Kisan 'Yan Arewa a Edo: Rundunar Sojoji Ta Bayyana Yadda Aka Warware Matsalar
- Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi ƙarin haske kan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo da ke Kudancin Najeriya
- DHQ ta bayyana cewa shugabannin jihohin Edo da Kano sun shawo kan matsalar ta hanyar zaman da suka yi a tsakaninsu
- Hedkwatar tsaron ta kuma bayyana cewa dakarun sojoji ba su gaza ba a ƙoƙarin da suke yi na fatattakar ƴan ta'adda da ƴan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana inda aka kwana kan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo.
DHQ ta bayyana cewa shugabannin jihar Edo da Kano, waɗanda kisan gillar da aka yi a Uromi ya shafi mutanen jihohinsu, sun warware matsalar.

Asali: Twitter
Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su waye suka warware matsalar kisan ƴan Arewa?
Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana cewa shugabannin jihohin biyu sun zauna domin shawo kan matsalar.
"Shugabannin jihar Edo da Kano sun ɗauki matakin da ya dace kan lamarin. Kusan kowa ya san cewa shugabannin Edo sun kai ziyara Kano kan batun da kuma don jajantawa iyalan waɗanda abin ya shafa."
"Saboda haka, a matakin siyasa, an warware komai. Ba na tsammanin za a samu wata matsala. Idan wani ko wata ƙungiya na haifar da tashin hankali ko barazana, hukumomin tsaro za su gudanar da bincike idan suka gano." za a gudanar da bincike."
- Manjo Janar Markus Kangye
DHQ za ta ci gaba da fatattakar miyagu
Hakazalika, DHQ ta ce hare-haren makiyaya da kashe-kashen da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da Abuja, Enugu, Benue, Ondo, Zamfara, da Cross River, ba alama ba ce cewa rundunar sojoji ta gaza kan sauke nauyin da ke kanta.
Manjo Janar Kangye yana mayar da martani ne kan tambayoyi da suka shafi yadda makiyaya ke kai hare-hare suna kashe ƴan Najeriya ba tare da sojoji sun ɗauki wani mataki ba, rahoton The Punch ya tabbatar.
"A maimakon haka, DHQ ta jaddada cewa dakarunta suna ci gaba da yaƙi da makiyaya masu tada hargitsi da ƴan ta’adda, inda suke kawar da su da shugabanninsu a cikin hare-haren da ake ci gaba da kai wa."
"Rundunar sojoji ba ta yi watsi da yaƙi da makiyaya masu tada rikici ba, ƴan ta’adda, da ƴan bindiga ba. Mun kawar da da dama daga cikinsu kuma muna ci gaba da ragargazarsu da shugabanninsu har sai mun kawar da barazanarsu gaba ɗaya."
- Manjo Janar Markus Kangye
Hakazalika, Manjo Janar Kangye ya ce jita-jitar da ke yawo cewa Jamhuriyar Nijar ta janye daga rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) har yanzu ba gaskiya ba ne.
DSS sun cafke masu hannu a kisan ƴan Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar tsaro ta DSS sun samu nasarar cafke wasu daga cikin manyan waɗanda ake zargi da hannu a kisan ƴan Arewa a jihar Edo.
Jami'an na hukumar DSS sun yi nasarar cafke mutanen ne bayan sun samu muhimman bayanan sirri a kan motsinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng