'Ka Gaggauta Daukar Mataki': An Fadawa Tinubu Abubuwa 2 da Ke Barazana ga Najeriya

'Ka Gaggauta Daukar Mataki': An Fadawa Tinubu Abubuwa 2 da Ke Barazana ga Najeriya

  • Chief Bode George ya ce rikicin siyasa a Ribas da yunkurin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye na iya barazana ga Najeriya
  • Ya soki yadda majalisa ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas ba tare da rinjayen kashi biyu bisa uku ba, inda ya ce hakan ya saba doka
  • Tsohon mataimakin shugaban PDP ya yi tir da yadda INEC ta sauya matsayi kan batun yi wa Natasha kiranye, abin da ya kira da rashin adalci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP, Chief Bode George, ya fadawa Shugaba Bola Tinubu abubuwa biyu da ke barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya.

Chief Bode George ya yi gargadin cewa rikicin da ke faruwa a Ribas da ya kai ga dakatar da gwamnan jihar na gaba-gaba wajen iya lalata dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

'Ka sani mulki zai kare,' An yi wa Tinubu nasiha mai zafi kan tafiya Faransa

Jigon PDP, Bode George ya gargadi Tinubu kan rikicin River da Natasha
Bode George ya ce Rikicin Rivers da na Natasha za su iya zama matsala ga dimokuradiyyar Najeriya. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Facebook

Jigon PDP ya gargadi Tinubu kan Rivers, Natasha

Jigon na PDP ya kuma ce watsi da zargin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi kan Sanata Godswill Akpabio, na iya zama barazana ga Najeriya, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Chief George ya ce tarihin siyasar Najeriya ya nuna cewa irin wadannan rikice-rikice ne suka haddasa rugujewar Jamhuriyya ta Farko da ta Biyu.

A cewar dattijon, tsarin mulkin shugaban kasa da ake amfani da shi yanzu yana ƙara zama mafi muni fiye da na mulkin soja da aka gani a baya.

A wani saƙo da ya fitar, ya soki amincewar da majalisar tarayya ta yi da dokar ta ɓaci da Tinubu ya sanya a Ribas ta hanyar kada kuri'ar baki, yana mai cewa hakan ya saba ƙa’ida.

An soki Tinubu, majalisa kan rikicin Rivers

Chief George ya ce abin mamaki ne yadda ake samun rikicin siyasa a Ribas, musamman janye jami’an tsaro daga shugaban majalisa da aka zaɓa tare da barin tsohon da aka tsige da kariya.

Kara karanta wannan

'Magagin faduwa zabe bai sake shi ba,' Fadar shugaban kasa ta tankawa Peter Obi

Ya kuma soki majalisar tarayya kan amincewa da dakatar da Siminalayi Fubara, yana mai cewa hakan ya saba doka domin ba a sami rinjayen kashi biyu bisa uku na ’yan majalisa ba.

Jaridar Punch ta rahoto tsohon mataimakin shugaban PDP yana cewa:

"A jihar Ribas, an dakatar da Gwamna Fubara, mataimakinsa da ’yan majalisa, kuma majalisar tarayya ba tare da rinjayen kashi biyu bisa uku ba, ta amince da wannan matakin."

Jigon na PDP ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta daukar mataki domin ceto dimokuradiyyar kasar daga wannan abin kunya.

Bode George ya soki INEC kan Natasha

Bode George ya kuma soki majalisar dattawa da hukumar zaɓe ta kasa (INEC) kan yadda suka yi watsi da koke-koken Natasha Akpoti-Uduaghan kan Akpabio.

Haka kuma, ya soki yunkurin da ake yi na yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye daga majalisa, yana mai cewa wannan abin kunya ne ga Najeriya.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas

Ya bayyana dakatar da ita da daga majalisar kuma yunkurin yi mata kiranye a matsayin wani abu da zai jawo dimokuradiyyar Najeriya ta raunana.

"Sanatoci ba su da 'ya'ya mata ne?" - Bode George

Bode George ya zargi INEC da rashin gaskiya a yunkurin yi wa Sanata Natasha kiranye
Bode George ya dauki zafi kan yadda ake yunkurin yi wa Sanata Natasha kiranye. Hoto: @Naija_PR
Asali: Facebook

Ya zargi INEC da rashin gaskiya, yana mai cewa hukumar a farko ta ki amincewa da batun yi wa Natasha kiranye, amma cikin sa’o’i 24 sai ta sauya matsayi.

"Kalli yadda aka yi wa Natasha taron dangi a majalisa. Waɗannan sanatocin ba su da ’ya’ya mata ne? A yayin da rashin tsaro, cin hanci da talauci ke addabar ƙasa, shin lamarin Natasha shine mafi muhimmanci? Ita mamba ce mai karfi a PDP, kuma ba za mu bari a ci mata mutunci haka ba,"

- inji Bode George.

George ya jinjinawa Sanatoci kamar su Aminu Tambuwal, Seriake Dickson da Enyinnaya Abaribe da suka bijire wa wannan abin da ya kira cin zarafin majalisa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi barazanar da ya yi wa Wike kan rasa mukaminsa, ya ba shi mamaki

Bode George ya soki Tinubu kan tafiya Faransa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan tafiyarsa zuwa Faransa.

Bode George ya ce bai dace shugaban kasar ya bar Najeriya ba a yayin da kasar ke fama da manyan kalubale da ke bukatar kulawarsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel