azumi za ka ji ana sanya karatunsa a rediyo, muna saurare.
"Ko wannan azumin ma ya yi karatu. Kwatsam muka ji cewar ya rasu. Na shiga damuwa sosai. Malamai sai rasuwa suke yi, karshen duniya kenan."
- Mamah Bauchi.
Abubuwa 7 game da marigayi Dutsen Tanshi
Tun da fari, mun ruwaito cewa, marigayi Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya rayu ne a kan wasu muhimman abubuwa 7 da suka hada da tsayuwa a kan tauhidi.
An ce malamin ya kasance mai riko da Sunnar Annabi Muhammad (SAW), kuma ya kasance a sahun gaba wajen kawo abubuwan da za su inganta rayuwar al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng