Ana Wata ga Wata: An Ayyana Dokar Hana Fita a Jihar Kogi kan Sanata Natasha
- Shugaban karamar hukumar Okehi, da ke Kogi ya kafa dokar hana fita saboda dalilan tsaro, inda ya haramta tarukan jama’a da gangamin siyasa
- Amoka Monday ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne don hana duk wani rikici da ka iya tasowa, tare da tabbatar da doka da oda a yankin
- Sanya dokar hana fita na zuwa ne yayin da gwamnati da 'yan sanda suka hana taruka yayin da Sanata Natasha Akpoti ke shirin dawowa gida
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Shugaban karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi, Amoka Monday, ya kafa dokar hana fita a duk fadin yankin karamar hukumar.
Ya bayyana cewa an sanya dokar hana fita ne saboda dalilan tsaro, bayan haramta gangamin siyasa da tarukan jama’a marasa tsari a jihar.

Kara karanta wannan
Yunkurin raba Sanata Natasha da kujerarta: An ji abin da INEC za ta yi a kwana 90

Asali: UGC
Kogi: Ciyaman ya sanya dokar hana fita
Umarnin sanya dokar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban karamar hukumar ya sanya wa hannu a ranar Litinin, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar hukumar Okehi na daga cikin kananan hukumomin da Sanata Natasha Okpoti ke wakilata a majalisar dattawa.
Shugaban karamar hukumar ya ce matakin ya zama dole domin tabbatar da zaman lafiya da bin umarnin gwamnatin Kogi da kwamishinan ‘yan sandan jihar.
“Dokar hana fitar, wacce ta fara aiki nan take, ta hana zirga-zirga da tarukan jama’a a fadin yankunan da aka ayyana dokar ta shafa.
“Duk wanda aka samu ya na yawo ko tara jama'a a wuraren da aka hana ba tare da izini daga hukumomin da suka dace ba, za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kotu."
- Inji sanarwar Amoka Monday.
"Lafiyar al'ummarmu ta fi mana komai" - Ciyaman
Amoka Monday ya jaddada cewa tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne fifikon gwamnatinsa, inda ya gargadi cewa ba za a lamunci duk wani abu da zai iya kawo rikici ba.
“Lafiyar al’ummarmu ta fi komai muhimmanci a wajenmu. Ba za mu bari a samu wani yanayi da zai kawo tashin hankali ko rashin tsaro ba," inji Monday.
Ya bayyana cewa yanke shawarar kafa dokar hana fita wani mataki ne na rigakafi domin hana duk wani rikici da ka iya tasowa.
Shugaban ya tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatin karamar hukumar na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro don sa ido kan lamarin da daukar matakan da suka dace wajen kare doka da oda.
Gwamnati ta nemi hadin kan 'yan Kogi

Asali: Original
Dokar hana fita da haramcin gangamin siyasa na daga cikin matakan da gwamnatin jihar Kogi ke dauka domin tabbatar da zaman lafiya, dakile yada jita-jita, da tabbatar da cewa ana gudanar da tarukan jama’a bisa doka.

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano
An bukaci al’ummar yankin da su bi wannan doka tare da ba hukumomin tsaro hadin kai domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.
Gwamnatin karamar hukumar ta kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin bin doka.
Sanata Natasha ta dage sai ta ziyarci Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta tabbatar da cewa ziyarar da take shirin kai wa yankin Kogi ta Tsakiya domin bikin Sallah na nan daram.
A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaranta ya fitar a ranar Litinin, Natasha ta musanta rade-radin da ke cewa ta soke wannan ziyara saboda umarnin gwamnatin Kogi.
Asali: Legit.ng