Abin da Sarki Sanusi II Ya Faɗa Wa Gwamma Abba bayan Ya Yi Hawan Sallah a Kano

Abin da Sarki Sanusi II Ya Faɗa Wa Gwamma Abba bayan Ya Yi Hawan Sallah a Kano

  • Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan ci gaba da yake zuba wa a Kano
  • Sanusi II ya ce ƙoƙarin da gwamnan ke yi na inganta harkokin ilimi, kiwon lafiya noma da tsaro a jihar Kano ya cancanci a jinjina masa
  • Gwamna Abba Kabir ya jaddada godiya ga mai martaba sarkin bisa jagorancin da yake yi da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a Kano

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya jinjinawa Gwamna Abba Yusuf bisa ƙoƙarin da yake yi na inganta ilimi, kiwon lafiya, noma, da tsaro a Kano.

Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya jagoranci ƴan Majalisar Masarautar Kano domin kai gaisuwar Sallah ga gwamnan a fadar gwamnati.

Kara karanta wannan

"Ku sha shagalin Sallah": Gwamna Abba ya tuna da mutanen da ke ɗaure a jihar Kano

Abb ada Sanusi.
Sanusi ya yabawa Gwamna Abba bisa ayyukan ci gaban da yake yi a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Sanusi ya kuma yaba wa Majalisar Dokokin Kano bisa rawar da ta taka wajen dawo da martabar Masarautar Kano, kamar yadda Channels tv ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir

Da yake kwararo yabo ga Abba, basaraken ya ce:

“Mun zo gaisuwa da barka da Sallah da kuma gode maka bisa kokarin da ka ke yi, musamman a fannin ilimi da noma, inda ka samar da kayan aikin gona na zamani a farashi mai rahusa.
“Muna da kwarin gwiwa cewa gwamna zai ci gaba da aikinsa na gari, kuma muna kira ga shugabannin kananan hukumomi su yi koyi da shi.

Sarkin ya bukaci shugabannin kananan hukumomi su zama masu jajircewa wajen gudanar da mulki kuma su riƙe amanar da al’ummarsu ta ba su.

Gwamnan Kano, Abba ya gode wa Sanusi II

A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir ya gode wa Muhammadu Sanisi II bisa jagorancinsa da kuma kokarinsa na inganta zaman lafiya da hadin kai a Kano.

Kara karanta wannan

'Mu na zaman makoki, su na hawan Sallah,' Sarki Sanusi ya fusata wasu

“Muna gode wa Allah da ya ba mu damar ganin wannan rana. Yana daga cikin al’ada cewa a irin wannan rana, Sarki da mukarrabansa su kawo mana gaisuwar Sallah,” in ji gwamnan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yabawa Sarkin kan kokarinsa na hadin kan mabiya addini daban-daban a faɗin jihar Kano.

“Sarkinmu jagora ne na kwarai wanda ke kula da jama’arsa. Kokarinsa na hadin kan kungiyoyin addini ya cancanci yabo.

- In ji Abɓa Kabir.

Abba Kabir Yusuf.
Gwamna Abba ya shirya gyara Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Wane shiri Abba ke da shi a Kano?

Gwamna Abba ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na mayar da Kano birni mai ingantaccen tsari da ci gaba.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ta surutu kan hawan sallah da Mai martaba sarki ya yi, wanda daga nan ne ya zarce fadar gwamnatin Abba don kao gaisuwa.

Gwamna Abba ya taimakawa ƴan gidan yari

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya ba da kyautar tulin kayan abinci da shanu 12 ga fursunonin da ke zaune a gidajen gyaran hali a jihar Kano.

Gwamna Abba ya yi haka ne domin tallafa masu, su sanu damar yin shagalin karamar sallah kamar kowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262