An Kutsa Gidan Dan Agajin Izala a Abuja, An Sassara Shi da Makami har Lahira
- Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ‘yan ta'adda sun kashe Malam Khalid Adamu a gidansa da ke Abuja
- Kungiyar Izala ta sanar da cewa Malam Khalid Adamu shi ne Sakataren Kudi na Majalisar Agaji ta yankin Lugbe
- Shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci hukumomi su kamo masu laifin tare da gurfanar da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wasu ‘yan ta'adda sun kai hari a cikin gidan Sakataren Kudi na Majalisar Agaji ta Lugbe, Malam Khalid Adamu da ke babban birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun kashe Khalid Adamu ta hanyar sara da suka da suka yi masa.

Asali: Facebook
A wani sako da kungiyar Izala ta wallafa a shafinta na Facebook, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi Allah wadai da kisan da aka yi wa Khalid Adamu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kisan ya jefa damuwa a zukatan al’umma, musamman 'yan agaji da ke fadin kasar nan, inda mutane da dama suka bayyana alhininsu tare da yin addu’a ga marigayin.
Bayanin Sheikh Abdullahi Bala Lau
Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya jajanta wa iyalan mamacin da ‘yan uwansa, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su gudanar da bincike mai zurfi domin gano wadanda suka kashe shi.
Shugaban kungiyar Izalan ya bayyana cewa wannan hari ya jawo babban rashi ga aikin agaji da al’umma gaba daya.
Sheikh Bala Lau ya ce:
"Muna kira ga jami’an tsaro da su binciko wadanda suka aikata wannan ta’addanci domin gurfanar da su a gaban kuliya."
Shehin malamin ya kuma roki Allah ya gafarta wa marigayin, tare da jaddada bukatar daukar matakin gaggawa domin hana sake afkuwar irin wannan ta’asa a nan gaba.

Asali: Facebook
Al’umma sun yi addu’o’i ga dan agajin

Kara karanta wannan
'Yadda watsi da shirin Sardauna ke jawo asarar rayukan Hausawa,' Yan kasuwa kan kisan Edo
Bayan samun labarin kisan gillar, mutane da dama sun nuna jimaminsu tare da yin addu’o’i ga Malam Khalid Adamu.
Zainab Ja’afar Mahmud ta ce:
"Allah ya mi shi rahma, ya sa ya huta, ya saka masa da aljanna."
Ismail Abdullahi Usman ya yi addu’a da cewa:
"Allah ya jikansa, ya yi masa rahma. Muma idan tamu tazo, Allah ya sa mu yi kyakkyawan karshe."
Abubakar Mohammed ya bayyana cewa:
"Allah ya ji kan shi da rahma. Su kuma wadanda suka aikata wannan aika-aika, su ne abin tausayi."
Shi kuwa Sunusi Abubakar ya yi fatan:
"Allah ya gafarta masa, ya sa Aljanna ce makomarsa. Su kuma wadanda suka aikata wannan ta’asa, Allah ya tona asirinsu.
Mutane da dama na kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin da ya dace domin tabbatar da ganin cewa irin wannan aika-aika ba ta ci gaba da faruwa ba.
Malamin Kabiru Gombe ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa Sakataren kungiyar Izala na kasa, Sheikh Muhammadu Kabir Haruna Gombe ya rasa wani daga cikin malamansa.
Sheikh Kabir Haruna Gombe ya ce wani malaminsa mai suna Ibrahim Bawa Gwani ya rasu a jihar Gombe yana dan shekaru 70 a duniya.
Asali: Legit.ng