"An Yi Rashi," Shugaba Tinubu Ya Yi Magana da Allah Ya Karɓi Rayuwar Galadiman Kano
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta'aziyyarsa bisa rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi
- Tinubu ya bayyana marigayin da dattijo, wanda ya ba da gagarumar gudummawa a masarautar Kano da Najeriya baki ɗaya
- Marigayin, wanda ya rasu yana da shekaru 92 a duniya, shi ne mahaifin shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhini bisa rasuwar Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban jigo a masarautar Kano.
Marigayin ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 92 a duniya bayan fama da doguwar jinya.

Asali: Twitter
Alhaji Abbas Sanusi, wanda aka nada Galadiman Kano ya kasance daya daga cikin manyan dattawan masarautar Kano, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi jana'izar Galadiman Kano
Ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban masarauta da al’ummar jihar Kano baki daya.
Marigayin ya rasu ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama, ciki har da Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi jana’izarsa a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu da misalin karfe 10:00 na safe a yau Laraba 2 ga watan Afrilun 2025.
Manyan mutane da ƴan siyasa da suka haɗa da jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf sun halarci jana'azar Galadiman Kano.
Bola Tinibu ya yi alhinin wannan rashi
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da ɗaukacin al'ummar jihar Kano bisa wannan rashi da aka yi.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin ginshikin masarautar Kano da kuma ci gabanta.
Ya ce irin gudunmawar da Alhaji Abbas Sanusi ya bayar tun lokacin da aka nada shi sarauta, ba za a manta da ita ba.

Kara karanta wannan
Abin da Buhari ya ce bayan rasuwar dattijo, Galadiman Kano, ya fadi giɓin da ya bari
A cewarsa, marigayin ya kasance jigo mai kokari a harkokin masarauta da al’adu, wanda ya taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummar Kano da Najeriya baki daya.

Asali: Twitter
Tinubu ya mika ta'aziyya ga gwamnatin Kano
Bola Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar Kano, majalisar masarautar Kano, da kuma iyalan mamacin bisa wannan babban rashi.
Ya ce masarautar Kano ta yi babban rashi, kuma Najeriya gaba daya za ta yi kewar irin dattako da basirar da marigayin ke da su.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya saka masa da Aljannar Firdausi, tare da bai wa iyalansa da daukacin al’ummar jihar Kano hakurin jure rashinsa.
Tuni manyan ‘yan siyasa da shugabanni daga sassa daban-daban na kasar nan suka fara bayyana alhininsu kan rasuwar Galadiman Kano.
Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Galadiman Kano
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi jimami da alhinin rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.
Buhari ya ƙara da cewa babu tantama wannan babban rashi ne ba ga iya jihar Kano kadai ba har ma da Arewa da kuma Najeriya baki daya.
Asali: Legit.ng