Galadima: Aminu Ado na Karbar Ta’aziyya a Fadarsa, Sarakuna, ’Yan Siyasa na Tururuwa
- Aminu Ado Bayero na ci gaba da karbar ta’aziyya bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi Bayero
- Basaraken ya karbi wakilan Sarkin Hadejia, Dr. Adamu Abubakar Maje, da sauran manyan baki a fadarsa
- Alhaji Tanko Yakasai, daya daga cikin dattawan Kano, ya kai ta’aziyya ga Sarkin Kano a yau Alhamis
- Wadannan ziyara an yi su ne domin jajanta wa Sarkin Kano kan babban rashi da aka yi a Kano da Arewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na ci gaba da karbar ta'aziyya bayan rasuwar Galadiman Kano.
Basaraken ya karbi bakuncin sarakuna da manyan dattawa da 'yan siyasa daban-daban a yau Alhamis 3 ga watan Afrilun 2025.

Asali: Facebook
Galadiman Kano: Aminu Ado ya soke bukukuwan sallah
Wannan na daga cikin wata sanarwa da shafin Masarautar Kano ta wallafa a manhajar X a yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan matakin Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero na soke duk wasu shirye-shiryen bukukuwan sallah da aka tsara sakamakon rasuwar Galadiman Kano.
Sanarwar da fadarsa ta fitar ta bayyana cewa bukukuwan sallah da za a yi a gidan Nasarawa an soke su saboda wannan babban rashin da aka yi.
Yayin sanarwar, Sarkin Kano ya bayyana alhini, yana cewa Galadiman Kano dattijo ne mai jajircewa da ya ba da gudunmawa ga Kano da Najeriya.
Sarki Aminu Ado Bayero ya yi addu’a Allah ya gafarta wa mamacin, ya sa ya huta, tare da yi wa iyalansa da al’ummar Kano fatan hakuri da juriya.
Sarkin Hadejia ya ziyarci Aminu Ado Bayero
A cikin sanarwar, an gano wakilan Sarkin Hadejia, Dr. Alhaji Adamu Abubakar Maje domin yi masa ta'aziyya kan babban rashin da aka yi.
Sanarwar ta ce:
"Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayaro CFR CNOL JP ya na ci gaba da karbar ta’aziya, Mai Martaba Sarki ya karbi wakilan Mai Martaba Sarkin Hadejia Dr. Alh. Adamu Abubakar Maje CON bisa Wakilcin Galadiman Hadejia.
"Allah ya ba da lada."

Asali: Twitter
Aminu Ado na karbar gaisuwar Galadiman Kano
Har ila yau, Aminu Ado Bayero ya karbi bakuncin daya daga cikin dattawan Arewacin Najeriya kuma tsohon dan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai.
A cewar sanarwar:
"Daga Fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayaro CFR CNOL JP ya na ci gaba da karbar ta'aziyyar marigayi Mai Girma Galadiman Kano, Alh. Abbas Sanusi Bayero.
"Daya daga cikin dattawan Kano, Dattijo Alh. Tanko Yakasai ya kai ziyarar ta'aziyya fadar a yau Alhamis 3 ga watan Afrilun 2025."
Dukan wadannan ziyara an yi su ne a yau Alhamis 3 ga watan Afrilun 2025 domin jajantawa basaraken kan rashin Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.
Tinubu ya yi ta'aziyyar Galadiman Kano
Kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aziyyarsa bisa rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.
Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin da dattijo, wanda ya ba da gagarumar gudummawa a masarautar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Marigayin, wanda ya rasu yana da shekaru 92 a duniya, shi ne mahaifin shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng