Bikin Sallah: Gwamnatin Yobe Ta Sanya Almajirai Masu Yawa Farin Ciki

Bikin Sallah: Gwamnatin Yobe Ta Sanya Almajirai Masu Yawa Farin Ciki

  • Gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta sanya farin ciki a zukatan almajirai masu karatu a makarantun Tsangaya
  • Almajirai 1,360 sun samu kayan Sallah a rabon da gwamnatin ta yi na tufafi a makarantun da ke faɗin jihar
  • Kowace makaranta da aka zaɓo, an.ba ta wani kaso na takalma da kayan sawa da kuma abinci ga malaman da ke kula da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta gwangwaje almajirai domin murnar zuwan bikin Sallah.

Gwamnatin ta raba kayan Sallah da tufafi ga almajirai 1,360 a makarantun Tsangaya da ke faɗin jihar.

Gwamna Mai Mala Buni na Yobe
Gwamnatin Yobe ta raba kayan Sallah ga almajirai Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Shugaban hukumar AISEB mai kula da harkokin karatun almajirai a jihar, Dr. Umar Abubakar, ne ya ƙaddamar da rabon a birnin Damaturu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Almajirai sun samu kayan Sallah a Yobe

Ya bayyana cewa kowace makarantar Tsangaya da aka zaɓa ta samu kaya 40 da takalma 40 don rabawa almajirai.

Haka kuma, an raba tallafin abinci ga malamai domin sauƙaƙa musu nauyin kula da almajiransu a wannan lokaci na bukukuwan Sallah.

A cewarsa, wannan tallafi na Sallah an shirya shi ne domin ya amfani almajirai sama da 1,360 daga makarantun Tsangaya daban-daban a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa, manufar shirin ita ce inganta jin daɗin almajirai, ta yadda za su samu yin farin ciki a lokacin Sallah ba tare da jin ƙuncin rashin tufafi ko abinci ba.

Dr. Umar Abubakar ya yabawa Gwamna Mai Mala Buni bisa jajircewarsa wajen kula da walwala da jin daɗin almajirai da sauran masu ƙaramin ƙarfi a jihar Yobe.

Ya ce gwamnan ya kasance mai kishin al’ummar jihar, yana aiwatar da shirye-shiryen da ke inganta rayuwar yara masu karatu a Tsangaya.

Kara karanta wannan

Bayan Aminu Ado ya haƙura, Gwamnatin Kano ta canza tsarin ranar jajibirin sallah

Gwamna Mai Mala Buni
Gwamnatin Yobe ta raba kayan Sallah ga almajirai Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Gwamnatin Yobe ta samu yabo

A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar makarantun tzangaya ta Jihar Yobe, Goni Modu Goni Aisami, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Buni bisa fifita buƙatun almajirai da sauran mabuƙata.

Ya bayyana cewa wannan shiri na rabon kayayyakin Sallah wata gagarumar alama ce ta irin kulawar da gwamnatin ke nunawa ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

Haka kuma, ya yaba da sauye-sauyen da aka kawo domin inganta rayuwar almajirai da malamansu.

Hakazalika ya yi kira ga gwamnatoci da sauran masu hannu da shuni su ci gaba da tallafawa ilimin almajirai domin samar da kyakkyawar makoma a garesu da kuma al’umma baki ɗaya.

Matawalle ya raba shanu domin bikin Sallah

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Dr. Bello Matawalle ya gwangwaje mambobin jam'iyyar APC da abin alheri a jihar Zamfara.

Bello Matawalle ya raba shanu ga mambobin jam'iyyar ta sa domin su gudanar da bukukuwan Sallah cikin walwala da jin daɗi.

Kara karanta wannan

Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a

Ministan ya bayyana cewa rabon shanun na daga cikin irin aikin alherin da ya saba yi a duk shekara a irin wannan lokacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel