'Yadda Watsi da Shirin Sardauna ke Jawo Asarar Rayukan Hausawa,' Yan Kasuwa kan kisan Edo

'Yadda Watsi da Shirin Sardauna ke Jawo Asarar Rayukan Hausawa,' Yan Kasuwa kan kisan Edo

  • Hadaddiyar kungiyoyin masu fataucin dabbobi da kayan abinci, ta bayyana takaicinta game da kisan Hausawa 16 da aka yi a Jihar Edo
  • Shugaban kungiyar, Dakta Muhammad Tahir ya bayyana kisan da 'rashin imani', tsagwaron 'dabbanci' da kiyayya ga 'yan kasuwar Arewa
  • Ya ce ko da yake, magabata sun hango cewa mutanen Arewa da ke safarar kayan abinci zuwa Kudancin kasar nan za su fada fuskanci matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoDr. Muhammad Tahir, Shugaban hadaddiyar kungiyoyin masu fataucin dabbobi da kayan abinci ta kasa, ya yi Allah wadai da kisan Hausawa akalla 16 da aka yi a jihar Edo.

A tattaunawar da ya yi da Legit, Dr. Muhammad Tahir ya bayyana takaicinsa kan irin kiyayyar da ya ce ana nuna wa masu safarar kaya daga Arewaci zuwa Kudancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 4 na bibiyar hakkin Hausawan da aka kashe a jihar Edo," HRN

Kisan
An kashe Hausawa akalla 16 a Edo Hoto: Sam digitalz/Fahd Muhammad
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu bata-garin jama’a suka hallaka mutanen da aka tabbatar da cewa mafarauta ne, kuma sun taso ne daga Fatakwal zuwa Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dabbanci ne,’ Shugaban ‘yan kasuwa a Arewa

Daily Post ta wallafa cewa jama’a da dama, hadi da kungiyoyi a Arewacin Najeriya, sun nuna damuwa kan kisan gillar da aka yi wa Hausawa a Edo.

A karin bayaninsa, Shugaban hadaddiyar kungiyoyin masu fataucin dabbobi da kayan abinci ya shaida cewa ‘yan Arewa suna cikin mawuyacin hali saboda rashin tsaro a dukkanin sassan kasar.

Gwamna
Gwamnan Edo a Kano kan kisan Hausawa Hoto: Sunusi Batre D-Tofa
Asali: Facebook

Ya ce:

“Na farko dai muna Allah wadai da wannan dabbanci da aka yi, muna kuma Allah wadai da wannan rashin imani da aka yi wa al’ummarmu. Muna Allah wadai da matakan kiyayya da ake nuna mana.”

‘An dade ana kashe Hausawa,’ Yan kasuwa

Dr. Muhammad Tahir ya jaddada wa Legit cewa wannan ba shi ne karo na farko da ake tare motocin Hausawa ko wadanda suka taso daga Arewa zuwa Kudu ba.

Kara karanta wannan

Alkawarin gwamnan Edo ga iyalan mafarautan Kano da aka kashe a jiharsa

Ya kara da cewa ‘yan Arewa sun dade suna fuskantar matsala daga mazauna Kudancin Najeriya, wanda ya dade yana jawo musu asarar rayuka da dukiyoyinsu.

Dr. Muhammad Tahir ya kara da cewa:

“An yi asarar rayuka, tun ba yau ba, shekaru da dama ana irin wannan abubuwa. A kashe mutum, a tare mota mai kaya da dabbobi, a kone gaba daya. Ko kuma a tare mota da kaya da duka motar a kone su. Ko kuma a kashe dabbobi, ko kuma a kashe mutane daidaiku. Yau kuma ga shi ya zama kamar ruwan dare.”

Kisan Edo: An hango kalubale kan Hausawa

Shugaban ya bayyana cewa tun zamanin tsohon Firimiya, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, magabata sun yi hasashen cewa ‘yan kasuwar Arewa za su iya fuskantar kisan gilla da sauran kalubale daga ‘yan Kudu.

Ya ce:

“Tun zamanin Sardauna, magabata masu albarka sun yi irin wannan hangen, sun ce ya kamata a samu kasuwa ta tsakani, inda za mu kai dukiyarmu mu sayar, su ma su kawo nasu su sayar.”

Kara karanta wannan

Atiku ya mayar da hankali kan tausaya wa talaka a sakon barka da sallah

“Mu ma mu sayi abin da muke bukata, su ma su sayi abin da suke bukata. In ya so, kowa ya koma garinsa cikin aminci.”

An ɗora laifin kisan Hausawa kan shugabanni

Ya kuma dora alhakin halin da ake ciki a yau a kan ‘yan siyasa da sauran shugabanni da ba sa daukar rayuwar masu fataucin dabbobi da sauran kayan abinci da muhimmanci.

Dr. Muhammad Tahir ya koka kan yadda rashin tsaro ya tsayar da harkokin noma a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.

Ya ce yanzu haka Kudancin kasar na neman ya fi karfin ‘yan kasuwa saboda matsalar rashin tsaro da kisan wulakanci da ake yi wa masu safarar kaya.

Gwamnan Edo ya isa Kano bayan kisan Hausawa

A wani labarin, kun ji cewa gwamna Monday Okpebholo na Edo ya kai ziyara ta musamman zuwa jihar Kano domin jajantawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kisan Kanawa, mafarauta.

Ziyarar ta zo ne a cikin wani yanayi na alhini, yayin da kisan ya shafi yawancin Hausawan 'yan asalin jihar Kano da ke hanyarsu ta dawo wa gida, wadanda iftila'in ya fada masu a Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.