Shugabannin Musulmi Sun Tunkari Tinubu kan Batun Dakatar da Gwamna Fubara

Shugabannin Musulmi Sun Tunkari Tinubu kan Batun Dakatar da Gwamna Fubara

  • Jagororin musulmi a Ribas ciki har da shugabannin Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci sun tunkari Bola Tinubu kan Simi Fubara
  • Shugabannin musulmai reshen Ribas sun buƙaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dawo da Gwamna Siminalayi Fubara kan mukamisa
  • A cewarsu, duk da rigingimun siyasar da aka jima ana fama da su a jihar Ribas, dakataccen gwamnan ya tafiyar da mulki yadda ya kamata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Shugabannin Musulmi a Jihar Rivers sun bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da cikakken iko ga Gwamna Siminalayi Fubara, wanda aka dakatar.

Wannan kira ya fito ne daga kungiyoyin Musulunci 20 reshen jihar Riibas, ciki har da Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci.

Siminalayi Fubara.
Shugabannin musulmi a jihar Rivers sun nemi Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa jagororin musulmin sun yi wannan kira ne da suka ziyarci Gwamna Fubara a gidansa da ke Fatakwal domin taya shi murnar Sallah.

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane matakai Bola Tinubu ya ɗauka a Ribas?

Idan ba ku manta ba a ranar 18 ga Maris, Shugaban Ƙasa Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas da ke yankin Neja Delta.

Shugaban ƙasar ya kuma dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Odu, da ‘yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Gwamnatin tarayya ta bayyana hare-haren da aka kai kan bututun mai da rikicin siyasar jihar tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike, a matsayin dalilan daukar wannan mataki.

Bugu da ƙari, Shugaba Tinubu ya nada Ibok-Ete Ibas, tsohon hafsan rundunar sojin ruwa ta Najeriya, a matsayin shugaban riko wanda zai jagoranci al'amuran Ribas.

Shugabannin Musulmi sun roki a dawo da Fubara

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Fubara, Nelson Chukwudi, ya fitar, ya ce shugabannin Musulmi sun bukaci Mai Girma Rinubu da ya sake nazari kan batun dokar ta-bacin da ya sa a Ribas.

Kara karanta wannan

Siyasar Rivers: Shugaban riko ya sauke dukkan mutanen da Fubara ya nada

A cewarsa, jagororin musulman Ribas sun kuma yi kira ga shugaban ƙasa ya dawo da Gwamna Fubara kan mukaminsa.

Shugabannin Musulmin sun jaddada cewa duk da rikicin siyasa, Gwamna Fubara na gudanar da mulki cikin kwarewa da sanin ya kamata.

Sir Siminalayi Fubara.
Gwamna Fubara ya samu goyon bayan Musulmi Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Musulmai a jihar Ribas na tare da Fubara

Da yake jawabi a madadin al’ummar Musulmi, Nasir Uhor ya bayyana cikakken goyon bayansu ga Gwamna Fubara.

Ya kuma tabbatar da cewa za su ci gaba da yin addu’o’i da goyon baya gare shi a yayin da yake kokarin shawo kan kalubalen siyasa da jihar ke fuskanta.

Ya kuma bukaci Gwamnan da ya ci gaba da hakuri, yana mai tunatar da shi cewa addinin Musulunci na koyar da cewa Allah yana sakawa masu juriya da lada mai girma.

Fubara ya faɗi abin da yake damunsa

A wani labarin, kun ji cewa Dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce wani lokacin ya na jin ba daɗi, wani lokacin kuma damuwa game da ayyana dokar ta-baci a jihar.

Fubara, ya bayyana cewa a halin yanzu ya bar dukkan al’amuran rikicin jihar a hannun Ubangiji domin kawo mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262