An Bar Kasa ba Kowa: Shettima Ya Shilla Kasar Waje bayan Tinubu Ya Kwana a Faransa
- Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin Dakar a Senegal, domin wakiltar Bola Tinubu a bikin cika shekaru 65 da 'yancin kai
- A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Sanata Shettima ya tabbatar da halartarsa a bikin da ake gudanarwa kowace 4 ga watan Afrilu tun 1960
- Shugaba Bassirou Diomaye Faye ne ya gayyaci shugaban kasar, wanda ke nuna kyakkyawar alaƙa tsakanin Najeriya da Senegal a fannin diflomasiyya
- Manyan taruka za su gudana a 'Place de la Nation', Dakar, inda Shugaba Faye zai karɓi Shettima da sauran manyan baƙi daga Afrika da sauran sassan duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa birnin Dakar da ke kasar Senegal.
Shettima ya kai ziyarar don wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin cika shekaru 65 da samun 'yancin kai na ƙasar.

Kara karanta wannan
Abin da Buhari ya ce bayan rasuwar dattijo, Galadiman Kano, ya fadi giɓin da ya bari

Asali: Twitter
Tinubu ya wuce Paris da ke kasar Faransa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shettima ya wallafa a shafinsa na X a yau Alhamis 3 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya tafi Paris, don wata gajeriyar ziyarar aiki, inda zai duba nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun daga 2023 zuwa 2025.
Haka nan zai yi amfani da wannan lokaci wajen tantance manufofinsa kuma tsara wasu dabarun ayyuka gabanin cika shekaru biyu a mulki.
Fadar shugaban kasa ta ce duk da yana kasar waje, Tinubu zai ci gaba da kula da harkokin gwamnati, sannan zai dawo gida cikin makwanni biyu.

Asali: Twitter
Ƴan Najeriya sun dura kan Bola Tinubu
Ƴan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan tafiyar da shugaban ƙasan ya yi zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa.
Wasu daga ciki sun yi masa fatan alheri kan tafiyarsa cikin nasara yayin da wasu suka caccake shi kan yawan tafiye-tafiyen da yake yi.
Musabbabin zuwan Kashim Shettima kasar Senegal
Hakan ya biyo bayan bikin ranar 'yancin kai a kowace 4 ga Afrilu tun daga shekarar 1960, tare da bukukuwa na ƙasa, jerin gwano, da tarukan al'adu da Senegal ke yi.
Halartar Shettima ya biyo bayan gayyatar da Shugaba Bassirou Diomaye Faye na Senegal ya aika, wanda ke nuna kyakkyawar alaƙa tsakanin Najeriya da Senegal.
Manyan tarukan za su gudana a 'Place de la Nation' da ke Dakar, inda Shugaba Faye zai karɓi Shettima da sauran manyan baƙi daga Afrika da sauran sassan duniya.
An gargadi Tinubu kan tafiye-tafiye
A baya, kun ji cewa jigon PDP, Bode George ya soki Bola Tinubu bisa tafiyarsa Faransa a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar tsaro.

Kara karanta wannan
Ana jimamin kisan 'yan Arewa, Tinubu zai shilla zuwa kasar waje, zai shafe mako 2
Kusa a PDP ya ce gwamnati na aiwatar da manufofi masu barazana ga hadin kan kasa, tana maimaita kura-kuran baya.
George ya kuma zargi jam'iyyar APC da Majalisar Dattawa da kokarin kawo cikas wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan bayan zarge-zargenta kan Godswill Akpabio.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng