Muhimman Abubuwan da Suka Faru Tun bayan Kisan 'Yan Arewa a Edo
- Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci a nunawa duniya mutanen da aka kama kan kisan ƴan Arewa a Edo
- Takwaransa na jihar Edo, Monday Okpebholo, ya tabbatar da miƙa mutane 14 da aka kama zuwa Abuja don ci gaba bincike
- An nemi ba iyalan mamatan diyya sannan Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan, ya umarci a gudanar da bincike cikin gaggawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci a nunawa duniya waɗanda aka kama kan zargin kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo.
Har ila yau, ya jaddada buƙatar biyan cikakkiyar diyya ga iyalan mamatan domin tabbatar da adalci kan wannan mummunan lamari.

Asali: Twitter
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin, 31 ga Maris, 2025, kamar yadda mai magana da yawun bakinsa ya bayyana a shafin Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba Kabir Yusuf ya yi kalaman ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar jihar Edo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Monday Okpebholo, wanda ya kai ziyarar ta’aziyya Kano.
Abubuwan da suka faru bayan kisan ƴan Arewa a Edo
Kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewan dai, ya jawo mutane da dama sun yi tofin Allah tsine saboda irin zaluncin da aka yi musu.
Bayan aukuwar lamarin, abubuwa da dama sun auku, kuma hukumomi sun ɗauki matakai.
Ga kaɗan daga cikin muhimman abubuwan da suka faru:
1. Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da kisan
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah wadai da kisan, inda ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike cikin gaggawa.
A cikin wata sanarwa, ya bayyana kisan a matsayin ta’addanci da rashin imani, tare da jaddada cewa dole ne a hukunta waɗanda suka aikata hakan.
Ya ba da umarnin cewa hukumomin tsaro su ɗauki matakin da ya dace don kamo waɗanda suka aikata laifin.
2. Gwamnan Edo ya dakatar da shugaban rundunar tsaro
Bayan faruwar mummunan lamarin, gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya gaggauta dakatar da dukkan ƙungiyoyin sa-kai marasa rijista da ke aiki a faɗin jihar.
Haka zalika, ya dakatar da kwamandan rundunar tsaron jihar Edo, Friday Ibadin, sakamakon rawar da ƴan sa-kai suka taka a kisan.
Mai magana da yawun gwamnan ya bayyana cewa ƙungiyar ƴan sa-kan da ta jagoranci kisan, ba ta da rajista a ƙarƙashin dokokin tsaron jihar Edo, kuma ayyukansu sun sabawa manufofin gwamnati.
3. Kama mutane 14 da ci gaba da bincike
Sufeto-Janar na ƴan Sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya tabbatar da kama mutane 14 da ake zargi da hannu a mumminan kisan
Ya kuma tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin da abin ya faru domin tabbatar da doka da oda, tare da alƙawarin cewa za a ci gaba da kama sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.
Sufeto-Janar na ƴan sandan ya naɗa DIG Sadiq Abubakar, don jagorantar binciken tare da tabbatar da cewa za a gudanar da shi cikin adalci da sauri.

Asali: Twitter
4. Gwamna Okpebholo ya kai ziyarar ta’aziyya Kano
A jawabinsa yayin ziyarar ta’aziyya, Gwamna Okpebholo ya bayyana kisan a matsayin abin takaici tare da tabbatarwa iyalan mamatan cewa za a yi adalci.
Ya ƙara da cewa matakin farko shi ne tabbatar da an ɗauki gawarwakin mamatan domin a yi musu jana’iza yadda ya kamata.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta biya diyya ga iyalan mutanen da suka rayukansu.
5. DSS ta cafke manyan waɗanda ake zargi
Tashar Channels tv ta rahoto cewa jami'an hukumar DSS sun cafke manyan waɗanda ake zargi da hannu a kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a Uromi.
Jami'an na DSS sun samu nasarar cafke mutanen ne guda biyu bayan sun samu bayanan sirri a kansu.

Kara karanta wannan
Gwamnan Edo ya gana da Barau kan kisan Hausawa, ya fadi shirinsa kan iyalan mamatan
DHQ ta yi magana kan kisan ƴan Arewa a Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), ta bayyana cewa an warware matsalar batun kisan ƴan Arewa a jihar Edo.
Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa shugabannin jihohin Edo da Kano ne suka zauna suka shawo kan matsalar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng