Gwamna Nwifuru Ya Fusata, Ya Umarci Cafke Kwamishinoni 5? An Ji Gaskiya

Gwamna Nwifuru Ya Fusata, Ya Umarci Cafke Kwamishinoni 5? An Ji Gaskiya

  • Gwamnatin jihar Ebonyi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Franics Nwifuru ta musanta wasu rahotanni da aka yaɗa a kanta
  • Ta musanta cewa Gwamna Francis Nwifuru ya umarci a cafke wasu kwamishinoni guda biyar da ke aiki a ƙarƙashinsa
  • Hakazalika, rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi ta bayyana cewa babu wani kwamishina da ta cafke da ke tsare a hannunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ebonyi - Gwamnatin jihar Ebonyi ta yi magana kan rahotannin da ke cewa Gwamna Francis Nwifuru ya ba da umarnin cafke kwamishinoni biyar.

Gwamnatin ta ƙaryata rahoton da ke cewa Gwamna Nwifuru ya ba da umarnin kama kwamishinonin guda biyar saboda jinkirin kammala wasu ayyuka da saɓa ƙa’ida a kwangila.

Gwamna Francis Nwifuru
Gwamna Nwifuru ya umarci a cafke wasu kwamishinoni Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin majalisar zartarwa ta jihar Ebonyi kan kula da kammala ayyukan gidaje, Cif Donatus Ilang, ya fitar a Abakaliki.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya caccaki Tinubu, ya fadi sauyin da zai kawo da shi ne shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Ebonyi ta musanta cafke kwamishinoni

Ayyukan da ake magana akai sun haɗa da gina gidaje 140 ga mutanen ƙauyukan Izzo da Amaze, waɗanda rikicin ƙabilanci na Ezilo/Ezza Ezilo ya raba da gidajensu a ƙaramar hukumar Ishielu.

Donatus Ilang, wanda shi ne kwamishina kan harkokin Iyaka, zaman lafiya da warware rikice-rikice, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya maras tushe.

“Babu wani kwamishina da aka kama, kuma za ku iya tabbatar da hakan daga ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro.”
“Mutanen da ke yada irin wannan labari na bogi suna fitar da shi ne daga gurɓataccen tunaninsu.”

- Cif Donatus Ilang

Gwamna Nwifuru bai ji daɗi ba

Ya ƙara da cewa an sanar da kwamishinonin kan rashin jin daɗin gwamna game da jinkirin kammala ayyukan, tare da shirin ɗaukar matakai kan masu laifi.

Kwamishinan ya ce kwamishinonin sun yi alƙawarin samar da dukkan bayanan da za su bai wa kwamitin damar fuskantar ƴan kwangilolin da suka gaza kammala ayyukan.

Kara karanta wannan

Gwamnan Edo ya gana da Barau kan kisan Hausawa, ya fadi shirinsa kan iyalan mamatan

“Gwamna na da burin tallafawa mutanen da rikicin ƙabilanci ya shafa ta hanyar samar musu da matsuguni.”
“Mun bai wa duk masu ruwa da tsaki a aikin lokaci don su bi ƙa’idojin kwangilar. Matsayarmu ita ce tabbatar da cewa an aiwatar da kyawawan manufofin gwamna ga waɗannan al’ummomi, kuma ba za mu yi wasa da hakan ba.”

- Cif Donatus Ilang

Ƴan sanda sun faɗi abin da suka sani

Hakazalika, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Ebonyi, DSP Joshua Ukandu, ya bayyana cewa babu wani kwamishina da ke hannunsu.

“Ba mu kama wani kwamishina ba."

- DSP Joshua Ukandu

Gwamna Nwifuru ya sallami hadimansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya sallami wasu daga cikin hadimansa masu aiki a gwamnatinsa.

Gwamna Francis Nwifuru ya kori hadiman ne guda biyu bisa zargin aikata laifuffukan da suka shafi rashin ɗa'a da cin amanar aiki.

Matakin da Gwamna Nwifuru ya ɗauka ya biyo bayan tabbatar da aikata laifuffukan da ake zarginsu na cin amanar aiki da rashin ɗa'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng