Duk da Kakaba Haraji, Najeriya Ta Kawar da Kai, Ta Cigaba da Taimakon Nijar

Duk da Kakaba Haraji, Najeriya Ta Kawar da Kai, Ta Cigaba da Taimakon Nijar

  • Najeriya na ci gaba da kokarin rage wahalhalun tattalin arziki a Nijar, amma ana fargabar yadda ake samar da man fetur zuwa kasar
  • An ga tankar mai, wadda ake zargin mallakin AA Rano ce, tana jigilar man fetur zuwa kasar Nijar, lamarin da ya haifar da tambayoyi
  • Wannan na faruwa ne yayin da Najeriya ke kokarin daidaita bukatun cikin gida da kuma taimakawa Nijar da ke fama da wahala
  • Hakan ya biyo bayan kakaba haraji kan Najeriya da ƙasashen Nijar, Mali da kuma Burkina Faso suka yi kan kayayyakin da ake kawo wa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Niamey, Nijar - Kasar Nijar na ci gaba da fuskantar matsalolin wadataccen man fetur da ke neman tagayyara ta.

Najeriya na ci gaba da kokarin rage wahalhalun tattalin arziki a kasar Nijar, amma ana fargabar samar da man fetur (PMS) zuwa kasar makwabta.

Kara karanta wannan

Yadda Nijar, Mali da Burkina Faso suka kakabawa Najeriya, ECOWAS haraji

Najeriya na ci gaba da taimakon Nijar ɓangaren mai
Har yanzu ana fama da ƙarancin mai a Nijar yayin da Najeriya ke taimaka mata. Hoto: Bayo Onanuga, Muhammad Badamasi.
Asali: Facebook

Nijar sun kakabawa Najeriya, mambobin ECOWAS haraji

Rahotan Zagazola Makama ya ce wahalar man a kasar na karuwa yayin da Najeriya ke kokarin samar da man domin saukaka makwabciyar nata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga kungiyar tattalin arzikin Afrika ta Yamma, ECOWAS.

Kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun kakaba harajin kashi 0.5% kan kayayyakin da ke shigowa daga kasashen ECOWAS.

Wannan mataki ya kara dagula dangantaka tsakanin wadannan kasashe da ECOWAS bayan ficewarsu daga kungiyar a farkon shekarar nan.

Kungiyar kasashen da aka fi sani da AES na kokarin kafa hadin gwiwar tattalin arziki mai karfi bayan fara hadin gwiwar tsaro tun 2023.

Harajin na iya haddasa tashin farashi, durkushewar kasuwanci da kuma raunana hadin kai na tattalin arzikin yankin.

Nijar na fuskantar matsalar mai a Najeriya
Najeriya ta ci gaba da taimakon Nijar da man fetur bayan matsalar da ta shiga. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Wahalar mai da ake ciki a kasar Nijar

Lamura na neman tsayawa a Nijar tun a kwanakin baya saboda matsalolin rashin wadatuwar man fetur a cikin ƙasar.

Kara karanta wannan

Shugaban hadakar PDP ya yi Allah wadai da jita-jitar da ake yada wa kan Atiku

Rahotanni na nuni da cewa rashin man fetur ya hana harkokin kasuwanci da zirga-zirga a Nijar tsawon makonni biyu.

An ruwaito cewa gwamnatin mulkin sojan Nijar ta tura wakilai zuwa birnin Abuja domin rokon Najeriya ta tura mata mai.

An 'gano' tankokin AA Rano a Nijar

Biyo bayan lamarin, Najeriya ta amince da bayar da taimako ta hanyar aikawa da motoci 300 cike da mai zuwa jamhuriyyar Nijar.

An ga tankar mai, wadda ake zargin mallakin AA Rano ce, tana jigilar man fetur zuwa Nijar, lamarin da ya haddasa tambayoyi game da asalin wadannan kaya.

Wannan lamari na faruwa ne yayin da Najeriya ke kokarin daidaita bukatun cikin gida da kuma tallafawa makwabciyarta da ba su ga maciji a wasu ɓangarori.

Halin rashin man fetur a Nijar

A baya, kun ji cewa Kasar Jamhuriyar Nijar na fama da wani matsanancin karancin fetur, lamarin da ya haddasa dogayen layuka a gidajen mai.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi martani ga Amurka kan zargin kashe kiristoci karkashin Tinubu

Majiyoyi sun tabbatar da cewa safarar man fetur daga Najeriya zuwa Nijar na karuwa sakamakon matsalar da kasar ke fuskanta da ya yi mata katutu.

Hukumar mai ta Nijar ta ce kamfanin SORAZ ba zai iya samar da isasshen mai ba don biyan bukatun 'yan kasar ba duba da yawan bukatar haka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel