Abubuwa 3 da ba Ku Sani ba game da Marigayi Galadiman Kano
Shugaban majalisar masarautar Kano mafi tsufa kuma babban majibincin al'amuran masarauta, Alhaji Abbas Sanusi, ya rasu yana da shekara 92.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – An kirkiro sarautar Galadiman Kano a lokacin daular Habe, kafin zuwan Fulani a shekara ta 1804.

Asali: Twitter
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan mukami shi ne mafi girma a majalisar masarautar Kano har zuwa shekara ta 1890, lokacin da aka aro sarautar Waziri daga majalisar sarki ta Sakkwato.
A yanzu, sarautar Galadiman Kano ita ce ta biyu a daraja a cikin jerin sarautun masarautar Kano, bayan mukamin Waziri, kuma wanda ke rike da ita ya rasu bayan ya nada sarakuna da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da ya kamata ku sani game da Mama uwar sarakai, da suka hada da;
1. A ina aka haifi marigayi Galadiman Kano?
Daily Nigerian ta ruwaito cewa an haifi marigayi Abbas Sanusi a shekara ta 1933 a karamar hukumar Bichi a Kano, kuma ya fara karatunsa a makarantar firamare ta Kofar Kudu a shekara ta 1944.

Asali: Facebook
Bayan gama firamare, ya zarce zuwa Kano Middle School, wadda yanzu ake kira kwalejin Rumfa, a shekara ta 1948.
A wannan lokaci, ya na tare da marigayi Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim.
2. Yadda aka rika daga likkafar Galadiman Kano
A wata hira da aka yi da shi a lokacin da ya ke raye, Alhaji Abbas Sanusi ya taba bayyana yadda mahaifinsa, Muhammadu Sanusi I, ya ba shi sarautar Sarkin-Dawakin Tsakar Gida.
Nadin, wanda aka yi masa a shekara ta 1959, ya hadu da kara masa matsayi, inda aka nada shi a matsayin Hakimin karamar hukumar Ungogo.
Bayan mahaifinsa ya bar Kano, sabon sarkin Kano, Muhammadu Inuwa, ya nada shi Dan Iyan Kano a shekara ta 1962.
Bayan rasuwar Muhammadu Inuwa, Alhaji Ado Bayero ya zama sarki kuma ya nada shi Wamban Kano.
A wannan mukami na karshe da ya rike kafin rasuwarsa, Malam Muhammadu Sanusi II ne ya nada shi a matsayin Galadima.
3. Yadda marigayi Galadiman Kano ya so zama sarki
Rahoton ya ci gaba da cewa a lokacin da marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya yi jinya a kasashen waje, Alhaji Abbas Sanusi ne ke kula da harkokin masarautar Kano.
Bayan rasuwar Ado Bayero a watan Yuni, Galadiman Kano Abbas Sanusi na daga cikin 'yan gidan sarauta da suka nemi su gaje shi.
Sai dai 'yan majalisar zaben sarki sun karkata ga tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, wanda ya zama sabon sarkin Kano.
Marigayi Abbas Sanusi ya bar 'ya'ya 38 da jikoki fiye da 87.
Ana shirya jana’izar Galadiman Kano
Wata sanarwa daga Alhaji Kabiru Abbas Sanusi, ɗan marigayi Galadiman Kano, ta tabbatar da cewa za a yi jana'izar marigayin a ranar Laraba da 10.00 na safe a Kofar Kudu, fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Alhaji Abbas Sanusi ɗa ne ga marigayi Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na I, kuma mahaifin Abdullahi Abbas, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano.
Galadiman Kano ya rasu
A baya, mun wallafa cewa an wayi gari da labarin rasuwar fitaccen jigon masarautar Kano, Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi. Mamacin, bayan ya sha fama da jinya mai tsawo.
An haifi Alhaji Abbas Sanusi a shekarar 1933, kuma ya taso a cikin gidajen sarauta, ya samu tarbiyya da horo na sarauta daga mahaifinsa, marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng