Sarkin Musulmi Ya Aika Sako ga 'Yan Najeriya, Ya Gano Kukuren da Suke Yi kan Shugabanni

Sarkin Musulmi Ya Aika Sako ga 'Yan Najeriya, Ya Gano Kukuren da Suke Yi kan Shugabanni

  • Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya koka kan halayyat zagin shugabanni da wasu ƴan Najeriya ke da ita
  • Sarkin Musulmin ya buƙaci ƴan Najeriya da su guji yin ɓatanci idan za su shigar da ƙorafinsu ga shugabanni
  • Ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa sanya shugabanni cikin addu'a domin su samu nauyin da ke kansu yadda ya dace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi muhimmin kira ga ƴan Najeriya.

Sarkin Musulmin ya buƙaci ƴan Najeriya da su guji yin amfani da kalmomin ɓatanci wajen bayyana ƙorafinsu ga shugabanni.

Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar
Sarkin Musulmi ya bukaci 'yan Najeriya su daina zagin shugabanni Hoto: Ningi Emirate
Asali: Facebook

Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayyana hakan ne a saƙon barka da Sallah da ya fitar jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi a filin Idi na Fakon Idi a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: Ganduje ya tura sako mai muhimmanci ga Musilmi bayan kammala azumi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Sarkin Musulmi ya ba da?

Sarkin Musulmin ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni a kowane matakai addu'a.

"Yana da kyau a faɗawa shugabanninmu idan akwai matsala, amma yayin yin haka, dole ne mu guji kalmomin ɓatanci."
"Idan ka zagi shugabanka, ta yaya za ka buƙaci ya yi maka wani abu?"
"Amma idan ka faɗa masa matsalarka cikin ladabi, ina da tabbacin zai saurare ka kuma ya ɗauki matakin da ya dace."
"Ku yi wa shugaban ƙasa addu’a, ku yi wa gwamnoni addu’a, ku yi wa shugabannin ƙananan hukumomi addu’a, kuma ku yi wa ƴan majalisu addu’a, domin Allah Ya ji tausayinsu Ya kuma taimake su wajen sauke nauyin da ke kansu."
"Hakanan, ku ci gaba da yin addu’a don zaman lafiya, ci gaba, da albarka a jihohinmu da ƙasa baki ɗaya."

- Alhaji Muhammad Sa'a Abubakar

Sarkin Musulmi ya taya murnar gama azumi

Kara karanta wannan

Sallah: Matawalle ya ware 'yan APC, ya yi musu babbar kyauta a Zamfara

Sarkin musulmin wanda shi ne shugaban majalisar ƙoli ta harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya kuma taya al'ummar Musulmi murna bisa kammala azumin kwanaki 29 na Ramadan.

Alhaji Muhammaɗ Sa'ad Abubakar
Sarkin Musulmi ya ba 'yan Najeriya shawara Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Twitter

Ya yi kira gare su da su ci gaba da ɗaukar ɗabi’u na gari da suka koya a watan azumi a rayuwarsu ta yau da kullum.

Har ila yau, ya yabawa malaman addini kan yadda suka gudanar da Tafsirin Ramadan cikin natsuwa, yana mai kira gare su da su ci gaba da hakan a wa’azozinsu na gaba.

Bugu da ƙari, ya jinjinawa Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto bisa rabon tallafin Ramadan ga talakawa da marayu, da kuma aiyukan ci gaba da ake aiwatarwa a faɗin jihar.

Sarkin Musulmi uba ne

Kabir Ibrahim ya nuna gamsuwarsa kan shawarar da Sarkin Musulmin ya ba da wajen shigar da ƙorafi kan shugabanni.

Ya nuna cewa shugabanni mutane ne masu ƙima waɗanda ya kamata a mutunta su yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a

"Gaskiya shawara ce mai kyau domin shugabanci ba abin wasa ba ne. Sarkin Musulmi uba ne kuma shawarwarinsa abun ɗauka ne."

- Kabir Ibrahim

Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan Shawwal

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ys tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1446AH.

Sarkin Musulmin ya bayyana cewa za a gudanar da Idi na ƙaramar Sallah a ranar Lahadi, 30 ga watan Maris 2025 wanda ya yi daidai da 1 ga watan Shawwal 1446AH.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng