Yadda Nijar, Mali da Burkina Faso Suka Kakabawa Najeriya, ECOWAS Haraji
- Kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso sun kakaba harajin kashi 0.5% kan kayayyakin da ke shigowa daga kasashen ECOWAS
- Wannan mataki ya kara dagula dangantaka tsakanin wadannan kasashe da ECOWAS bayan ficewarsu daga kungiyar a farkon shekarar nan.
- Kungiyar kasashen da aka fi sani da AES na kokarin kafa hadin gwiwar tattalin arziki mai karfi bayan fara hadin gwiwar tsaro tun 2023
- Harajin na iya haddasa tashin farashi, durkushewar kasuwanci da kuma raunana hadin kai na tattalin arzikin yankin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Niamey, Nijar - Kungiyar kasashen Sahel wato Mali, Nijar da Burkina Faso sun sanya harajin kashi 0.5% kan kayayyakin da ke shigowa daga kasashen ECOWAS.
Wannan mataki na zuwa ne bayan da wadannan kasashe suka fice daga kungiyar ECOWAS a farkon shekarar 2025 bayan jerin juyin mulki da kuma takunkumin tattalin arziki da aka kakaba musu.

Kara karanta wannan
Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano

Asali: Facebook
Nijar, Mali sun nemo hanyar inganta arzikinsu
A wata sanarwa da kungiyar AES ta fitar makon da ya gabata, ta bayyana cewa kudin harajin zai taimaka wajen bunkasa ayyukan kungiyar, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan matakin da shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya fara dauka kan wasu kasashe.
Jamhuriyar Nijar ta fara hana ‘yan Najeriya masu fasfon ECOWAS shiga kasarta, sai dai idan suna da fasfo na kasa da kasa.
‘Yan kasuwa da matafiya sun koka kan yadda jami’an tsaron Nijar ke amfani da wannan doka wajen karbar cin hanci daga matafiya.
Duk da wannan mataki, har yanzu iyakar Illela da Konni na bude, amma ana zargin cewa Nijar na shirin hana babura wucewa tsakanin kasashen.

Asali: Getty Images
Yaushe dokar harajin kan ECOWAS zata fara aiki?
A baya, AES ta fara ne a matsayin kawancen tsaro tsakanin shugabannin mulkin soja na kasashen uku a shekarar 2023, cewar rahoton Vanguard.
Yanzu haka, kungiyar na kokarin zama gamayyar tattalin arziki tare da samar da fasfo na bai daya da karfafa dangantakar soji da kasuwanci.
Harajin ya fara aiki a ranar Juma’a 28 ga watan Maris din shekarar 2025 da muke ciki kuma yana shafar dukkan kaya daga ECOWAS banda tallafin jin kai.
Wannan mataki na iya haddasa tashin farashin kaya, matsalolin sarkar kayayyaki da kuma raunana tattalin arzikin yankin.
Duk da cewa zai iya samar da kudin shiga ga wadannan kasashen na wucin gadi, zai iya janyo illa ga hadin kan tattalin arzikin yankin na dogon lokaci.
Majalisa ta bukaci binciken zargin Tchiani
Mun baku labarin cewa Majalisar Dattawa za ta yi duba kan zargin da shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya yi kan game da Lakurawa.
Majalisar za ta fara bincike kan zargin shugaban na cewa Najeriya tana haɗa kai da Faransa don haddasa rikici a kasar Nijar.
Sanatoci za su kai ziyara jihohin Sokoto, Zamfara da Kebbi don tantance ko da gaske akwai ƙungiyar 'yan bindiga Lakurawa a yankunan nan.
Mataimakin Shugaban Majalisa, Barau ibrin , ya umurci kwamitoci su binciki lamarin kuma su bayar da rahoto a cikin makonni huɗu.
Asali: Legit.ng