Ana cikin Bikin Sallah, 'Yan Bindiga Sun Tafka Ta'asa kan Jami'an Tsaro a Katsina

Ana cikin Bikin Sallah, 'Yan Bindiga Sun Tafka Ta'asa kan Jami'an Tsaro a Katsina

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke bindigogi sun kai harin ta'addanci a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Ƴan bindigan sun kai harin ne a wasu ƙauyuka guda biyu na ƙaramar hukumar Safana wacce ke fama da matsalar rashin tsaro
  • Tsagerun a yayin harin sun hallaka wani kwamandan ƴan sa-kai da ke jagorantar tawagar tsaro a yankin
  • Harin da ƴan bindigan suka kai kuma, ya jawo sanadiyyar raunata wasu mutum uku bayan sun buɗe wuta kan mai uwa da wabi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyukan Bajat da Dole da ke cikin ƙaramar hukumar Safana ta jihar Katsina.

Harin na ƴan bindigan ya yi sanadiyyar mutuwar kwamandan ƴan sa-kai guda ɗaya tare da jikkata wasu da dama a ranar 1 ga watan Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun gwabza fada da 'yan Boko Haram, an samu asarar rayuka

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun kashe kwamandan 'yan sa-kai a Katsina Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Katsina

Harin na ƴan bindigan ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali, yayin da mutane suka ruga cikin daji don tsira da rayukansu.

Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan bindigan sun afka yankin da misalin karfe 6:00 na yamma, ɗauke da muggan makamai, inda suka fara harbi ba kakkautawa.

Miyagun sun kutsa cikin gidaje, suna harbi da kuma lalata dukiya. A yayin farmakin, an kashe kwamandan ƴan sa-kai, Nura Baushe, wanda ke jagorantar tawagar tsaro a yankin.

Sauran waɗanda suka jikkata sun hada da Amadu Dole, Surajo Shehu, da Shafiu Sulaiman.

An garzaya da su zuwa asibitin koyarwa na tarayya da ke Katsina domin samun kulawar likitoci sakamakon raunukan da suka samu.

Waɗanda suka tsira da ransu sun bayyana cewa ƴan bindigan sun harbi waɗannan mutanen ne a ƙoƙarinsu na kare kansu da iyalansu.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan bindiga, sun samu gagarumar nasara

Bayan harin, hukumomin tsaro sun ɗauki matakin gaggawa ta hanyar tura jami’an tsaro zuwa yankin domin daƙile ci gaba da kai hare-hare.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun kashe kwamanda na 'yan sa-kai a Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

An tsaurara matakan tsaro a Katsina

Hakan ya taimaka wajen dawo da zaman lafiya, inda aka jibge jami’an tsaro domin hana sake faruwar irin wannan hari.

Al’ummar yankin sun buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakan kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Sun nuna cewa hare-haren ƴan bindiga na barazana ga rayuwarsu da dukiyoyinsu.

Akwai buƙatar ƙara tsaurara tsaro

Abubakar Mika ya shaidawa Legit Hausa cewa akwai buƙatar jami'an tsaro su ƙara ɗaukar matakai domin kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga.

"Ya kamata jami'an tsaro su ƙara azama duk da cewa suna ƙoƙari wajen kawo ƙarshen hare-haren ƴan bindiga."
"Rayukan mutane da dama sun salwanta sakamakon hare-haren miyagu, lokaci ya yi da ya kamata a kawo ƙarshen matsalar.

- Abubakar Mika

Ƴan bindiga sun saki Birgediya Janar Tsiga

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kwanton bauna, sun hallaka 'yan kasar waje da dan sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa Birgediya Janar Maharazu Tsiga da ƴan bindiga suka sace a jihar Katsina, ya shaƙi iskar ƴanci.

Ƴan bindigan dai sun sace tsohon shugaban na hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) ne a gidansa da ke garin Tsiga a ƙaramar hukumar Bakori.

Birgediya Janar Maharazu Tsiga ya shafe kusan watanni biyu a tsare a hannun ƴan bindiga tun bayan da suka yi garkuwa da shi.

Duk da biyan kuɗin fansa da iyalansa suka yi, ƴan bindiga sun ci gaba da tsare Maharazu Tsiga har na tsawon lokaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng