Bayan Rasuwarsa, An Ji Abubuwa 7 da Dr Dutsen Tanshi Ya Gina Rayuwasa a kan Su

Bayan Rasuwarsa, An Ji Abubuwa 7 da Dr Dutsen Tanshi Ya Gina Rayuwasa a kan Su

  • Malamin addini Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya rasu a daren Alhamis, 3 ga Afrilu, lamarin da ya girgiza al’umma da dama
  • Dutsen Tanshi Majlis Bauchi, shafin da ke kula da karatuttukan marigayin ya sanar da cewa za a gundanar da jana’izarsa a safiyar Juma'a
  • Legit Hausa ta zakulo muhimman abubuwa 7 da marigayi Idris Abdullaziz Dutsen Tanshi ya gina rayuwarsa a kan su, ciki har da riko da tauhidi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - A daren ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, Allah ya karbi rayuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.

Labarin mutuwarsa, ta girgiza jihar Bauchi, mahaifar malamin da kuma Najeriya da kasashen Afrika baki daya, kasancewarsa shahararre a fannin wa'azi.

An tuno da abubuwan da marigayi Dr. Idris Abdulaziz ya gina rayuwarsa a kan su
Tauhidi da wasu abubuwa 5 da marigayi Dr. Idris Adulaziz Dutsen Tanshi ya gina rayuwarsa a kan su. Hoto: Dutsen Tanshi Majlis Bauchi
Asali: Facebook

Dr. Idris Dutsen Tanshi ya rasu

Shafin Dutsen Tanshi Majlis Bauchi na Facebook ya tabbatar da rasuwar Dr. Idris Abdul'aziz, tare da bayyana cewa za a gudanar da jana'izarsa da karfe 10:00 na safiyar Juma'a.

Kara karanta wannan

Pantami ya yi magana da Allah ya karɓi rayuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce, za a gudanar da jana'izar babban malamin ne a masallacin Idi da ke cikin 'Games Village' Bauchi.
"Sallah janazar babban limamin mu, Imam Dr. Idris Bauchi (Rahimahullah) karfe: 10:00 na safe, a masallacin Idi, Games Village, Bauchi"

- Inji sanarwar masallacin.

A wata sanarwar ta daban, an roki mahalarta wannan jana'iza da su ajiye motocinsu a cikin harabar Games Village, amma a ajiye babura a cikin harabar masallacin Malam Tijjani Guruntum.

Abubuwa 7 da Dutsen Tanshi ya ginu a kan su

Bayan rasuwar wannan fitaccen malami, Legit Hausa ta zakulo wasu muhimman abubuwa 7 da marigayi Dr. Idris Dutsen Tanshi ya gina rayuwarsa a kansu.

Kamar yadda aka wallafa a shafin Dutsen Tanshi Majlis Bauchi, marigayi Dr. Idris Abdul'aziz ya gina rayuwarsa ne a kan:

1. Tsantsar riko da Tauhidi.

2. Riko da koyarwar Annabi (Sunnah.)

3. Fallasawa da kuma tsage gaskiya a kowane lokaci.

Kara karanta wannan

Wasiyoyi 5 da marigayi Dr Idris Dutsen Tanshi ya bari kafin mutuwarsa

4. Nazari, hangen nesa, da tsara yadda rayuwar al'umma za ta ci gaba.

5. Hakuri, juriya, dogewa da riko da kaddara a lokutan jarabawa da tsananin rayuwa.

6. Damuwa kwarai a kan duk wani abu da ke barazana ga rayuwar al'umma.

7. Tsayawa tsayin daka ba tare da jin tsoron hare-hare ko cin zarafin Mushrikai da 'yan bidi'a ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.