Ana tsaka da Bikin Sallah, Bello Turji Ya Ragargaza Kauye Guda a Sakkwato
- Shahararren dan bindiga, Bello Turji, ya kai farmaki kan wasu manoma a garin Lugu da ke karamar hukumar Isa, a Sakkwato
- An ce Turji na dawowa ne daga wata ziyarar Sallah da ya kai a Isa lokacin da ya kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 11
- Mazauna yankin sun ce tun ranar Asabar aka samu labarin shirin Turji na kai ziyara zuwa gabashin Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni
- Sun kara da cewa an mika bayanan sirri ga hukumomi domin su dauki matakin hana hakan, amma ba a yi komai a kai ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto – Fitinannen dan bindiga, Kachalla Bello Turji, ya kashe manoma 11 a garin Lugu, karamar hukumar Isa, jihar Sakkwato, da safiyar Laraba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Turji na dawowa ne daga ziyarar Sallah a wata al’umma da ke Isa lokacin da ya kai harin.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin Isa, Basharu Altine Giyawa, ya ce tun ranar Asabar aka samu labari kan shirin ziyarar Turji zuwa gabashin Gatawa a karamar hukumar Sabon Birni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An sanar da hukumomi shirin Bello Turji
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Basharu Altine Giyawa ya bayyana cewa an mika wannan bayani ga hukumomi domin daukar matakin gaggawa.
Ya ce:
"Amma jiya, Turji da mutanensa sun bar kauyensa, Fakai, da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, suka bi ta wasu garuruwanmu a Isa, suka yi bikin Sallah, sannan suka kashe manoma 11 a hanyarsu ta komawa Fakai."
Giyawa ya dora alhakin kisan kan hukumomin tsaro bisa gazawar su wajen daukar mataki kan bayanan sirri da aka basu.
'Mun samu rahoto kan Turji,' Dan majalisa

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano
Hon. Aminu Boza, dan majalisar dokokin jihar Sakkwato daga yankin, ya tabbatar da samun rahoton, amma ya dage kan cewa Turji bai kai ziyarar Sallah ko’ina a yankinsa ba.
Boza ya ce:
"Eh, an sanar da mu shirin ziyarar Turji zuwa gabashin Gatawa, kuma mun dauki matakin gaggawa. Mun je Sabon Birni kuma mun dauki matakan tsaro don hana hakan. Wataƙila hakan ne ya sa ya fusata ya kashe manoma marasa laifi a Isa."

Asali: Twitter
Haka kuma, rahotanni sun nuna cewa Turji ya tsaya a garin Tozai, inda ya kashe shugaba kungiyar sa-kai na yankin.
Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce kawai sojoji ne za su iya tabbatar da harin, domin su ne ke aiki a yankin.
Turji: Sojoji na koyon sababbin dabarun yaki
A baya, kun samu labarin cewa Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ya ce an dauko hanyar magance matsalar tsaro a sassa daban-daban na kasar.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake kaddamar da shirin horas da dakarun Najeriya 800 a jihar Kaduna domin kara musu ƙarfi wajen yaki da 'yan ta’adda irinsu Bello Turji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng