Pantami Ya Yi Magana da Allah Ya Karɓi Ran Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Pantami Ya Yi Magana da Allah Ya Karɓi Ran Sheikh Idris Dutsen Tanshi

  • Sheikh Isa Ali Pantami ya miƙa sakon ta'aziyya bisa rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci da ke zaune a Bauchi, Dr. Idris Abdul'Aziz Dutsen Tanshi
  • Sheikh Idris ya rasu ne a daren Juma'a, 6 ga watan Shawwal, 1446AH a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya bayan fama da jinya
  • Jim kaɗan bayan samun labarin, Pantami, tsohon ministan sadarwa ya yi ta'aziyya ga iyalan marigayin da ƴan uwansa, ya roƙi Allah Ya sa shi a Aljanna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali ibrahim Pantami ya yi alhinin rasuwar babban malamin musulunci, Dr. Idris Abdul'Aziz Dutsen-Tanshi.

Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar fitaccen malamin tare da addu'ar Allah ya jiƙansa kuma ya gafarta masa kura-kuransa.

Sheikh Pantami da Marigayi Dr. Idris.
Sheikh Isa Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar Dr. Idris Dutsen-Tanshi Hoto: Prof. Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Malam Pantami, wanda shi ma babban malamin Sunnah ne a Najeriya, ya miƙa sakon ta'aziyya ne a wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Idris Abdul'Aziz Dutsen Tanshi ya rasu

Rahotannin Legit Hausa ta samu sun tabbatar da cewa Allah ya karbi rayuwar Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi bayan ya sha fama da jinya.

Bayanai sun nun cewa Dr. Idris Abdul'aziz ya riga mu gidan gaskiya ne a daren jiya Alhamis, wanda shi ne daren Juma'a a addinin Musulunci.

Wasu rahotanni sun nuna cewa marigayin ya shafe tsawon lokaci yana fama da jinya kafin rasuwarsa duk da dai ba a bayyana ciwon da yake fama da shi ba.

Wannan dalili ne ya sa bisa tilas ya dakatar da karatuttukansa da kuma huduba a masallacin Juma'a da ya saba yi a garin Dutsen-Tanshi inda ya wakilta dalibansa.

Sheikh Pantami ya yi ta'aziyyar rasa Dutsen Tanshi

Bayan labarin rasuwar ya bazu, Sheikh Isa Pantami, ɗaya daga cikin manyan maluman Sunnah a Najeriya ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansa da ƴan uwa.

Pantami ya yi wa marigayin addu'ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya shi a Aljannah, sannan ya roki Allah Ya kyautata karshen kowa.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Idris Dutsen Tanshi ya fada kan rashin lafiya da mutuwa kafin ya Cika

Sheikh Pantami.
Sheikh Pantami ya yi ta'aziyyar rasuwar Dr. Idris Dutsen Tanshi Hoto: Prof Isa Ali Pantami
Asali: UGC
"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji'un! Muna mika ta'aziyyar rasuwar Dr Idris AbdulAzeez zuwa ga iyalansa da yan'uwansa. Allah Ya yafe masa kura-kurensa, Ya sa Aljannah ce makoma. Allah Ya kyautata namu bayan na su."

- In ji Isa Pantami.

Har ila yau, Pantami ya tunatar da cewa duk abin da Allah Ya dauka, da wanda Ya bayar, na sa ne kuma yana da lokacin da aka tsara masa a duniya.

Ya nuna cewa hakuri da juriya su ne mafi alkhairi a irin wannan lokaci.

Wasiyoyin marigayi Dutsen Tanshi

A wani labarin, mun kawo maku jerin wasiyyoyi biyar da Sheiƙh Idris Dutsen Tanshi ya yi kafin Allah ya karɓi rayuwarsa.

Daga cikin wasiyyoyin malamin, ya hana ɗaukar hotuna a lokacin jana'izarsa kuma ya hana yi masa zaman makoki bayan rasuwarsa.

Ana sa ran za a yi masa jan'iza yau Juma'a, 4 ga watan Afrilu, 2025 da misalin karfe 10:00 na safiya a Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262