"Ku Ɗauki Kowa a Matsayin Ɗan Gida," Sarkin Musulmi Ya Tura Saƙo ga Gwamnoni

"Ku Ɗauki Kowa a Matsayin Ɗan Gida," Sarkin Musulmi Ya Tura Saƙo ga Gwamnoni

  • Mai alfarma Sarkin musulmi ya buƙaci gwamnonin Najeriya su daina nuna banbanci tsakanin mazauna jihohinsu
  • Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya ce jihar Sakkwato suna ɗaukar kowane mutumin da ke rayuwa a matsayin a ɗan gida
  • Ya buƙaci sauran jihohi su yi koyi da wannan domin tabbatar da zaman lafiya da kyautata zamantakewa tsakanin ƴan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci gwamnonin da su dauki duk wani dan Najeriya da ke zaune a jiharsu a matsayin dan gida.

Mai alfarma Sarkin musulmi ya yi wannan kira ne yayin ziyarar Barka da Sallah da ya kai wa Gwamna Ahmed Aliyu a masaukin shugaban ƙasa da ke Sokoto.

Sultan.
Sarkin Musulmi ya bukaci gwamnoni su ɗauki kowa ne mazaunin jiharsu a matsayin ɗan gida Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

A cewarsa, a Sokoto duk ‘yan Najeriya ana daukar su ‘yan asalin jiha ne, hakan yana ba su damar jin cewa suna da cikakken matsayi a cikin al’umma, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Musulmi sun ba Hausawa shawara kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Sakkwato ta ɗauki ƴan Najeriya

Sarkin Musulmi ya ce:

“A Sokoto, ba mu da baki, sai dai al’ummomi daban-daban da ke zaune a nan,” in ji shi.

Sarkin Musulmi ya bukaci sauran jihohi su yi koyi da wannan tsari domin tabbatar da zaman lafiya, hadin kai, da kuma zamantakewa mai kyau tsakanin ‘yan kasa.

Wane saƙo Sarkin Musulmi ya aikawa gwamnoni?

Ya jaddada muhimmancin gwamnonin su ba da fifiko wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummarsu, yana mai cewa tsaro shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma.

“A Sokoto, mu na jin dadin ayyukan da gwamna ke yi, kuma muna tabbatar masa da goyon bayan masarauta domin ya ci gaba da aikin alheri da yake yi wanda mu ke fatan zai kawo sauyi,” in ji Sarkin.

Sultan ya kara da cewa, namijin kokarin da Gwamna Aliyu da hukumomin tsaro ke yi ya haifar da gagarumin ci gaba a yaki da ‘yan bindiga a jihar Sakkwato.

Kara karanta wannan

Atiku ya mayar da hankali kan tausaya wa talaka a sakon barka da sallah

Gwamma Aliyu ya gano tushen matsalar tsaro

A nasa jawabin, Gwamna Aliyu ya jaddada kudurin gwamnatinsa na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

Ya alakanta matsalar tsaron da ake fama da ita da rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa.

“Mun horar da dubban matasa da mata sana’o’i daban-daban domin su zama masu dogaro da kai. Mu na shirin kaddamar da wani shirin koyar da sana’o’i domin rage zaman banza da rigima tsakanin matasa,” in ji shi.

Gwamnan ya nanata cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa addinin Musulunci fifiko, ya ce za a ci gaba da kula da Masallatai da makarantun Islamiyya yadda ya kamata.

Ya gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’in da suke yi da kuma goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Me ya kamata mutane su yi wa shugabanni?

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Musulmi ya buƙaci ƴan Najeriya da su guji yin amfani da kalmomin ɓatanci da rashin ɗa'a wajen tura ƙorafinsu ga shugabanni.

Ya kuma shawarci jama'a da su sanya shugabanninsu a addu'a domin Allah ya ba su damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel