Ayyukan Alheri, Kushe da Sukar da aka Yi wa Kyari Lokacin da Yake Shugaban NNPCL

Ayyukan Alheri, Kushe da Sukar da aka Yi wa Kyari Lokacin da Yake Shugaban NNPCL

An fara magana kan ayyukan da tsohon shugaban NNPCL, Mele Kyari ya yi da suka jawo masa yabo ko suka bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi.

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauke shugaban kamfanin man Najeriya na NNPCL, Mele Kyari.

Abubuwa da dama da suka shafi harkokin mai sun faru a lokacin Mele Kyari wanda mutane suka yabe shi a kai ko kuma suka soke shi.

Mele Kyari
An samar da tashar lantarki a lokacin Mele Kyari a Maiduguri. Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da suka faru a NNPCL a lokacin da Mele Kyari ke rike da kamfanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Samar da wutar lantarki a Maiduguri

A ranar Alhamis, 2 ga watan Maris, 2022 Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin wutar lantarki na gaggawa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Kara karanta wannan

Bayan sauke Mele Kyari, Tinubu ya yi sababbin nade nade 9 a kamfanin NNPCL

Buhari
Buhari na jawabi a lokacin kaddamar da tashar wutar Maiduguri. Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

An yi aikin da ke da karfin megawatt 52 ne don samar da wutar lantarki mai dorewa ga garin Maiduguri da kewaye.

NNPCL ne ya aiwatar da aikin bayan umarnin da Buhari ya bayar a shekarar 2021, don samar da wutar lantarki a Maiduguri da kewaye.

Dalilin gina tashar wutar lantarkin

A cikin shekaru da suka gabata, hare-haren 'yan ta’adda da kuma barnar da aka yi wa kayayyakin wutar lantarki sun haddasa matsalar yanke wuta a Maiduguri da kewaye.

Rashin wutar lantarki ya haifar da durkushewar tattalin arzikin yankin, lamarin da ya sanya Muhammadu Buhari a watan Afrilun 2021 ya umarci NNPCL da ya gaggauta daukar mataki.

A sakamakon haka, bayan tattaunawa da gwamnatin Borno, NNPCL ya gina tashar wutar lantarki mai amfani da iskar gas da ke da karfin megawatt 50 domin samar da wuta a Maiduguri.

Ana ganin aikin na cikin nasarorin da Mele Kyari ya samu a kamfanin NNPCL duk da cewa shi ma dan asalin jihar Borno ne.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sauke Mele Kyari da manyan shuabannin kamfanin NNPCL

Maiduguri
Tashar wutar Maiduguri mai amfani da iskar gas. Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

2. Farfado da matar Fatakwal

A watan Nuwamban 2024 kamfanin NNPCL ya sanar da farfadowar matatar mai ta Fatakwal da ke jihar Rivers.

Rahoton Channels TV ya nuna cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya NNPCL murna bisa nasarar da ya samu wajen farfado da matatar.

NNPCL
Motoci na lodin mai bayan farfado da matatar Fatakwal
Asali: Facebook

Tinubu ya kuma jinjinawa tsohon shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya assasa gyaran matatun tare da gode wa bankin Afreximbank da ya amince da bayar da kudin aikin.

Shugaban NNPCL na wancan lokacin, Mele Kyari ya sha yabo ganin cewa an dade ana kokarin ganin matatun man Najeriya sun dawo aiki.

3. Farfado da matatar Warri

A watan Disambar 2024 Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL) ya tabbatar da cewa ya kammala aikin gyaran matatar man fetur ta Warri tare da dawo da ita aiki bayan dogon lokaci tana tsaye.

A cewar sanarwar da NNPCL ya fitar, matatar Warri ta fara aiki ne a ranar 30 ga Disamba, inda kashi 60% na matatar ya fara aiki.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Yadda Edwin Clark da fitattun ƴan siyasa 4 suka mutu a 2025

Mele Kyari
Mele Kyari da wasu ma'aikata a matatar Warri. Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Gyaran matatar na cikin shirin farfado da matatun man fetur na kasar da aka fara karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Kamar matatar Fatakwal, wannan ma ana lissafa shi a matsayin manyan nasarorin da Mele Kyari ya samu a lokacinsa.

4. Taron Qur'ani na kasa a Abuja

An samu ce-ce-ku-ce kan wani taron Qur'ani da aka yi kokarin shirya wa a watan Fabrairun 2025 a Abuja.

A cewar Trust Radio, Sheikh Jalo Jalingo ya ce Mele Kyari ne ya zo da wannan tunani tare da gayyatar kungiyoyin addini domin cimma wata kyakkyawar manufa.

Shugaban Izala
Shugaban malaman Izala, Dr Jalo Jalingo. Hoto: Jibwis Najeriya
Asali: Depositphotos

Sheikh Jalo ya kara da cewa shirin zai amfanar da al’umma matuka, kuma yana fatan za a ci gaba da gudanar da shi domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai.

A yayin da aka nemi jin ta bakin NNPCL dangane da batun, babban jami’in hulda da jama’a na kamfanin NNPCL, Femi Soneye, ya noke kam amsa tambayar.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya yi magana da babbar murya kan kisan 'yan Arewa a Edo

Daga baya, ya kira jaridar Daily Trust domin karin bayani, inda ya ce:

“Gaskiya ita ce, duk wanda ya san Mele Kyari ya san cewa yana da matukar sha’awar duk wani abu da ya shafi addini.
"Amma a wannan batu, ba shi da hannu wajen shirya taron ko daukar nauyinsa.”

Batun taron da daga cikin abubuwan da wasu suka rika yabon Mele Kyari a kansa yayin da wasu kuma suka rika sukarsa duk da cewa ya nuna ba hannunsa a ciki.

5. Sayar da fetur da Naira ga Dangote

A watan Maris kamfanin NNPLC ya dakatar da sayar da man fetur da Naira wa matatar Dangote, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya.

Biyo bayan fara magana kan lamarin, Premium Times ta wallafa cewa NNPCL ya yi karin bayani kan yarjejeniyar sayar da danyen mai a Naira ga Matatar Dangote.

NNPCL ya ce tun asali yarjejeniya ta kasance ta tsawon watanni shida ne kacal, bisa ga yawan danyen mai da ake da shi a kasa.

Kara karanta wannan

Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin

Dangote
NNPCL ya dakatar da sayar da mai ga matar Dangote da Naira. Hoto: Dangote Industris
Asali: Getty Images

Lamarin ya jawo suka wa shugaban NNPLC na wancan lokacin, Mele Kyari kasancewar hakan ya sanya tashin farashin man fetur a Najeriya.

'Ba a kai hari matatar Fatakwal ba' - NNPCL

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin NNPCL ya musanta cewa 'yan Neja Delta sun kai hari matatar Fatakwal.

NNPCL ya yi karin haske ne a yayin da ake rade radin cewa an kai hari matatar saboda dakatar da gwamna Simi Fubara da aka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng