Mutane Sun Mutu da Wasu Jirage Suka Gamu da Hatsari ana cikin Shagalin Sallah a Najeriya
- An shiga jimami da wasu jiragen ruwa biyu suka yi karo a gabar ruwan da ke yankin Ijaw ta Kudu a jihar Bayelsa
- Rahoto ya bayyana cewa hatsarin ya laƙume rayukan mutum biyu yayin da wasu 13 suka ɓata a ruwa har yanzu ba a gano su ba
- Rundunar ƴan sanda ta ce babu wanda ya kai mata rahoton faruwar hatsarin amma ta fara bincike don gano abin da ya auku
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa - Mutane biyu sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya rutsa da su a karamar hukumar Ijaw ta Kudu da ke jihar Bayelsa.
An tattaro cewa wasu fasinjoji 13 sun ɓace sakamakon hatsarin jirgin da ya afku a gabar ruwa ta Akede da ke Kudancun Ijaw.

Asali: Original
Jiragen ruwa 2 sun gamu da hatsari
Daily Trust ta kawo rahoton cewa hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da wani jirgin ruwa mai gudu dauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa hatsarin ya girgiza mazauna yankin, inda da dama suka taru a wajen domin kokarin ceto wadanda suka fada cikin ruwa.
Majiyar ta ce wasu masu nutso sun shiga cikin ruwa domin kokarin gano sauran fasinjojin da ba a gansu ba, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane biyu nan take.
Yadda jiragen suka ci karo a cikin ruwa
An ji cewa jirgin mai suna Meeting Marine, wanda ke dauke da inji mai karfin 115HP, ya taso ne daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa lokacin da ya yi karo da jirgin kamun kifi a kusa da Akede.
Matukin jirgin, wanda aka bayyana sunansa da Saturday, ya gaza kauce wa jirgin masu kamun kifin saboda gudu, lamarin da ya haddasa afkuwar wannan mummunan hadari.
Shugaban kungiyar Ma'aikatan Ruwa ta Najeriya reshen Jihar Bayelsa, Kwamared Ogoniba Ipigansi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Asali: Getty Images
Ya ce an sanar da su abin da ya afku, amma matsalar rashin ingantaccen sadarwa a yankin ta hana su ƙawo ɗaukin gaggawa domin ceto waɗanda lamarin ya shafa.
"A halin yanzu dai ana ci gaba da kokarin ceto mutanen da suka bata, tare da hadin gwiwar mazauna yankin da masu ruwa da tsaki a fannin sufuri a jihar," in ji shi.
Rundunar ƴan sanda ta fara bincike
A bangaren hukumomi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Bayelsa, DSP Musa Muhammad, ya bayyana cewa har yanzu ba a kai rahoton hatsarin ofishinsu ba
Ya ce duk da haka, rundunar ta fara bincike domin tabbatar da gaskiyar al’amarin da kuma daukar matakan da suka dace.
Mazauna yankin sun bukaci hukumomi da su dauki matakan inganta tsaro da bin ka’idojin sufurin jiragen ruwa domin hana afkuwar irin wannan hatsari nan gaba.
Jirgin ruwa ya nutse a jihar Ribas
A wani labarin, kun ji cewa wani jirgin ruwa da ya ɗauko mutane sama da 20 ya gamu da mummunan hatsari bayan ya taso daga Fatakwal zuwa Bonny a jihar Ribas.
Bayanai sun nuna cewa jirgin ya yi tangal-tangal sakamakon wata guguwa mai ƙarfi da ta tashi ba zato ba tsammani, daga bisani kuma ya nutse a ruwa.
Asali: Legit.ng