Gwamnan Edo Ya Gana da Barau kan Kisan Hausawa, Ya Fadi Shirinsa kan Iyalan Mamatan

Gwamnan Edo Ya Gana da Barau kan Kisan Hausawa, Ya Fadi Shirinsa kan Iyalan Mamatan

  • Gwamnan jIhar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyarar ta'aziyya ga Sanata Barau Jibrin kan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a jiharsa
  • Monday Okpebholo wanda ya nuna takaicinsa kan lamarin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an cafke wasu da ake zargin akwai hannunsu a lamarin
  • Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta tallafawa iyalan mamatan da suka rasa ransu a mummunan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyarar ta’aziyya ga mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I Jibrin a gidansa da ke Abuja.

Gwamna Okpebholo ya kai ziyarar ne kan kisan da aka yi wa mafarauta ƴan Arewa a Uromi, ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo.

Gwamnan Edo ya ziyarci Sanata Barau
Gwamna Monday Okpebholo ya gana da Barau Jibrin Hoto: @m_akpakomiza, @barauijibrin
Asali: Twitter

Gwamnan ya ziyarci gidan mataimakin shugaban majalisar dattawan da ke Maitama, Abuja, a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Matakin da gwamnan Edo ya dauka kan kisan gillar da aka yi wa 'yan Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai ba da shawara na musamman ga mataimakin shugaban majalisar dattawa kan harkokin yaɗa labarai, Alhaji Ismail Mudashir, ya bayyana cewa gwamnan ya je ne don miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Sanata Barau wanda shi ma ɗan asalin Kano ne.

Gwamnatin Edo za tallafawa iyalan mamatan

Ya ce gwamnan na Edo ya yi alƙawarin gwamnatinnsa za ta tallafa wa iyalan mamatan.

Gwamnan na jihar Edo ya bayyana cewa an kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike.

Ya jaddada cewa za a hukunta duk masu hannu a wannan aika-aikar, tare da bayyana kisan a matsayin abin baƙin ciki, abin tir da Allah wadai.

“Abin takaici ne cewa hakan ya faru a jiharmu. Mun zo ne domin mu sanar da kai da sauran mutane cewa ba mu ji daɗin abin da ya faru ba."
Shugaban ƙasa ya ɗauki matakin gaggawa kan wannan lamari. Shi ma bai ji daɗin hakan ba. Sufeto Janar na ƴan sanda ya fara ɗaukar mataki. Ya zuwa yanzu, an kama mutum 14 da ake zargi."

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

"Za a kai su Abuja domin gudanar da bincike. Mun kuma kafa kwamiti domin tabbatar da cewa an kula da iyalan mamatan."

- Gwamn Monday Okpebholo

Monday Okpebholo
Gwamnan Edo ya ziyarci Sanata Barau.Jibrin Hoto: m_akpakomiza
Asali: Facebook

Sanata Barau ya buƙaci a yi adalci

Da yake mayar da martani, mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce dole ne a hukunta waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki domin zama izina ga saura.

“Ba za mu iya sauya abin da ya faru ba, amma abin da duk yan Najeriya ke buƙata shi ne a tabbatar da cewa an kama waɗannan mutane kuma an hukunta su."
"Kuma kuna yin ƙoƙari sosai a wannan fanni. Haka kuma na ji daɗin jin cewa gwamnatin ku ta shirya taimakawa iyalan waɗanda abin ya shafa."

- Sanata Barau Jibrin

Direba ya faɗi yadda aka kashe ƴan Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa direban motar da ya ɗauko mafarauta ƴan Arewa da aka kashe a jihar Edo, ya bayyana yadda lamarin ya auku.

Kara karanta wannan

Atiku ya bi layin Kwankwaso game da mummunan kisan da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Direban motar ya bayyana cewa duk da shaidun da suka.ba da.waɗanda ke nuna cewa su ba masu laifi ba ne, ba a saurare su ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel