"Na Ɗauki Laifin," Gwamna Ya Nemi Afuwar Ƴan Najeriya kan Abin da Ya Faru a Gadar Sama
- Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya kai ziyara wurin aikin gadar Independence, wanda ya haddasa cunkoso mai tsakani
- Gwamnan ya bai wa mazauna Legas da sauran ƴan Najeriya haƙuri bisa wahalar da suka sha a matsanancin cunkoso bayan fara aikin
- Ya bukaci duk wanda ke da uzurin da zai sa ya bi ta gadar ya yi amfani da fasahar zamani kamar Zoom wajen biyan buƙatunsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya nemi afuwa daga ‘yan Legas da suka fuskanci matsanancin cinkoso sakamakon aikin gyaran gadar Independence da ke Legas.
Rufe gadar don gyare-gyare ya jefa dubban mazauna yankin cikin matsala daga yammacin Laraba zuwa safiyar Alhamis.

Asali: Twitter
A wata sanarwa da ya wallafa a X da safiyar Alhamis, Gwamna Sanwo-Olu ya ziyarci wurin domin duba aikin da kuma gane wa idonsa cunkoson da mutane ke fuskanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hotuna da bidiyon fasinjojin da suka makale a wurin sun karade kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka yi Allah-wadai da lamarin.
Gwamnan Legas ya ba da haƙuri
Yayin da yake magana da manema labarai, Gwamna Sanwo-Olu ya nemi afuwar ƴan Najeriya a ciki da wajen Legas, yana mai cewa ba a yi wa mazauna yankin cikakken bayani kafin fara aikin ba
"Na farko, ina mai neman afuwa daga dukkan mazauna Legas da suka fuskanci wannan matsanancin cinkoso da ya haddasa wahala cikin awanni 24 da suka gabata, ku yi haƙuri," in ji shi.
Ya ce ya dauki nauyin abin da ya faru a madadin gwamnati, a matakin jiha da na tarayya, yana mai cewa duk da wahalar da mutane suka fuskanta, aikin yana da muhimmanci domin kaucewa hadari mai girma.
Me yasa za a yi gyaran gadar?
"Wannan aikin yana da mahimmanci domin hana wata babbar matsala da ka iya faruwa nan gaba.

Kara karanta wannan
A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas
"Mun san babu wani lokaci da za a iya cewa shi ne mafi dacewa da yin irin wadannan ayyuka."
- In ji Gwamna Sanwo-Olu.
Gwamnan ya kara da cewa kwangilar aikin an kulla ta tun sama da shekaru uku da suka wuce, kuma gwamnati tana kokari don tabbatar da lafiyar gadar.
Gwamna Sanwo-Olu ya ba matafiya shawara
Sanwo-Olu ya bukaci ƴan Legas su yi shiri daidai da halin da ake ciki, yana mai shawartar wadanda ba su da mahimman ayyuka a Victoria Island su guji tafiya can har na tsawon makonni biyu zuwa uku.
"Idan ba lallai dole sai kun je Victoria Island a wannan lokaci ba, ina ba ku shawara ku yi amfani da kafafen sadarwa kamar wayar salula, zoom da sauransu don gudanar da ayyukanku," in ji shi.
Gwamnatin Legas ta haramta duka a makaranta
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sake jaddada haramcin dukan ɗalibai a makarantun da ke ƙarƙashin gwamnatin Legas.
Ya jaddada cewa har zuwa yau dokar haramta dukan dalibai saboda rashin ɗa’a da wasu laifuka don gudun samun raunuka, suma ko ma mutuwa tana nan daram.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng