Abin Boye Ya Fito Fili: Dalilin Shugaba Tinubu Na Korar Mele Kyari daga NNPCL
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi garambawul a kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) a ranar Laraba, 2 ga watan Afirilun 2025
- Mai girma Bola Tinubu ya sauke Mele Kyari da mambobin kwamitin gudanarwa na NNPCL sannan ya maye gurbinsu da sababbi
- Jami'ai a fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa wannan sauyin na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na bunƙasa ɓangaren mai a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A ranar Laraba, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da korar Mele Kyari da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na kamfanin NNPCL.
Jami'ai a fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa korar ta samo asali me sakamakon yadda suke tafiyar da ayyukansu da gazawa wajen cimma manufofin samar da mai.

Asali: Getty Images
Jaridar The Punch ta rahoto cewa wasu jami'an da suka nemi a sakaya sunansu ne suka sanar da ita hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Bola Tinubu ya sauke Mele Kyari
A wani yunƙuri na bazata a ranar Laraba, Tinubu ya sauke Mele Kyari, wanda ya jagoranci kamfanin NNPCL tun daga 2019, sannan ya maye gurbinsa da sababbin shugabanni.
Fadar shugaban ƙasa ta ce an sauke Kyari ne a matsayin wani ɓangare na garambawul domin bunƙasa samar da ɗanyen mai da iskar gas a Najeriya.
Jami’an fadar shugaban ƙasa da suka san yadda lamarin ya wakana sun ce wannan sauyi ya danganci yanayin yadda ake tafiyar da kamfanin na NNPCL.
Sun bayyana cewa waɗanda suke riƙe da muƙaman suna ta kwan gaba kwan baya kuma kuma wasu daga cikinsu sun zama ɓangare na matsalar, maimakon su zama mafita.
Meyasa Tinubu ya yi sauyin shugabanci a NNPCL?
Jaridar Daily Trust ta ce wata majiya ta bayyana cewa tuni aka yi niyyar korar Mele Kyari, amma Tinubu ne ya kawo tsaiko a shirin.
Wani jami'i, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin magana kan lamarin ba, ya bayyana cewa:
"Shugaban ƙasa ya ɗauki wannan mataki ne saboda muna buƙatar yin abubuwa daban. Waɗanda suka riƙe muƙaman a baya sun jefa mu cikin wani hali, har wasu daga cikinsu suka zama matsala maimakon su kawo mafita."
"Dole ne a samu sabon shugabanci. Muna bukatar sababbin mutane da za su kawo sababbin dubaru a cikin tsarin."
"Ku duba su. Kowannensu ƙwararre ne a harkar masana’antar mai. Su na da ƙwarewa sosai, sun san yadda masana’antar ke tafiya. Ba ƴn siyasa ba ne."
"Wannan shi ne karon farko da muke da kwamitin shugabanni da suka kunshi tsantsar ƙwararru."

Asali: Twitter
Tinubu na son sababbin jini a NNPCL
Wani jami’i da ya san batun ya ce Shugaban ƙasa na da imanin cewa dole ne a samu sababbin jini domin inganta samar da mai.
"Ko da yaushe ana buƙatar sababbin masana da za su kawo ci gaba ta hanyoyin zamani. Shugaban ƙasa yana da ajandarsa, kuma an bayyana hakan a cikin sanarwar."
"Ya gaya musu manufarsa, kamar yawan ɗanyen mai da muke fitarwa. Ya buƙaci su duba dukkan rijiyoyin mai don a san waɗanda ke aiki da waɗanda ba sa aiki."
"Dole ne mu inganta waɗanda ba sa aiki. Ya buƙaci su tantance dukkan kadarorinmu a cikin wani takaitaccen lokaci domin tabbatar da samar da mai."
"Nan da shekarar 2030, dole ne mu riƙa samar da ganga miliyan uku na ɗanyen mai a kullum, kuma daga yanzu zuwa 2027, dole ne mu tabbatar da cewa muna fitar da ganga miliyan biyu a kullum."
"Sannan, a ɓangaren iskar gas, dole ne mu samar da biliyan 10 na cubic meters daga yanzu zuwa 2030. Waɗannan su ne matakan auna nasara, kuma haka ya kamata a yi."
- Wani jami'i
Martanin ƴan Najeriya kan sauke Kyari
A wani labarin da muka kawo muku kun ji cewa ƴan Najeriya sun bayyana mabambantan ra'ayoyi kan sauke Mele Kyari daga shugabancin kamfanin NNPCL da Shugaba Bola Tinubu ya yi.
Hakan na zuwa ne dai bayan shugaban ƙasan ya sanar da yin sauyin shugabancin kamfanin NNPCL wanda hakan ya taɓa mutane da yawa.
Asali: Legit.ng