Rashin Imani: Direba Ya Fadi Ainihin Yadda Aka Kashe 'Yan Arewa a Jihar Edo
- Direban motar da ya ɗauko ƴan Arewan da aka kashe a jihar Edo, ya yi bayani kan yadda mummunan lamarin ya auku
- Ya bayyana cewa ya haɗu da su ne suna neman motar da za ta dawo da su gida domin yin bukukuwan Sallah
- Direban ya bayyyana cewa babu wata matsala da suka samu a tafiyarsu har sai sa suka zo Uromi sannan aka yi musu wannan kisan kiyashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Bayanai na ta ƙara fitowa kan yadda aka yi wa wasu mafarauta ƴan Arewa kisan gilla a jihar.
Direban babbar mota da ya tsira daga harin, ya ba da labarin abin da ya faru, inda ya musanta cewa lamarin ya shafi rikicin ƙabilanci.

Asali: Original
Direban motar ya yi bayanin ne a wani bidiyo da Zagazola Makama ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kashe mafarauta ƴan Arewa a Edo
Lamarin dai ya faru lokacin da matafiyan, waɗanda mafarauta ne, ke kan hanyarsu daga Port Harourt jihar Rivers, zuwa Kano domin bukukuwan Sallah.
Direban babbar motar, wanda ba a bayyana sunansa a bidiyon, ya bayyana cewa yana jigilar kayayyakin kamfanin Dangote zuwa Obajana a jihar Kogi ne lokacin da ya haɗu da su a Elele, inda suka roƙe shi da ya taimaka musu su hau motar zuwa Arewa.
A cewarsa, tafiyar ta kasance lafiya ba tare da wata matsala ba har sai da suka isa Uromi, inda wata ƙungiyar sa-kai ta tare su.
Direban motar ya yi bayani
"Na zo Elele sai waɗannan mutanen (mafarauta) suka tare ni, suna buƙatar za su je gida Sallah, sai na gaya musu cewa kamfaninmu ya hana ɗaukar fasinja, ga shi ku ƴan uwana ne za ku je gida Sallah. Ga shi kuna da yawa, ku yi haƙuri ba zan ɗauke ku ba."

Kara karanta wannan
Hafsan tsaro ya tsoma baki kan kisan ƴan Arewa a Edo, ya fadi shirinsu kan lamarin
"Bayan mun yi haka da su, na yi tafiyar kilomita biyu, sai na ga cewa na bar ƴan uwana a Kudu suna neman taimako, sai na ƙara juyowa na zo na same su har suna mamaki."
"Na ce ba zan iya barin ku a nan ba domin na san za ku je gida, saboda kuna ƴan uwana Hausawa Musulmi."
"Mun taso lafiya muna tafiya ba inda muka samu cikas sai da muka zo Uromi, a nan Uromi muka samu ƴan sa-kai sai suka tare mu a cikin gari."
"Da suka tare mu sai suka tambaye ni me na ɗauko, sai na ɗauko takardar shaidar cewa kayan kamfani ne na ɗauko. Waɗannn mutanen fa, sai na ce ƴan uwana ne na ɗauko daga Port Harcourt za su je gida Sallah, kuma mutanen Kano ne."
"Sai ya ce baruwansa su sauko bai yarda da su ba, a lokacin da ya faɗi haka sai ɗaya daga cikinsu ya hau saman motar, sai ya ga karnukansu da kayan aikinsu (bindigar farauta)."

Kara karanta wannan
Bidiyon yadda aka yi jana'iza, aka birne ’yan Arewa 16 a Edo cikin hawaye da tausayi
"Yana saukowa kawai sai ya gayawa ƴan uwansa ƴan Uromi cewa waɗannan mutanen masu garkuwa da mutane ne, kuma ƴan Boko Haram ne. Yana faɗin hakan sai aka fara fasamin gilashi sai kuma duka."
- Direban mota

Asali: Facebook
Ya ƙara da cewa shugaban ƴan sa-kan ya tafi da shi da wasu mutum biyu zuwa ofishin ƴan sanda inda ya sanar musu da cewa masu garkuwa da mutane ne.
Bayan ƴan sanda sun bincike su, ba su samu komai da ke nuna zargin da ake musu ba.
Ya ce kafin shugaban ƴan sa-kan ya dawo, shi ne har an cika umarnin da ya ba da na kashe mutum 16 zuwa 17 daga cikinsu.
Barau ya yi Allah wadai da kisan ƴan Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya nuna takaicinsa kan kisan gillar da aka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo.
Sanata Barau ya buƙaci hukumomin tsaro da su tabbatar da cewa sun zaƙulo mutanen da suka aikata laifin domin su girbi abin da suka shuka.
Asali: Legit.ng