Hausawa da Fulani Sun Gwabza Fada a Zamfara, an Zubar da Jini

Hausawa da Fulani Sun Gwabza Fada a Zamfara, an Zubar da Jini

  • Rikici ya barke tsakanin Fulani makiyaya da al’ummar Hausawa a Makarantar Firamare ta Dan Sokoto Model a Bungudu, Jihar Zamfara
  • Rahotanni sun nuna cewa wani matashi mai shekaru 17, Abbas Sani, ya rasa ransa a rikicin bayan an tsinci gawarsa cikin jini
  • Jami’an tsaro sun kaddamar da farmaki a yankin da abin ya faru, inda suka cafke mutane 15 da ake zargi da hannu a haddasa rikicin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Wani mummunan rikici ya barke tsakanin Fulani makiyaya da al’ummar Hausawa a garin Bungudu, Jihar Zamfara, yayin bikin Sallah karama a ranar 1 ga Afrilu, 2025.

Bayanai sun nuna cewa hatsaniyar ta faru ne a harabar Makarantar Firamare ta Dan Sokoto Model, inda lamarin ya rikide zuwa tashin hankali.

Kara karanta wannan

Matashi ya mutu, 1 kuma rai a hannun Allah bayan artabu kan budurwa a bikin sallah

Zamfara
An yi fada tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa a Zamfara. Hoto: Nigeria Police
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kai ruwa rana a wajen rikicin ne a cikin wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar wani matashi mai shekaru 17, Abbas Sani, wanda ya ke zaune a kauyen Kuga.

Jami’an tsaro sun bayyana cewa sun kaddamar da bincike mai zurfi bayan aukuwar rikicin, wanda ya kai ga kama mutane 15 da ake zargi da hannu a lamarin.

An tsinci gawar matashi jina-jina

Wani ganau ya shaida cewa bayan hargitsi ya barke, an tsinci gawar Abbas Sani cikin jini a harabar makarantar.

A cewarsa, an garzaya da shi zuwa Asibitin Karamar Hukumar Bungudu domin a ba shi agajin gaggawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Bayan haka, an ajiye gawarsa a dakin ajiye gawa na asibitin, yayin da jami’an tsaro suka ci gaba da daukar matakan tsaro a yankin domin hana barkewar sabon tashin hankali.

Kara karanta wannan

Uromi: Barau ya yi alkawari bayan ziyarar iyalan Hausawan da aka kashe a Edo

‘Yan sanda sun kama mutane 15

Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun gudanar da sintiri a yankin domin dakile rikicin da kuma cafke wadanda ke da hannu a ciki.

Bayan wani samame da suka kai, an kama mutane 15 da ake zargi da tayar da fitina da haddasa asarar rai.

Yan sanda
Yan sanda sun kama mutane 15 bayan rikici a Zamfara. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da kama mutanen, tana mai cewa za a ci gaba da bincike don gano musabbabin rikicin da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da laifi.

An bukaci kwantar da hankali a Zamfara

Duk da matakan da jami’an tsaro suka dauka, wasu shugabannin al’umma sun bukaci a zauna lafiya, domin kauce wa ci gaba da rikici.

A yanzu haka dai al'ummar yankin sun zuba ido domin ganin irin matakin da 'yan sanda za su dauka na kamo sauran da ake zargi da aikata lafin da kuma hukunta su.

Kara karanta wannan

'An ba ni cin hancin Naira biliyan 5 domin tsige Fubara,' Ehie ya yi zazzaga

Rikicin makiyaya da manoma a Arewa

Rikicin makiyaya da manoma a Arewacin Najeriya ya samo asali ne daga rikici kan filaye da albarkatu tsakanin Fulani makiyaya masu kiwon dabbobi da manoma Hausawa da sauran kabilu.

Makiyaya na bukatar filaye masu faɗi da yabanya don kiwon dabbobinsu, yayin da manoma ke buƙatar ƙasa mai karfi don noma abinci.

A sakamakon yawaitar fari, sare dazuka, da bunkasar noma, wuraren kiwo sun ragu a Arewa, lamarin da ke haddasa rikici yayin da dabbobi ke shiga gonaki suna lalata amfanin gona.

A wasu lokutan, rikicin kan dauki salo na kabilanci ko addini, inda ake kai farmaki kan kauyuka da kuma daukar fansa.

Rikicin ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi, tare da rura wutar rashin tsaro a yankin.

Duk da kokarin gwamnati da kungiyoyin tsaro na kawo karshen matsalar, har yanzu tana ci gaba da barazana ga zaman lafiya da harkokin noma a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya yi magana da babbar murya kan kisan 'yan Arewa a Edo

Wannan matsalar ce ta habaka zuwa sace-sacen mutane da ake yi a wasu yankunan kasar, musamman Arewa maso Yamma.

Jihohin da suka fi shan fama da wannan labari sun hada da Zamfara, Katsina, Kebbi, Kaduna da kuma Benuwai da Niger a yankin Arewa ta Tsakiya.

Kisan Edo: Gwamnan Sokoto ya yi magana

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu ya yi Allah wadai da kisan Hausawa a jihar Edo suna kan hanyar dawowa gida.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci jami'an tsaro su tabbatar da sun kama masu hannu a laifin tare da gurfanar da su a gaban alkali.

Gwamnan na cikin fitattun mutanen Arewa a suka yi magana domin ganin an yi adalci ga 'yan farautar da aka kashe ba tare da an same su da wani laifi ba.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel