Hawan Sallah: An Taso Sanusi II da Abba Kabir a Gaba kan Bijirewa Umarnin Ƴan Sanda

Hawan Sallah: An Taso Sanusi II da Abba Kabir a Gaba kan Bijirewa Umarnin Ƴan Sanda

  • Wata ƙungiyar farar hula ta bukaci bincike kan asarar rayuka yayin bukin Sallah a Kano, suna zargin gwamnati da rashin bin dokar hana hawan sallah
  • Kungiyar ta soki Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi bisa kin bin umarnin 'yan sanda, wanda ya janyo mutuwar mutane da dama
  • Ta bayyana cewa tun daga farko mulkin Abba Kabir ya fara da rushe-rushen da suka haddasa mutuwar mutane fiye da 25 ba tare da tausayi ba
  • Daga bisani ta bukaci a binciki lamarin, a hukunta masu hannu a ciki, sannan gwamnatin Kano ta fayyace dalilin kin kare rayukan al’umma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wata ƙungiyar farar hula ta soki matakin gwamnatin Kano da Sarki Sanusi II na saba doka a bikin sallah.

Kara karanta wannan

Biyan diyya da alkawuran da Abba Kabir ya yi kan Hausawan da aka kashe a Edo

Kungiyar mai suna Global Initiatives for Good Governance (GIGG) ta bukaci a gudanar da bincike kan asarar rayuka yayin bukin Sallah a Kano.

An soki Abba Kabir da Sanusi II kan saba umarnin ƴan sanda
An bukaci ɗaukar mataki kan bijirewa umarnin yan sanda da Abba Kabir da Sanusi II suka yi. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Sanusi II Dynasty.
Asali: Facebook

Ana zargin Abba, Sanusi II da saba doka

Hakan na cikin wata sanarwa da jagoran ƙungiyar Abubakar Yahaya Capenta ya fitar wanda Hassan Cikinza Rano ya yada a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Capenta ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi da watsi da dokar hana hawan sallah.

Kungiyar ta ce wannan “rashin ɗa’a” ba sabon abu ba ne, domin tun daga ranar biyu na mulkinsa, Gwamna Abba Kabir ya fara rushe gidaje, wanda ya haddasa mutuwar mutane fiye da 25.

Ta kuma tuna cewa kwanan nan an sake rushe gidaje a Rimin Zakara, wanda hakan ya yi sanadin rasa rayuka.

Amma abin mamaki, gwamnan ya bayyana cewa bai yi nadama ba ko kadan kan wannan abin da ya yi.

Kara karanta wannan

Ana zargin matashi da kisa a tawagar Sanusi II, ƴan sanda sun gargadi al'ummar Kano

Ana zargin Sanusi II da Abba Kabir da jawo rashin tsaro a Kano
Kungiya ta bukaci binciken Abba Kabir da Sanusi II kan saba umarnin ƴan sanda. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa.
Asali: Facebook

Kungiya ta shawarci al'ummar jihar Kano

Har ila yau, ta yabawa jami’an tsaro a jihar Kano bisa jajircewarsu wajen tabbatar da tsaro duk da halin da ake ciki, sannan suka bukaci a hukunta gwamna da sarkin bisa rawar da suka taka.

Kungiyar ta ce dole ne a tabbatar da adalci domin maido da amana da kuma hana ci gaba da cin zarafin jama’a.

Kungiyoyin sun kuma yi kira ga al’ummar Kano da su kasance masu sa ido tare da bukatar shugabanni su ɗauki alhakin aikinsu.

Sanarwar ta ce:

“Jiharmu tana bukatar shugabanci mai kishin al’umma fiye da nuna iko da rashin kulawa da rayukan mutane.”
“Kungiyar tana bukatar adalci da binciki mutuwar da aka yi sakamakon wadannan haramtattun ayyuka.
"A gurfanar da duk wanda ke da hannu a saba dokar ‘yan sanda da bayyana dalilin wannan cin zarafi.
"Ba za mu daina fafutukar neman adalci da shugabanci nagari ba, al’ummar Kano sun fi dacewa da hakan.”

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi matsayarsa kan umarnin hana hawan Sallah a Kano

An kama wanda ya yi kisa a tawagar Sanusi II

Kun ji cewa Rundunar ‘yan sandan Kano ta cafke Usman Sagiru mai shekara 20 daga Sharifai kan zargin kashe wani dan sa-kai da harin da aka kai bayan sallar idi.

A yayin watsewa daga filin sallah, Sagiru da wasu sun soka wa Surajo Rabiu wuka, wanda daga baya ya rasu, sannan Aminu Suleman na jinya a asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng