Rama Azumin Ramadan da Sauran Hukunce Hukuncen Sittu Shawwal a Musulunci
- Malamin addinin Musulunci, Dr Jamilu Yusuf Zarewa ya yi bayani filla kan hukunce hukuncen da suka shafi azumin sittu Shawwal
- Dr Jamilu Yusuf Zarewa ya ce Annabi (SAW) ya tabbatar da azumin sittu Shawwal a ingantanccen hadisi, kuma yana da lada mai dimbin yawa
- Malamin ya yi bayani kan hukuncin niyya da yin azumin a jere tare da karin haske kan hukuncin fara azumin kafin rama na Ramadan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Malami a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Dr Jamilu Yusuf Zarewa ya yi bayani game da hukunce-hukuncen azumin sittu Shawwal.
Ya ce Annabi Muhammad SAW ya tabbatar da azumin sittu Shawwal a cikin wani hadisi, kuma wanda ya yi azumin bayan ya kammala Ramadan zai samu ladan azumin shekara guda.

Asali: Facebook
Sheikh Dr Zarewa ya yi bayanin ne a cikin wata hira da ya yi da BBC Hausa kamar yadda shafin Darul Fikr ya wallafa hirar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya kara da cewa azumin sittu Shawwal yana cike gibin da mutum ya samu yayin azumin watan Ramadan, kamar yadda aka fahimta daga hadisin Annabi (SAW).
Lokacin fara azumin sittu Shawwal
A cewar Dr Jamilu Zarewa, ana iya fara azumin sittu Shawwal daga rana ta biyu bayan sallar Idin azumi.
Malamin ya bayyana cewa ba dole ba ne a yi azumin sittu Shawwal a jere; mutum na iya rarraba shi yadda yake so.
Haka kuma, ya fi dacewa mutum ya kulla niyyar yin azumin tun da dare, amma idan ya tashi da safe bai ci abinci ba sannan ya yi niyya, hakan ma zai wadatar.
Rama Ramadan ko fara sittu Shawwal?
Sheikh Zarewa ya yi bayani cewa ya fi dacewa mutum ya rama azumin da ya kubuce masa a Ramadan kafin ya fara sittu Shawwal.
A cewar malamin:
"Matar da ta yi jinin haila a Ramadan, za ta fara ramawa ne kafin ta yi azumin sittu Shawwal. Haka ma wanda ya yi rashin lafiya."
Malamin ya kara da cewa duk da cewa wasu malamai suna ganin za a iya fara sittu Shawwal kafin a rama Ramadan, babu wata hujja mai karfi da ke tabbatar da hakan.
Matsayin azumin sittu Shawwal
Dr Zarewa ya bayyana cewa azumin sittu Shawwal sunnah ne, kuma wasu malamai sun ce sunnah ce mai karfi.
Sai dai duk da haka malamin ya ce idan mutum bai yi azumin ba, ba shi da wani laifi a shari’ar Musulunci.
Ingancin Hadisin sittu Shawwal
Akwai malamai da suka ce hadisin da ya tabbatar da azumin sittu Shawwal bai inganta ba, amma Sheikh Zarewa ya ce hadisin ingantacce ne kuma Imam Muslim ne ya ruwaito shi.
Malamin ya yi bayani cewa Imam Malik ya hana azumin sittu Shawwal ne domin kada jahilai su hada shi da azumin Ramadan.

Asali: Facebook
Sai dai, malamai a mazhabar Malikiyya sun yi karin haske da cewa yin azumin sunnah ne. Haka kuma, sauran mazhabobi da malamai sun bayyana cewa azumin sittu Shawwal sunnah ne.
An yi wa dan agajin Izala kisan gilla
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izala ta sanar da kisan gillar da aka yi wa wani dan agajinta a Abuja.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci a yi bincike domin gano 'yan ta'addan da suka bi dan agajin har gida suka masa kisan gilla.
Asali: Legit.ng